NOVEL SHARES -
a ba ki ji ba?".
tace,"wanne?".
Ya galla mata harara bai ce komai ba, haka kawai taji tana tsoronsa, yanda taga ya jijjiga kai bata san me zai aikata ba, saboda haka hannunta na shaking taja kujeran ta zauna a ɗarare.
"na zauna". ta faɗa tana kusan ƙwarewa.
ta wutsiyar ido yake kallon hannunta dake rawa akan plate, yana da tabbacin yarinyar nan bata da isashshiyar lafiya.
Muryarsa a kausashe yace,"buɗe abincin kici".
ta wani waro ido waje ta kalle shi, cin sanyin jiki tace,"na ƙoshi".
rufe bakinta ya haɗe da wani mugun kallo daya watso mata, bata san lokacin da ta damƙe plate ɗin abincin ba.
Turaki kuwa kallon ƙasusuwan jikinta kawai yake, ina alamar ƙoshi anan?, kamu ɗaya zai yi mata ta ɓalle gaba ɗayanta, idan kuwa yace zai yi mata kallon tsab sai ya ƙirge duka ƙashin jikin nata, kuma a hakan ta ke ikirarin ta ƙoshi.
ya karkato kanta murya a ɗage yace,"kin ci abincin nan ko sai na miƙe kinga asalin tsayina?".
babu shiri Fillo ta kai hannu cikin plate ɗin zata fara ci, ya dakatar da ita cikin tsawa da cewan,"ɗau spoon".
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*10*
wannan tsawar da Turaki ya sakar mata ita tasa ta rikicewa gaba ɗaya, she was completely out of her mind, spoon ɗin da ta ɗauka ya faɗi ƙasa ya bada sautin wata ƙara wadda sai da Turaki yasa hannu ya toshe kunuwansa.
haushin hakan yasa shi damƙo hanunta cikin zafin nama, wanda bai san lokacin da yay hakan ba. ɓacin rai ne kawai, jin mugun riƙon da yayi mata sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara rumtse idanuwanta da kyau, ta shiga girgiza kanta a hankali cikin zubar hawaye masu zafi.
muryarta tayi can ƙasa, amma hakan bai hana lafuzan bakinta shiga kunnansa ba, thats why he focuse attention on something she is saying. "dan Allah kar kiyi mata komai". ya so yaji dukkan abunda tace sai dai hakan ya gagara, sai wanda kawai ya tsinta, kuma daga shi ɗin tayi shiru, bata sake cewa komai ba sai shashsheƙar kuka da ta ke yi.
ya ƙura mata ido kawai yana dubanta da kyau da kuma mamakin fitar hayyacin da tai a lokaci ɗaya, ba sai an faɗa masa ba da ganin yarinyar yasan bata da isashshiyar lafiya. lokacin da ta dawo cikin natsuwarta ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan hannunsa da har yanzu ke riƙe da nata gam.
ƙirjinta banda up and down babu abinda yake, idonsa na kan dining table ɗin da alama wani abu yake tunawa, hakan yasa bai san da buɗe idanuwan nata ba sai jin maganarta yayi.
"Hannuna". ta faɗa muryarta na fitowa a hankali. ya ɗago ido ya kalli hannunsu dake haɗe, sai kawai yasha mur sannan ya kalleta yace,"ba ki da hankali da za ki sakarwa mutane cokali yayi wannan uwar ƙarar, kuma kukan na uban mene?".
bata ce da shi komai ba tayi shiru, ƙoƙarin ta janye hannunta ta ke amma yaƙi sakinta, ta matse ido kaɗan ta buɗe tare da cewan,"ka matse min fata". sai a lokacin ya ankare ya sakar mata hannu, ta wutsiyar ido ya kalli yanda fatar wurin tayi jawur.
ita dai tunda ya sakar mata hannun sai ta kama wajen tana shafawa a hankali saboda zafi, so take ta gama hucewa ta miƙe ta tafi inda tafi kauri, tafiyar da ba zata ƙara dawo da ita nan ba, wannan zuwan nata shine na farko kuma shine na ƙarshe ba za'a kuma wani ba.
ta miƙe zata bar kujerar ya ɗaga kai ya kalleta, murya a tamke, fuska a ɗaure yace,"koma ki zauna, in kinga kin tashi a wurin nan to kin cinye wannan ƙazantar taki".
ta kalli abincin ta kalle shi, ta ɗan haɗe fuska sannan tace,"Hajiya ce ta girka bani ba ai".
yanda muryarta ta kumbura wajen faɗa sai ya zamana kamar da rashin kunya ta faɗa, hakan yasa yay saurin ɗagowa, da miƙewarsa tsaye da kai hannu fuskarta zai mareta duk bai san lokacin da yay ba. banda Allah ya taimaka tayi saurin yin ƙasa da fuskarta da sai ya sharara mata marika.
ya yiwa dining table ɗin wani mugun duka hannunsa na dunƙulewa akai. "saboda nace kici ƙazantarki shine za ki buɗe ba ki kice min Hajiya ce ta girka, what do yo mean by saying that?".
ta ƙanƙame jikinta saboda ganin kamar zai saka ma ta hannu, ya hankaɗa kujerar baya ya fito yay tsaye gabanta, tana jin yanda hucin isakar hancinsa ke sauka a jikinta. kallonsa ta ke ta ƙasan ido, zata iya rantsewa wannan mutumin ko me jinnu ko kuma me ƙarancin lafiyar ƙwaƙwalwa.
yana shirin kai hannu ya shaƙi wuyanta don ta fassara masa abinda ta ke nufi da maganarta, sai ga Zaytuna ta shigo parlon, tun daga bakin door da ta hangesa tai saurin ƙarasowa ta riƙe hannunsa tana dubansa a rikice.
"matsa baya". tace da Fillo wadda ke duƙe har lokacin, kuma jin hakan yasa tayi saurin matsawa da baya ta raɓe daga bango tana sauke numfashin kamar wacca tayi tseren gudu, zuciyarta cike fal da tsoronsa.
Zaytuna ta juya ta ƙara kallonta sannan ta ƙara maido da kallonta kansa. "please Hamma nah sorry".
idan da zata zauna zaman lissafi zata iya lissafa wucewar kusan rabin shakara rabon da taga ya shiga cikin wannan mood ɗin, mai sauya shi ya fita daga Turakinsa ya koma wata halittar ta dab