ta zo ta kwantar da su tana yi musu wasa, idan zata yi aiki sai ta saka musu karatun alƙur'ani kafin ta fita.
yayin da suka girma su fara kiranta da Ummi, mahaifin su kuma su kira shi da Abie, ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata lokacin da zata fara shirya su cikin kayan makaranta, ta ba su lunch box na abincin su, sannan tayi driving ɗin su zuwa makaranta, yayin da suka dawo ta zauna domin yi musu home work ɗin da aka ba su, idan weekend ya zo sai su dinƙa yada zango a field su na yin wasa tare da ita, ko kuma suke shiga cikin swimming fool.
ita dai ta riga ta gama tsara yacca rayuwar jin daɗi zata kasance tsakaninta da ƴaƴanta, ba zata zamto ɗaya daga cikin irin uwayen nan da basa jan yaran su a jiki ba, ita zata zam yaranta na liƙe da ita ne ko da yaushe, ta dinƙa jin damuwar su suma su na jin tata, zasu zama manyan aminanta kamar yanda zata zame musu.
sai taji kamar zuciyarta ta ƙara girma da tsiron wata sabuwar ƙauna ta daban, ƙaunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan ƙaunar ta ɗa da uwa, irin ƙaunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri na son tabbatar da abinda kake so, Allah shahidi, shi zai yi mata shaidar irin son da take yiwa yaran, tana ƙaunar su fiye da ranta, a yanzu su ne rayuwarta, in har babu su tabbas babu ita.
har ƙarfe uku tana ɗakin yaran a zaune, sallolinta duk anan tayi, abinci ma da aka kawo mata anan taci, ko ƙwalli ɗaya bata bari ya zuba ba gudun karta ɓata musu ɗaki.
zuwa lokacin kuwa sun yi waya da Turaki yafi sau goma, bini-bini sai ya kirata yace ga shi nan yana hanya, kuma taji gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake tun san da tace masa tana jin mararta na ciwo sosai, kamar dai zata fara labour.
cikin mintunan da ba zasu wuce biyar ba bayan wayar su ta ƙarshe sai ga Turaki ya dawo, yana shiga ɗakin yaran ya ganta zaune akan darduma tana goge hoton enlargement ɗinsu ita da shi, fuskarta ta washe da murmushi, wani murmushi da Turaki zai iya cewa bai taɓa ganinsa a saman fuskarta ba.
"welcome back".
ya ƙarasa ya zauna a gabanta yana tankwashe ƙafafunsa, ya ƙura mata ido sosai yana ganin yanda take cije fuska, tana so ta ɓoye masa zafin ciwon da ke cinta, tana so ta ɗauko ƙarfin hali domin ta nuna masa babu komai, babu wani abu da yake damunta, babu wata matsala, duk saboda hankalinsa ya kwanta.
"kin ci abinci?".
"na ci, me ka taho min da shi?".
ya matso da ledar da ya shigo kusa da ita yana buɗewa. "irin naman da kike so".
ai ko nan da nan ta warci ledar, ta miƙa masa enlargement ɗin tace,"maƙala musu wannan, an manta jiya ba'a saka shi ba, mp3 ɗin su na karatun alƙur'anin ka bar shi a ɗakinka, ka ɗauko sai a ɗora musu a saman wancan table ɗin, ungo wannan diary ɗin sa min shi cikin wadrobe ɗin su, kasa shi ƙasan kayan Aayan".
duk maganar tayi ne a lokacin da ta fara cin naman, Turaki ya miƙe yayi duk abin da tace, san da ya kammala har ta gama cin naman, ya shiga tsokanarta da kura, kasancewar naman yana da yawa sosai.
sai da suka ƙara kimtsa ɗakin sosai sannan suka zauna a tsakiyar gadajen biyu, suka shiga hira, wata iriyar hira suke yi mai ratsa jiki, hira da zasu ce ba su taɓa irinta ba a tsawon zaman su, hirar da ta yiwa kowannensu daɗi matuƙa. kan Fillo na saman ƙirjinsa yayin da yake shafa gashin kanta, duk hirar da suke yi muryarta na fitowa ne tana ratsa dukkan ɗakin a hankali, cikin wani amo na rauni da ya gaza ɓoye dauriyar ciwon da ke cinta.
ana sallar magriba ciwon naƙuda me tsanani ya ɓallewa Fillo, lokacin tayo alwala kenan ta fito daga banɗaki, tayi saurin dafa bango tare da duƙawa a wajen tana dafe bayanta, a lokacin wata azaba ta tsarga jikinta, sai taji numfashinta kamar ya tsaya cak a maƙogoronta, taji kamar duk wani ɓurɓushi na halittar jikinta yana barinta gaba ɗaya.
ta rumtse ido na tsawon mintuna tana ambaton Allah cikin wata rarrauniyar murya, wani sabon bala'in zafi taji ya fara bin dukkan jijiyoyinta, sai taji ina ma ta kwasa a guje ta bar cikin ɗakin ta fita waje ko zafa sami sauƙi acan, sai dai ko yatsanta guda ta kasa motsawa, ji take yi tamkar an saka ƙaton dutse an danneta.
muryarta tun tana fita da ƙarfi har ta zo ta daina fita, lokacin Turaki ya shigo ɗakin kamar an hankaɗosa, dama tun san da zai tafi masallaci yaji hankalinsa bai kwanta ba, yaji gaba ɗaya ba ya so ya tafi masallacin gwara yay sallarsa anan, amma sai ta hana shi, ta tilasta masa akan sai ya tafi masallaci ya sami jam'i.
cikin tsananin tashin hankali ya ƙaraso in da take, cikin bala'in ruɗu na farat ɗaya yace,"kin gani ko, sai dai na faɗa miki ba zan fita ba".
"ka kaini a cire min su Jannaty, ba zan iya ƙara kwana a haka ba, don Allah ka taimaka min, zan mutu...".
Sauran harufan suka katse sakamakon wani sabon ciwon da ya murɗa mata, taji kamar an saka kibiya an soketa a tsakiyar cikinta da mararta.
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Fulani Nah daure mu fita".
ta kalle shi cikin hasken da zata ce a matsayin mutum uk