on nata su na barin wajen, tana jin kamar tana so tace musu su ƙyaleta ba sai an ciro yaran ba.
Turaki yabi ta da kallo yana ganin yacca hawaye ke sauka ta gefen idonta, hawaye na farko da zai cewa ya gani a tare da ita tun a ɗazu da ta fara naƙudar.
"don Allah kar kuyi min allurar bacci, ku yi min idona a buɗe, ina son ganin a yacca za'a fito min da Babies ɗina".
ta faɗa idanunta na kallon likitocin da ke kanta tare da nurses, a lokaci ɗaya sai taji tausayin bawan Allahn da rayuwarsa take tamkar a nannaɗe da tata, Turakinta! Mijinta!, uban ƴaƴanta, wanda ta san a duk lokacin da tata rayuwar ta ƙare, lokacin da ta zama bata cikin rayuwarsa, to tabbas bata san ya duniyarsa zata kasance ba.
sannan tausayin ƴaƴan da zasu fito daga cikinta yay mugun matse zuciyarta, bata san ya rayuwarsu zata kasance ba a yayin da babu ita, bata san ya tasu ƙaddarar rayuwar zata zama ba, bata san irin jarabawowin da za su fuskanta ba, duk da ta san babbar jarabawa a gare su shi ne na rashinta, za su taso ba tare da uwar da ta kawo su duniya ba, za su ta so ba tare da sun san wannan ɗumin jikin na uwa ba, za su taso babu wannan kulawa da soyayyar da yake a wurin uwa ba kaɗai.
"bismillahir-Rahmanirrahim, bring the knife".
haka taji likitan da ke tsaye akanta ya faɗa, kuma bayan wannan zata iya cewa jinta ya ɗauke na ɗan wani lokaci kafin ya dawo.
a san da aka fara aikin, idanun Fillo a jiƙe suke sharkaf da hawaye, hawayen da ya hanata ganin komai sosai. a wannan lokacin dukkan tunaninta ya gama hargitsiwa da kowanne motsin dake faruwa a cikin ɗakin tiyatar, tana jin yacca sautin zuciyarta ke bugawa da ƙarfi acikin kunnenta.
lokaci ɗaya taji sautin wata ƙara ta fita a jikinta, sautin da ta tabbatar na yanka ne, cikinta ake yankawa!, sai taji zafin ciwon da take ta daurewa ya ƙaru, zafinsa na ƙaruwa sosai da sosai, zafin da har ta kai ga kasa tantance cikinta ake yankawa ko kuma ruhinta ake zarewa.
hawaye ya bi ta gefen fuskarta, ta ji kamar ta ɗago tasa hannu ta danne wajen da aka yanka ko zata sami sassauci, sai dai babu abin da zata iya, bata da ƙarfin motsi ko kaɗan, tamkar matacciya take.
tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a cikin ɗakin tiyatar sai fafutukar da likitoci ke yi wajen ciro yaran daga cikin mahaifiyar su.
kunnuwan Fillo sun ji lokacin da aka ciro Baby na farko, Babyn da taji Dr na cewa da nurses su yi ƙoƙarin su wajen ganin yayi kuka, sai taji wani farin ciki ya ratsata, farin cikin da taji tamkar an yi mata bushara da gidan aljannah.
so take taga yaron da aka ciro, don haka cikin ƙarfin hali da dauriya ta karkata kanta gefe domin kallon jaririn da cibiyarsa kaɗai take iya hangowa, kuma a san da nurse ɗin ke juyowa zuwa sashinta, lokacin sabuwar azaba ta ƙara ratsata, tayi saurin rumtse ido tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
ambaton nata ya haɗe tare da kukan Baby na biyu da aka ciro, kukan da ya cika ɗakin gaba ɗaya, kukan da zata ce kamar ta tsinci sunan da take ta muradin ta haife su taji sun kirata da shi, Ummina!.
a san da Babyn yay shiru sai taji jikinta ya tsaya a lokaci ɗaya, yay sanyi ƙalau, numfashinta mai nauyi na cigaba da fita, yayin da zuciyarta ke bugawa a hankali, hakan yasa ta fahimci cewa hargitsin azabar ciwon da take sha yazo ƙarshe, ƴaƴa biyun da ke cikinta an fito da su duniya, ta zama uwa, dukkan fatanta da burinta ya gama cika, atleast ta samu masu yi mata adu'a a kowacce daƙiƙa a yayin da komai ya riga ya kai ƙarshe.
ta riga ta san abin da yake cikinta tuntuni, macece da na namiji ne ba sai an faɗa mata ba a yanzu. tana jin yacca motsin yaran da ake ta aikin gyarawa ke mutsutsu acikin kunnenta, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da son su da ƙaunar su, sannan a hankali ta fara jin komai na zamewa daga cikin kanta yana barin ƙwaƙwalwarta, cikin ranta tana adu'ar,_"Ya Rahman if you decide to take my soul at this time, i beg you Allah to give my husband and my childrens the strength to bear it, Allah kaji tausayin ƴaƴana, ka tausayawa maraicin su ka basu tamkar Hajiya Madina a matsayin wacca zata kula da su"._
da ga wannan furucin dake cikin ranta, sai kuma bakinta ya shiga maimaito kalmar shahadar da taji tana wanzuwa acikin kanta, hakan yasa idanuwan likitocin da ke ɗakin ya manne akanta, akan murfin idonta da ke barin kan twins ɗin da ake nuna mata amma ta kasa kallon su.
kuma wucewar sakanni biyar komai ya zama ya ƙare, komai ɗin dake rayuwar Fillo, shikenan wa'adin da ubangiji ya ɗiba mata ya cika, alƙalaminta ya riga ya bushe, ubangiji yayi hukuncinsa.
bayan wasu mintuna Turaki da ke tsugune a ƙofar ɗakin tiyatar yaji an buɗe ƙofar, bai motsa ba dan bai san ta yanda zai motsa ba, yana so dai ya buɗe idonsa yaga abin da ke wanzuwa, so yake ya buɗe ido ko ya samu zuciyarsa ta daina bugawar da take yi.
acikin wata fargaba da ke tare da shi yaji an ɗora hannu akan kafaɗar sa, sai ya ɗan buɗe ido kaɗan yana kallon nurses guda biyun da ke tsaye akansa tare da l