r akaita sai na zo, ya tafi ya nema mana ticket yanzu zamu taso Baffa".
"Zaytun kiyi haƙuri kinji ko, ki tayi mata adu'a kawai, idan aka ce za'a jira ku lokaci zai ƙure, kinga magariba na gabatowa".
bayan gama wayar ya ɗaga kai yana cewa da Yayar Hajiya Madina,"Asiya kirawo Ramla don Allah, tazo su yi sallamar ƙarshe".
"Baffa don Allah ku bar mana ita a haka ba sai an kaita wani wajen ba, mu zauna da ita a haka don Allah".
Yayan Hajiya Madina Baba Nafi'u yace,"tun ɗa zu kake ta surutai Sameer, ya isa haka, kai musulmi ne ya kamata ka yarda da wannan mutuwar, batun a bar muku ita babu shi domin binne gawa wajibi ne".
"don Allah Baba ku bar ta ko zuwa da safe ne, ƙila fa baccin ne yay mata nauyi da yawa, ko kuma shi likitan ne bai bincika da kyau ba, amma ɗazu mu ka gama hira da ita wallahi, wallahi lafiyarta ƙalau bacci kawai tayi tace idan Saamirawo(sirika Fillo) tazo to a tasheta".
Nihal ke maganar duk a gigice.
Baba Nafi'u ya ƙara cewa,"ku yi haƙuri kin ji Nihal, duk wani abu da ya ke faruwa tsarin ubangiji ne, namu tawwakali ne da addu'a, don haka ku yiwa mahaifiyarku adu'a".
Baffa ya numfasa a hankali ya shiga kiran sunan yaran nasa da sirikan nasa ɗaya bayan ɗaya.
"Khalil, Samir, Nihal, Halima, Ilham". sannan ya kalli Turaki daga ƙarshe yace,"Muhammad ku daure zuciyoyin ku, kuyi tawwakali ga Allah, wannan ita ce mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita, haka take riskar kowanne bawa ba sai an shirya mata ba, mu ma nan duk jiranta muke yi. yanzu lokaci na tafiya, mutane na can a waje su na jiran a fita da ita, na san abin da kowannenku yake ji, na san raɗaɗin da zuciyarku ke yi muku. ku yi mata adu'a, wannan kukan da ku ke yi da musawar da ku ke yi ba gata bane a wurinta, zallar soyayyar da za ku nuna mata shi ne kuyi mata adu'a, wannan jinkirin kaita ɗin da ake ba alkhairi bane agareta".
Maganar ta Baffa ta doki kunnuwan kowannen su, furucin da yay akan soyayya, sai kawai suka ji su na shuɗawa zuwa duniyar baya, wani lokaci me tsayi da ya shuɗe, kamar haka ne, kamar wannan lokacin su na zaune da ita take faɗa musu...
_"ku nuna min soyayyar ku ko bayan raina Ƴaƴana, ina nufin kar kuyi kuka da rashina, adu'a za ku yawaita yi min"._
Turaki ya matsa kusa da makarar, Baffa ya kalle shi, zuwa yanzu idanuwansa ƙamas babu alamun danshi na hawaye, haka fuskarsa tayi fayau babu wani abu da zaka tsinta a ciki illa tsananin tashin hankalin da yake ciki. haka shi ma Khaleel, wanda tun ɗa zu sai ayanzu da ya ɗora hannunsa akan makarar sannan hawaye yay nasarar gangaro masa, sai dai yay saurin saka gefen rigarsa ya goge.
hannun Turaki ya shiga cikin maƙarar, ya tallafo kan gawar, yasa ɗaya hannun ya yaye linkafanin ya tsayar da shi daidai wuyanta, inda fuskarta kawai suke iya gani, fuskar da suke gani tamkar zata yi musu magana.
muryarsa ta fito cikin sanyi, ya shiga jero tarin adu'oin da ya san su na cikin kansa, yi yake yi yana ƙara maimaitawa, har tsawon lokacin da bai san ya ɗauka ba me tsayi, har sai da Baba Nafi'u yasa hannu ya dafa kafaɗarsa yace,"ya isa haka Turaki".
shi kaɗai ne ya iya yi masa magana domin ko Baffa ba zai iya ba a wannan lokacin, shi kansa ya kifa kansa yana hawaye kamar yanda Hajiya Ramla da ƴaƴan suke yi.
"ke kam taki tayi kyau Madina, tabbas ke ɗin ƴar aljannah ce, ki yafe min Madina, don Allah don Annabi ki yafe min".
muryar Boɗejo suka ji ta amsa acikin ɗakin, a sanda take isowa wajen, kuma kukan da yaci ƙarfin ya hanata ƙarasa abun da zata faɗa.
har aka yi sallar jana'iza Turaki da Khalil basa cikin hayyacinsu sosai, a tsaye kawai suke, hannayensu sarƙe dana juna, yayin da idanunsu ke kafe akan makarar da ke ɗauke da gawar dake gabansu.
da ga bayan su kuma tarin ɗumbin jama'ar da ba zasu ƙirgu ba ne, don jama'ar gari yara da manya sun halarci jana'izar.
ƙarfe shida na yamma aka kai Hajiya Madina ƙabarinta, inda ɗumin jama'ar da suka fi ƙarfin ƙirga suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya.
acikin shirun da ya ratsa maƙabarta, babu sautin muryar da kake ji na tashi sai na manyan mutanen dake cewa.
"yauwa bismillah ku biyo ta nan".
"yauwa jama'a a ɗan gyara".
"ku riƙeta sosai".
"to ku miƙota nan".
"yauwa to ku ajiyeta nan, masha'Allahu!".
mutanen da suka ratso ɗauke da gawar ta cikin tarin ƙaburburan dake jere a cikin maƙabartar. suka ajiye makarar a bakin ƙasar da aka tone, kusa da ramin da yake gida matabacci, kuma gida na ƙarshe ga kowanne bawa, gidan da ke jiran duk wani mai rai, gidan da yake iri ɗaya da na me kuɗi dana talaka.
Turaki da Khalil na tsaye kusa da juna, tsayinsu kusan ɗaya, zuciyar kowanne na tunani kala-kala a game da mutuwar da ta riske su a yau. abun da basu taɓa zato ba, abun ba su taɓa kawo shi nan kusa ba, mutuwar ma da gaba ɗaya basa hasashenta.
"Bismillah".
Muryar limamin masallacin unguwar ta janyo Turaki da Khalil daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar su ta faɗa, suka juyo a tare suka kalle shi, sannan suka k