NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 305 of 323

. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce”. (Bukhari Wa Muslim). haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka. Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere. Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan. tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?. kuma rashin sanin amsar waɗan nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa. jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu. Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri. Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur’ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu. An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu. tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin. jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani. Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba. Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu. Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu. Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari]. me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri. Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba. muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa. mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah. domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi". ubangiji ba ya ɗaurawa wani rai face abin da zai iya ɗauka, Allah ya amince da mu, don haka mu ma muna buƙatar mu amince da iyawarmu ta cin jarabawa. Allah yasa mu da ce!. ƙarfe goma na safe a lokacin, Ilham ta fito daga ɓangarenta tare da wata yarinya da ba zata wuce shekara 8 ba. yarinyar ƙanwar Fulani Azima ce, aka bata ita kafin akaita makaranta, kasancewa yarinyar ta gama primary a halin yanzu. yarinyar na riƙe ne da jakar Ilham, tabi bayanta zuwa baƙar motar da taga ta shiga, sabuwar motar da me martaba ya bata kyautarta. a san da suka iso bakin gate domin fita, a sannan ne Fillo ke baro wajen Baba Me gadi da turtsetsen cikinta, da lokacin haihuwarsa kawai ake jira. Ilham ta zuge glass su na gaisawa da Fillo, da siririyar dariya a fuskarta tace da ita,"kin ga kuwa yacca kika koma?, Allah each and every day cikin nan kumbura ki yake ƙara yi". Fillo na kallonta tace,"ban da sharri dai". "Allah babu zancen sharri, jiya da muka ci dinner ba ki kumbura haka ba". Fillo tayi murmushi ta ce,"in ace ana mayar da cikin jikin wani ai ke zan mayarwa, ke ma ki ɗanɗana, ko da yake kwana nawa ne Allah na tuba, ina daga balcony zan ke hango ki a field
🏠