NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 302 of 323

ah za'a zare masa rai, wani daga bacci shikenan za'a zare ran, sai dai ya farka ya gansa a ƙabari, gidan da yake na gaskiya, gidan kowa. duk irin son mu da duniya wallahil azim sai mun barta, duk irin so da ƙaunar da muke yiwa juna wallahil azim mutuwa sai ta raba mu, Ya Qadeer kai mana kyakkyawan ƙarshe, Ya Rabbi kasa mu dace duniya da lahira Ya'ilahi! Ya Hayyu Ya ƙayyum, kasa mu mutu muna matsayin mutanen kirki, ba waɗanda zamu mutu duniya da mutanen cikinta na tirr da mu ba, ya Rahmanu kasa kar mu mutu da hakkin kowanne bawa akan mu, don mun san cewa baka yafe hakkin wani akan wani, ya jama'atul musulim mu yafi juna!, mu yafewa junan mu!, kar mu dinga ƙullar junanmu domin ba mu san lokacin da zamu yi tafiya me gaba ɗaya ba. "ta mutu". Khalil yay ƙarfin halin furtawa sauran ƴan uwansa da kowannen su ke tsaye yana so ya fahimci abin da ke faruwa. "Kamar ya ya wai? Mecece mutuwa kuma?". Sameer yay tambayar a rikice. "da ma haka ake mutuwar?, ɗa zu fa muka gama hira da ita ko awa ɗaya ba'a yi ba, haba this is insane, wallahi Dr ɗin nan ƙarya yake, ya za'ai ma Maama ta mutu, me tayi?, laifin me ta aikata?, don Allah Mum a kira wani likitan ya dubata, don Allah a kira wani likitan ya zo ya tasheta". idan ace ba kallon fuskar Nihal suke yi ba, za su rantse da Allah cewa ba ita tayi wannan maganar ba, don kwatakwata muryar ba tayi kama da tata ba, ta fito ne cikin wani amon sauti na ƙololuwar tashin hankali, tana rawa tamkar iska na kaɗata. haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙarasa, shi zai zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa, sai dai fatan dacewa kawai. "ka kira Baffan ku ka sanar da shi, sai ka kira min Samha da Zaytun, amma ban ce ka faɗa musu ba". Mum tayi furucin ga Khaleel, wanda yake tsaye har yanzu hawaye sun gaza sauko masa. a wannan lokacin kuwa Nihal na kan gawar Hajiya Madina, tana girgizata akan sai ta tashi, tana roƙon su akan su kira likita me hankali ya tashi mahaifiyarta, ai hirar da suka kwana jiya su na yi baya nufin wasiyya ta bar mata, ita dai azo a tashi Maama, don tace mata a ƙarshen watan nan zata fara yi mata order ɗin kayan kitchen ɗinta. a wannan lokacin kuma Turaki ya iya ɗago da kansa, ya kalli Nihal ɗin sannan ya kuma kallon fuskar gawar, sannan ya ƙara kallon zanin da aka rufe gawar hannun Fillo ke damƙe da shi, sannan ya kai ƙwayar idonsa kan Mum da ke zaune kanta a ƙasa, hawaye na saukowa su na zuba akan kayan da ke jikinta, sannan ya kalli Sameer da ke duƙe ya rufe fuskarsa da dukkan tafukan hannunsa da alama kukansa yake so ya tsayar tukunna ya ɗago ya ƙaryata mutuwar, sannan ya kalli Khalil wanda ke jingine a jikin wadrobe waya riƙe a hannunsa ya ƙurawa gawar ido, gashin idonsa ba ya ko ƙiftawa. a wannan lokacin ne kuma hankalinsa ya fara gaya masa wataƙila zai sauya ma'anar rabuwa ta mutuwa a yau, don baya tunanin akwai abin da zai raba shi da gawar nan da yake riƙe da hannunta, Maamansa ba, babu me raba shi da ita. *BAYAN AWA BIYU.* a cikin wannan awannin, labarin rasuwar Hajiya Madina ya karaɗe cikin garin gombe, da sauran ƴan'uwa da suke na kusa da na nesa. lokaci guda tarin al'umma suka shiga ɓulɓulowa su na sauka a gidan Alƙali Dikko domin yin ta'aziyya, mutuwar da ta taɓa manya da ƙanan yara. cikin gidan ya ɗauki shiru, a zazzaune ake wasu na kukan fili yayin da wasu ke kukan zuciya, domin tabbas anyi rashi, an yi rashin mace mai tsanani son mutane da kyautata musu, mai kirki da sauƙin kai, macen da ke da tsananin kyautatawa marayu, macen da ba'a faɗa da ita acikin mutane in har ba ƴaƴanta aka taɓa mata ba, macen da a tsawon rayuwarta babu wanda ya taɓa buɗa baki yayi kuka da ita, ya kuma ya faɗi aibunta. a wannan lokaci ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawansa, shi kaɗai ya san adadin alhinin da ke cikin zuciyoyin ahalin gidan Alƙali Dikko, musamman yaran, waɗanda suka ruɗe da koke-koke, banda Samha da ke ta aikin suma tana farfaɗowa ta ƙara komawa. "an gama yi mata wankan, ku faɗa musu za'a shigo da gawar ciki su yi mata adu'a". "ina Hajiya Ramlan take?". "yanzu ta tashi, Samha ce jini ya yanke mata, ana tunanin ko ɓari tayi". a lokacin wani tsoho ya leƙo parlon yace,"to ina yaran su ke ne?". "Baba Musa gasu nan fa, ku shigo da ita ɗin". ya juya fuskarsa daga waje yana kallon mutanen dake tsaye yace,"sai kun ɗago makarar da kyau fa, yawwa kai ɗan karkata ta can". mutanen maza su huɗu suka shigo parlon da gawar, da yake acan part ɗin nata wasu Kakanninta mata da su Boɗejo suka yi mata wanka. su ka ƙarasa da gawar suka ajiyeta a tsakiyar yaran da ke zaune a ƙasan carpet, wacca Zaytuna ce kawai babu sai Samha da aka yi asibiti da ita yanzu. Baffa ya ƙaraso wajen ya zauna shima, zaman nasa babu wuya kira ya shigo wayarsa, daga can ɓangaren Zaytuna da ke ta kuka tace,"Baffa don Allah ka
🏠