NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 310 of 323

ty, babu abun da zai faru kaji?, lafiya lau za'ayi aikin nan da izinin ubangiji, kuma lafiya lau za'a fito maka da ni da ƴaƴanka". Turaki ya ɗago kansa ya kalleta, a san da yake amsawa da Allahumma amin. Fillo ta dinƙa kallonsa tamkar yaune ta soma ganinsa, mamaki take yi sosai, bata taɓa yi masa murmushi ba yaƙi mayar mata da martanin hakan, haka zalika bai taɓa kallon fuskarta ba, ba tare da tasa fuskar ta washe da kyakykyawan murmushi ba, a yau kuma a wannan lokacin fuskarsa na looking so hard, babu wani emotion da za ta ce ta tsinta a ciki, zatonta ranar yau ita ce ranar da yake ta jira, wan nan lokacin shi ne yake tsimayin jiransa saboda ƴaƴansa guda biyu za su fito duniya, don haka a wannan lokacin ya kamata ace taga yana farin ciki ko ya ya ne. amma tun a gida da ta fara ce masa ciwo, yay ɗan guntun murmushi yana tsokanarta da Lukutar gombe zata haihu zata sace a koma gidan jiya, zata dawo kamar muciya da zani. ta san tayi dariya a lokacin da yay wannan maganar, but ita a lokacin data tsokane shi da cewa haka aka gani a muciya da zanin aka nace sai da aka ɗauka, bata ga wani kuzari na martanin dariya daga gare shi ba, kawai dai ya miƙe ya ɗauko jarkar rubutu ya bata ta tasha cikin mutuwar jiki. ta lumshe idonta ta buɗe kafin tace,"ƙarfe nawa Jannaty?". zai iya cewa da ƙyar ya iya karantar agogon kafin yace mata,"takwas da rabi Fulani nah". ta sauke numfashi ta ce,"sun ce sai ƙarfe tara da rabi zamu shiga, da za su bani dama da na kalli gabas nayi adu'a". sai kuma tace,"ka ci abinci Jannaty?". bai iya magana ba illa girgiza mata kai da yay. "me yasa to?, kana so Aayan ya taso ya fika ƙiba ko?, mutane suke tsokanarka su na cewa ɗanka yafi ka ƙiba". sai ya daɗa riƙe hannunta kamar wanda za'a ƙwace masa ita yace,"ta ya zan iya saka wani abu a cikina alhalin kina cikin mawuyacin hali?". "Jannaty na faɗa maka ka kwantar da hankalin ka, lafiya lau za'ayi komai babu abin da zai faru". "zan ci abinci amma sai an fito da ke, wataƙila ma yau ba zan ci irin abincin da za kici ba, wan da zanci zai fi wanda zaki ci daɗi, ko don saboda nayi ƙiba a daina yi min gori". tayi murmushi,"to me zaka ci?". sai ya kai hannunsa ɗaya saman breast ɗinta ya taɓa yace,"madaran yarana zan sha, mu uku za kiyi feeding yau". "baka da damuwa guda ɗaya ma za'a bar maka, sai suyi shairing guda ɗaya". ta ƙara cewa,"ka yi min waƙar da kake yi min Jannaty". ya girgiza mata kai,"ban da waƙa sai dai adu'a". "to kayi min karatu cikin ƙira'arka me daɗi". a hankali kuma ya shiga biyo mata suratul shu'araa. har san da yazo kan aya ta ashirin da takwas,_wa'izaa maridhtu fahuwa yashfeeeen_. sai ta ji wani abu na bi ta ƙasan zuciyarta, ta kira sunansa da irin amon sautin da zai ce bai taɓa jinta da shi ba, ya kalleta idanuwansu suka sarƙe waje ɗaya, ya haɗiye wani abu da bai san menene ba kafin yace,"menene Fulani Nah?, me kike so?, ciwon yana raguwa?". ta mayar da murfin idon ta rufe ta ce,"hold me Jannaty, i want to talk to you". ta faɗi hakan tare da buɗe idanuwanta. "Jannaty duk da halin da nake ciki ina yi maka murmushi, please kayi min wannan kyakykyawan murmushin naka atleast ko da sau ɗaya ne, ko da bai yi faɗi da yawa ba, ka daure kayi min ko ya ya ne". shirunta ya haɗe da bayyanar haƙoran Turaki duka a waje, maimakon murmushin da tace tana so sai kawai ya sakar mata dariyarsa me daɗin sauti, dariyar da har ita ma sai da tayi irin tasa ɗin, dariyar da ta ratsa jijiyoyin Turaki ta zarce har cikin zuciyarsa ta huda wani waje. ta buɗe baki a hankali tace,"ko kai fa Baban biyu, please you take good care of our kids, ko babu ni na san kai uba ne na gari, na san yaran mu ba za su yi kukan maraici ba, kayi musu dukkan gatan da uba yake yiwa ƴaƴansa, ka ba su wadataccen ilimi, kaja su a jikinka ta yanda zaka dinƙa jin damuwar kowannen su, ka kula da tarbiyar su, tarbiyar su da iliminsu!, tarbiyarsu da ilimin su don Allah Jannaty". furucin nata yasa yaji kamar zai yi kuka, ya ƙanƙameta yana faɗin,"bana son magana irin wannan, you promise me that we will be together forever, so why talking like this?". "Allah ya baka haƙuri ba zan ƙara ba daga yau, ka yafe min". taja hancinsa laɓɓanta na motsa da murmushin ƙarfin hali tace,"i love you Turakin Fulani". sai kawai ya miƙe tsaye, ya manta da nurses ɗin da ke tsaye a gefe, ya manta da su Mum da ke tsaye su na kallonsu, ya manta da mutanen dake giftawa, yasa hannu ya ɗagota, ya haɗe bakinsa da nata yana kissing har tsawon minti biyu, kafin daga baya ya shiga kissing ko'ina na fuskarta sannan ya rungumeta tare da furta,"i love you morethan you do Fulanin Turaki". a lokacin ne kuma Dr ya bawa nurses umarnin cewa su wuce da ita ɗakin tiyatar. sai taji hannun Turaki na zamewa daga cikin nata, muryarsa na fito a mugun karye, yana yi mata adu'ar Allah yasa ayi cikin sa'a, Allah yasa ta fito lafiya. sai kawai ta rumtse idanuwanta gam, tana jin nurses ɗin na tura gad
🏠