NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 309 of 323

u take ganinsa, ta tattaro dukkan sauran ƙarfinta da ya rage mata ta daure, ya kamata ta yunƙura ta miƙe tana dafa kafaɗarsa, zafin ciwon da ya ƙaru yasa duhu ya wanzu a cikin idonta, ta daina ganin komai, tabbas bata iya ganin komai harta mijinta da yake riƙe da ita, sai dai kunnenta na iya jiyo mata sautin muryarsa dake fita cikin tsananin tashin hankali. Allah ya taimaka musu a bedroom ɗin ƙasa ne, da basu san ta yanda za'ai su sauko daga saman ba. Turaki yaji tayi masa wata muguwar damƙar da zai rantse ba ita ba ce, domin ba ƙarfinta ba ne, bata da wannan ƙarfin ya sani. "ka ɗauko riyon Babies mu wuce asibiti". "ba zan iya tafiya na barki ba a haka". "zan iya Jannaty, zan iya daurewa, zan daure har ka dawo". nan da nan Turaki ya haye sama ya tattaro duk wasu abubuwa da za'a buƙata a asibiti, ya kira Ilham a waya ta taho part ɗin, tana shigowa parlon ta tarar da Fillo durƙushe a ƙasa tana ambaton Ya salamu, Ya Salamu ka kawo min da sauƙi, idan na kasa ubangiji ka bani dauriyar da zan iya. tayi kanta da sauri, Turaki ya sauko ya dire kayan hannunsa. "kira yaran nan su kai mota sai ki zo mu kamata". hankalin Ilham a tashe ta shiga ƙwalawa su Sakina kira, bata ma iya yi musu magana da baki ba sai nuni da tayi musu da hannu. fitowarsu compound Boɗejo ta iso gidan ita ma duk a ruɗe, tana ganin yanda suke tafiya da Fillon a hankali ta ɗaga murya wajen ce musu,"kai ai zuwa zaka yi ka kawo motar nan kusa, sai mun hanzarta kar ta haihu a mota". tsabar ruɗewa Turaki ya manta da tunanin hakan, don haka ya sakarwa Ilham ita ya wuce cikin sassarfa yana haɗawa da gudu. asibiti mafi kusa suka isa, su na zuwa aka karɓe su saboda ganin yacca Fillo ta gama galabaita cikin mintunan da gaba ɗaya ba zasu kai rabin awa ba, ƙari kuma da uban kuɗin da suka ji an sakar musu duk da cewa dama asibitin private ne. wucewar wasu mintuna da ba zasu wuce goma ba Dr ya fito yana shaida musu cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata CS. "in har zata haihu lafiya ku yi mata koma menene, ina da buƙatar matata don Allah". furucin ya fito daga bakin Turaki murya a kakkarye. Dr ya ba su takardar da za su yi signing akai, Turaki yay signing ɗin a san da hannunsa da jikinsa duka ke rawa. kafin Dr Yusuf ma ya karɓa yay sigining a ɓangaren signature na mahaifinta. cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna aka shiga preparation ɗin yiwa Fillo tiyata. lokacin duk ƴan gidan su Turaki sun iso asibitin, da Ammi mahaifiyar Yusuf, da wasu ƙannen Hayyo mutum biyu da suke anan garin gombe Safna da Alawiyya. duk ɗinsu su na zaune a ƙofar labour room ɗin da aka shiga da ita tun ɗazu, kowa yay jugum jiki duk a sanyaye, babu wanda zaka kalla kaga kwanciyar hankali a tare da shi, mahaifiyarta sai kiran waya take yi ana faɗa mata ko tiyatar ma ba'a shiga ba har yanzu. Turaki kuwa zama da tsayuwarma sun gagare shi sai zarya yake tayi, time to time sai yasa hannu ya sharce zufar da ke saman goshinsa. motsin buɗe ƙofar labour ɗin da aka yi yasa duk suka tattara hankalin su gun, Dr ya fito cikin sauri ya nufi side ɗin operation thiater, a san da nurses biyu ke turo gadon da Fillo ke kwance akai, tana sanye cikin uniform ɗin da ake sawa na CS, nurses ɗin suka tsayar da gadon a san da suka ƙaraso saitin family ɗin nata. Mum ta fara duba tace,"Mum kun zo?". kallo ɗaya zaka yi mata ƙwalla ta cika idanunka, duk suka taso suka iso wajenta, ɗayan hannunta da babu canular shi ta dinƙa miƙa musu su na gaisawa tana amsa tarin adu'oin da suke tayi mata. tana duban Ammi ta ce,"Ammi Ummi bata zo ba?". "bata zo ba Fillo, muna dai tayin waya da ita, tana ta yi miki adu'a, tace kar ki yawaita raki kiyi ta adu'a". "Ammi ina ta daurewa amma na kasa yin nishin da suka ce, kamar dai ko ba zan haihu ɗin ba ne". "za ki haihu kar ki damu, insha'Allahu ƴaƴanki za su fito". "Allah yasa Ammi. don Allah a ki kira min Ummina". ta furta hakan ƙwayar idonta na mannewa akan fuskar Turaki da yake tsaye yana kallonta ya kasa tahowa wajenta. bayan sun gama wayar da Ummi, nurses ɗin su ka cigaba da tura gadon, suka tsayar da shi a gaban Turaki. duk sun kasa ɗauke ido daga na juna, ita da take cikin ciwo ita ce me ƙarfin halin yi masa murmushi, don a wannan lokacin Turaki baya iya jin ko murmushin menene zai iya yi, ko da ace kuwa haihuwar tayi, har sai ya ga ta koma asalin Fulaninsa da ya sani, ba wannan Fulanin da yake gani ba me ƙarfin hali. ta miƙa masa hannunta ya kama ya riƙe, ya zubar da gwiwoyinsa a gaban gadon yana ce mata,"sannu Fulani Nah, sannu ƴar aljannah". sai fuskarta ta juye zuwa tsantsar damuwa tace da shi,"kayi haƙuri Jannaty ba zan iya ba, nayi duk iya ƙoƙarina amma na kasa, Dr ɗin yace ƙugun maza gare ni ba zan iya haihuwa da kaina ba sai dai suyi min aiki". Turaki ya kasa ce mata komai, ya kifa goshinsa a gefen hannunta, ta ɗago ɗayan hannun dake da canular da ƙyar ta ɗora a kansa. "Ka kwantar da hankalinka don Allah Janna
🏠