NOVEL SHARES -
alli gawar dake gabansu, wadda aka fito da ita daga cikin makara, a lokaci ɗaya suka tsinci kansu da tarin ruwan hawayen da ya bar idon su tun ɗazu.
a hankali Turaki ya durƙusa daidai kan gawar ya tallafo kan, Khalil da Samir da Baffa da Wan Hajiya Madina da Liman suka tallafi sauran jikin, sannan suka haɗu wajen zura gawar a cikin ramin ƙabarin.
lokacin da suka zura gawar acikin rabin ƙabarin, zuciyar kowannen bawa dake wurin ta matse da ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa, haka duk wanda bai tuba ba kafin mutuwa tabbas yay babbar asara.
idanuwan Turaki suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallon yacca ake mayar da ƙasar da aka haƙe ana rufe gawar gawar da ke ciki, har sai da hasken likƙafinin ya dusashe, yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi gaba ɗaya.
daga wannan lokacin kuma ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba, komai da ke cikin kansa ya zame yabar shi.
abin da zai ce yana iya jiyowa a duniyar da yake jinsa kamar ba'a cikinta ba, tarin adu'oin dake fitowa daga bakin liman, kafin a hankali kuma ya fara jin sautin wani abu na shiga kunnensa, sautin takun ƙafafu su na juyawa su na barin wajen.
sai ya kalli nasa ƙafafun, sai yake ganin tamkar ba zai iya ɗaga su ba, tamkar sun ƙame anan kenan har sanda tasa mutuwar zata zo ta riske shi.
yaji an riƙo hannunsa, da ƙyar ya iya ɗauke idonsa akan ƙabarin, ya juya ya kalli Baffa da Khalil, kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya fara tafiya da baya, a haka ya dinƙa tafiya da baya har ya bar cikin maƙwabartar, yana tafiya yana barin Hajiya Madina, yana kusantar gidan da zai koma a yau rana ta farko ya riske bata cikinsa, rana ta farko da zai koma bai ji muryarta ba na kiransa da wannan sunan da ita kaɗai ta raɗa masa, kuma ita ɗaya take kiransa da shi, Me Babban Suna!.
yaji wani uban gumi ya keto masa, ya wanke masa dukkan ilahirin jikinsa, a hankali kuma ƙwaƙwalwarsa ta karanto masa kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
shikenan sun yi tazara, tazarar da ba zasu ƙara kusantar junansu ba.
a lokacin da suka koma gida, tsakanin Khaleel da Turaki sai aka rasa wanda ya riga wani shiga ɗakin Hajiya Madina, an dai gansu sun shigo sun tsallake tarin mutanen dake zazzaune.
a cikin ɗakin na Hajiya Madina, Khalil na zaune a ƙasa, idonsa na manne akan gadon inda tayi baccin ƙarshe a duniyarta, yau rana ta farko da ya shigo ɗakin bai ganta ba kuma ko da ya zauna zaman jiranta ba zata shigo ba, shikenan ta tafi tafiya ta har abada, sun zama marayu, yanzu ba su da uwa, wannan jigon na jin daɗin duniya.
a hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kawai sai ya ajiye dukkan dauriyarsa, yay ƙasa da kansa, ya runtse idonsa da yake ganin hoton mahaifiyar tasa na haska masa, don haka saiya shiga rero kuka babu ƙaƙƙautawa, kuka tamkar ƙaramin yaro.
a wannan lokacin kuwa Turaki ya kifa kansa akan gadon, ƙamshin Maamansa na fitowa daga kan gadon na ziyartar hancinsa, yayin da yake damƙe da wannan ƙaton zanin da take cewa zanin goyon jikanta ne.
_"kwana ashirin da biyu ya rage Edd ɗin nata ya cika ko?, to Allah ya raba su lafiya. kaga Me Babban suna waɗan su gadaje na jarirai na gani da suka fi wanda na siyo kyau, mu sauya shi ko?"._
maganartata ta haska acikin kansa, shekaran jiya suka raba rana su na hira da ita, kuma yawancin hirar duk akan jikokin da taƙe ta burin ganin zuwan su ne, har daga ƙarshe ma take ce masa.
_"to ni ina ta lissafina ma, wa ya sani ko ba lallai ba ne na kai wannan lokacin, Allah dai ya san adadin shekarun da ya ɗiba mana a rayuwa, ni dai idan na tafi ku yafe ni Me Babban Suna ko da nayi muku laifi bisa kuskure"._
sai kawai yaji ya rasa dukkan dauriyarsa, ya manta shekarunsa, yana tunawa cewar shi fa ɗan Maamansa ne, kuma Maaman ta rasu a yau, bai san lokacin da wani matsanancin kuka ya kubce masa ba, ya shiga rero shi tamkar yaro sai dai gaba ɗaya babu sauti, illa tarin ruwan hawayensa da ke sauka su na jiƙa bedsheet ɗin.
har aka tura ƙofar ɗakin aka shigo tsakanin Turaki da Khalil babu wanda ya sani balle ya ɗago.
Fillo ta ƙarasa ta zauna akan gadon, tana zama kuma Turaki ya ɗago kansa ya ɗora akan ƙafafunta, ya damƙe cinyoyinta yana wani irin girgiza.
sai taji sabon kuka yazo mata, tunawa da tayi Nihal na can an rirriƙeta sai surutai take yi. saboda haka sai ta nutsa yatsunta acikin kansa tana motsa yatsun.
*BAYAN SATI BIYU.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*60*
*Jarabawa daga Mahaliccin mu.*
Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba.
A cikin Alkur’ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu