kina aikin patrol".
Ilham tayi dariya sosai tare da cewa,"Allah dai ya raba lafiya, ni ban ma fidda ran ba za ki haihu ba a yau".
sai kuma ta nunfasa ta ce,"zan je gida ne, an yi min waya jikin Mami ya ƙara tashi".
jikin Fillo yay sanyi tana me tunawa da halin da suka riski Fulani Azima a shekaranjiya da suka je dubata.
cikin sanyin murya tace,"Allah ubangiji ya bata lafiya, ko in je in shiryo mu tafi tare?".
"a'a ke da kike fama da kan ki, na faɗa miki bana fidda ran ba za ki haihu ba a yau, ƙila ma sai dai ai min waya ace Baby ya sauka. ɗa zu da asuba ai ina tayi miki dariya ta window".
Fillo ma tayi dariyar ta ce,"hmmm aikin mijinki ne, haka kawai duk ya jigatar da ni da safa da marwa, ke kinji yanda ƙafafuna ke ciwo kuwa. ai ana kaiwa gobe sai dai kuga na kai kaina asibiti sun yanka ni sun ciro muku yaran ku".
"da kanki ma za ki haihu insha'Allah, bari na tafi sai na dawo".
"to a dawo lafiya, ki yiwa Mamin sannu don Allah".
motar Ilham ta bar compound ɗin gidan, ita kuma Fillo ta shige part ɗin ta.
a ɗaki ta sami Turaki zaune yana rubutu a takarda, tun safe yake aikin rubuce rubucen office, tayi wurgi da hijab ɗin jikinta akan gado, kafin ta nemi waje ta zauna ta miƙe ƙafafu.
"Jannaty please come and massage my legs, Allah ciwo suke min sosai".
ya ɗago ya ɗora idanuwansa akanta, matuƙar tausayinta ya kama shi, in ace yana da ikon da zai fito mata da Babies ɗin nan babu abin da zai yi masa shamaki da hakan, ya ƙagu ta haihu haka ko don ta huta.
ya tattara takardun a gefe tukunna ya taso, kafin ya zauna a gabanta ta dakatar da shi da faɗin,"sorry ba ni riyon kayan su Maama".
ya ce,"me kuma za kiyi da shi?".
tayi masa wani kallo kafin tace,"kaji min mutum, me ake yi da gyara?, yau tun tashina ban gyara musu ba".
sai yay zamansa kawai, ta ɓata rai tana faɗin,"zan yi maka kuka". ta faɗa a shagwaɓe.
ya ɗago ido ya kalleta, sarai ya san zata aikata hakan, don haka ya miƙe yaje ya ɗauko ƙaton riyon da ke ɗauke da uban kayan Babies a ciki, ya ajiye zai zauna ta ƙara dakatar da shi.
"diary ɗi na". ya rufe ido tare da karyar da kai, zai yi magana tayi kalar tausayi tana haɗa hannayenta ta ce,"yi haƙuri Baban Ƴan biyu, ai don Allah nace".
sai da ya lakuce mata kumatu kafin ya fita ya bar ɗakinsa zuwa nata ɗakin, san da ya dawo tana waya da Boɗejo wacca ta kira tana tambayar lafiyar jikin nata.
ya zauna kawai ya shiga matsa mata ƙafafun, yana tsokanarta da lukutar gombe, bayan sun gama wayar da Boɗejo ta harare shi tare da fizgar diary ɗin tace,"ka duba min sirrina ko?".
"oho ke kika sani, ni me zan duba acikin diary ɗin da ake ɓoyewa kamar ana ƙulla munafurci a cikinsa, to ta ina ma zan iya gane watsaltsalun rubutun lukutar Gombe?, rubutun da ba iyawa aka yi ba".
dariya tasa Fillo dakatawa daga rubutun data fara,"oho dai duk abin mutum ba zai ga me ke ciki ba, ah tou! sirin mu ne ni da ƴaƴana"
"sirri ko munafurci?, yara tun basu zo duniya ba an fara koya musu hali mara kyau, ni dai gaskiya nake faɗa miki ki sauya hali, wannan ba halin zama mother ba ne".
ta ƙara yin dariya,"magana ce bata isheka ba sarkin ƴan sa ido, sirrin uwa da ƴaƴa ne dai ba zaka gani ba".
ta faɗa tana yi masa gwalo, sai ya sakar mata ƙafa suka shiga kokawa akan sai ya karɓi diary ɗin, ta ƙwalla ƙara babu shiri ya ƙyaleta yana aikin zaro ido da jera mata tambayoyi a hargitse.
"menene ya faru Angel?, na bige miki wani wajen ne?".
ta kashe masa ido ɗaya da cewa,"kasan idan baka daina takura min ba zan kaiwa Ilham jinginar ka, ka kwana dubu saba'in baka ganni ba".
"Allah ya baki haƙuri yallaɓiya ranki shi daɗe me girma uwar gida, da ki hora ni da rashin ganinki ai gwara ki zane min ɗuwawu na kasa zama, rashin ganinki ai azaba ne a gare ni".
"idan na mutu fa?".
sai ya ɗago yana kallon fuskarta da ta ƙara kyau yace,"ban hana ki yi min zancen mutuwa akan ki ba".
"Allah ya baka haƙuri ranka ya daɗe".
ta faɗa da murmushi a fuskarta.
bayan ta gama gyaran kayan Babies ɗin take ba shi labarin irin satar kayan da akayi ranar zaman sadaƙar bakwai ɗin Hajiya Madina.
"Daddyn Maama ka san me?, ina sabon less ɗin dana ɗauki zaninsa nace za'a ɗinkawa little Maama riga da shi?, to wallahi har da shi aka ɗauke, daga in ɗauko in ajiye kan gadon Mum in shiga toilet, ai kuwa na jera Allah ya isa babu adadi, saboda les ɗin nan Maama na sonsa".
yace,"Allah ya kyauta, rashin tsoron Allah ne duk yake saka sata a gidan mutuwa, Allah ya shirya masu yi kawai".
ta amsa da amin kafin ya kamata ta yunƙura su miƙe tare, toilet suka shiga domin yin wanka, acikin banɗakin sai da aka ɓata tsawon awa guda ana shan soyayya, sannan suka fito su na dariya, ita tana faɗin idan ya ɗauketa a yanda take yanzu ƙasusuwansa duk sai sun ɓalle, yayin da shi kuma ke faɗin ya sani, hannun lukutar gombe tsaf zai ɓalla shi ya ɓalle gaba ɗayansa..
kamar kullum yauma suka shirya kansu, ita ta saka wata ƙatuwar bubu da ta ɗauka