NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 307 of 323

acikin kayan Maama, kuma rigar sai tayi mata kyau sosai, saboda girman cikin jikinta sai awon yayi daidai da ita. "amma dai ba zaka jima ba ko?". amon muryarta ya fito a lokacin da take ɓalle masa maɓallin rigarsa. ya ce,"No yanzu zan dawo babu jimawa, takardun nan kawai zan kaiwa Khaleel, don't be lonely, am always with you, ina cikin nan". ya faɗa yana pointing saitin zuciyarta. tayi wani kalar murmushi tana kamo fuskarsa cikin tafukan hannunta biyu ta ce,"ina sonka mijina, ina ƙaunarka". "ni ma ina yi miki tsananin so matata, Allah yayi miki albarka, yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". "amin amin Daddyn little Maama". furuncin nata ya saka shi yin murmushi me faɗi, tare da duƙawa ya ɗage rigar jikinta ya yiwa cikin kiss, sannan ya ɗago suka yi kissing juna. da ƙyar ya iya sakinta yaje yana tattara takardun cikin sauri, ita kuma tana bashi labarin cewa,"Jannaty ka san me?". ba tare da ya juyo ba yace,"ban san me ba sai dai june". murmushin tayi sannan yace,"to ka san june?, tunda nake a rayuwarta ban taɓa hango kaina a matsayin uwa ba, ban taɓa tunanin zan ɗauki ciki ba balle har akai lokacin da zan haife shi". sai tayi shiru, yace,"ehen ina jinki lukutar Gombe". murmushi ya kasa ɗaukewa a saman fuskarta, tana kallon bayansa ta ƙara cewa,"sai ga shi Allah ya ƙadarta min ganin samun cikin, har zuwa watan haihuwarsa, zan haife ƴaƴa biyun da nagartaccen mijina ya bani su, na ƙagu in haife su Jannaty, ina tsananin son su fiye da kaina". cikin sigar zolaya yace,"har ni kin fi son su akaina?". ta ɗan taɓe baki tana kallonsa, da irin wasan da ke tsakanin mata da miji tace,"waye kai?". ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya mintsinin leɓenta, ya ɗora hannunsa a saman nata dake kan cikin. "yau kin ji sun juya?". ta ɗaga masa rigar tana faɗin,"kalla fa yanda suke ta ƙiriniya, duk sai duka suke kai min ta ko'ina, suma ai sun gaji da zaman". Turaki bai iya cewa komai ba illa shiru da yayi yana ta kallon cikin dake motsi, yana jinjinawa girman ƙudirar ubangiji. gaba ɗaya sai yake jin tamkar yasa hannu ya buɗe cikin ya ɗauko yaran, Fillo kuwa kallon cikin kawai take yi a gefe guda zuciyarta na saƙe-saƙen yacca rayuwar zata juya, yanda komai zai koma saɓanin tunanin su da hasashen su, yacca komai zai faru anan gaba kaɗan, nan da ɗan lokaci kaɗan ba me yawa ba, hakan take taji a jikinta. "ba fa na so yarana su yi kama da mijin lukutar gombe saboda bana so su yi muni, ka daina kalle min su". ya rungumota jikinsa yana cewa,"wallah ki roƙi Allah su yi kama da ni kiga yanda za'a dinƙa miki layi a ƙofar gida, in kuwa su kai kama da ke to kin shige su, ƙila sai dai mu ke kulle su a store". bayan fitarsa ta zauna a gefen gado, ta rufe idanuwanta a hankali, yayin da hannayenta ke ɗore akan ƙaton cikinta, ita ɗaya ke ta saƙawa wai yanzu halitta ce a cikin cikinta, halittar da ya girma kuma zai fito nan ba da jimawa ba, shikenan da zarar sun fito ita ma ta samu nata babies ɗin, irin wanda take gani daga nesa don bata iya ɗaukar jariri, za su fito a matsayin nata, yayin da zata amsa wannan sunan mafi daraja na Uwa, ƴaƴan su ita da Turaki, Ƴaƴan su ikon su. sai taji ƙwalla na neman taruwa a cikin idonta, ƙwallar da take ta zallar farin ciki da wani bala'in jin daɗin da ba zai misaltu ba. ta lumshe idanunta, ƙwaƙwalwarta na haska mata hoton yaran acikin kanta, ana jibi Hajiya Madina zata rasu ana scaning sai taji tamkar ta ɗauko su a wannan lokacin, babies ɗin su na kwance a cikinta gwanin sha'awa, ga sunan clearly a jikin screen cikin hoton black and white, kansu a haɗe su na ta watsal-watsal yayin da hannun kowanne ke gefen bakinsa, idanunsu a buɗe tarr tamkar kayi musu magana su amsa maka. kawai sai ta fara hasko yanda kammanin babies ɗin zai kasance, bata san ya Allah ya tsara halittar kamannin nasu ba, wataƙila su yi kama da su, wataƙila kuma su ɗauko kamannin su daban, sai dai a son samunta duk su ɗauko kamannin Turaki, ta yan da zata dinƙa kallonsa a fuskarsu idan baya gida, ba ya ga hakama idan suka ɗauko kamanninsa zasu fi kyau, irin wannan kyan da sai ta dinga tofe su da adu'a a kaɗawar kowanne sakan na agogo. tashi tayi akan gadon, ta isa gaban dressing mirror ta ɗauko diary ɗinta, sannan ta duƙa ta ɗauki riyon kayan babies, ta fita a ɗakin Turaki ta isa zuwa nata. wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu set ɗin kayan sanyi da Hajiya Ramla tayo mata aiken su a jiya, sannan ta fita ta nufi ɗakin kusa da na Turaki, ɗakin da suka ware domin yaran su, ɗakin da Turaki ya rufe mata ido ya shigar da ita sannan ya buɗe yana nuna mata yana faɗin for our coming kids. ɗakin tamkar already dama yara na rayuwa acikinsa, domin anyi decorating ɗinsa da duk wasu kayan wasan yara, komai na cikinsa pink and white, kayayyakin da almost siyayyar Marigayiya Hajiya Madina ne, sai ta isa gaban gadajen guda biyu, a wannan lokacin babu abin da ƙwayar idonta ta haska mata irin hoton yaran a zahiri, ta gama ba su nono
🏠