sami zama a gefen Hajiya Madina, sai ta ɗagota zuwa jikinta, sai taji gaba ɗaya jikinta ya saki, jikin Hajiya Madina ya zame daga nata ya koma makwancinsa.
ƙafafun Fillo suka tsuguna a kusa da Turaki, ta dafa kafaɗunsa hannuwanta na rawa, sai taji ɗan cikinta ya motsa a lokacin da ya riƙo nata hannun, ya juyo ya kalleta, suka haɗa ido tana ganin abun da bata taɓa gani ba acikin idonsa, ruwan hawaye!, ruwan hawayen da su ka sanya zuciyarta bugawa.
lokacin da Hajiya Ramla ta tabbatar da baccin Hajiya Madina ba na farkawa ba ne, lokacin tayi ƙarfin hali da dakiyar kallon Nihal, wacce ke tsaye ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, idanuwanta duk biyu a waje.
"Mum Maama bacci take yi ko me?, suma tayi?, zata farka?, ana ta tashinta taƙi ta tashi".
"idan baka saba aiki ba kayi to duk jikinka sai ya mutu, ina tunanin gajiya ce tasata wannan baccin me nauyi, ba sai mun tasheta bamu barta ta huta sosai".
sai ta juya ta kalli Turaki, ta ƙara juyowa ta kalli Nihal ta ce,"ina wayata?".
"Mum gata nan a hannun ki ai".
tsabar ruɗewa ta manta ma da wayar na hannunta, ta shiga contact ta danna kiran lambar Family Doctor ɗin su.
yana ɗaga tace da shi,"don Allah ka iso gida yanzu".
bayan ta ajiye wayar Nihal ta ce da ita,"Mum wa kika kira?".
"Dr Ibrahim ne".
sai a sannan Turaki ya ɗago ya kalli Mum, mene na buƙatar likita kuma a wannan lokacin?, idan ya zo me zai yi?.
su ka haɗa ido da Mum ɗin, tace da shi,"da yake tace min tana ciwon kai ɗazu, gwara ya zo ya dubata wataƙila BP ɗin ne ya hau ba mu sani ba".
ta fita a riki ce, tana sauka ƙasa taci karo da Sameer da Khaleel, sai suka tsaya kallon juna.
"da ma ba ku fita ba?".
Khaleel yace,"dawowa muka yi, lafiya Mum muka ganki a haka?".
"a'a babu komai, ko zaku koma kuga idan Baffa ya dawo?".
Sameer ya ce,"yanzu ya kira mu, yace ya kira wayoyin kowa bai samu ba".
"to ku tsaya anan ku kira min shi a waya".
ta faɗa tana juyawa ta koma saman, Khaleel ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da nazari da zurfin tunani.
a san da Dr Khamis ya ƙaraso, idanuwan kowa na kansa a lokacin da yake wasu dube-dube a fuskar Hajiya Madina, da kuma gwaje-gwajen da yake yi.
ban da Turaki da idonsa ke kan Maama kawai, yana jin wani bala'in ruɗani na shigarsa.
cikin ƴan mintuna kaɗan Dr Khamis ya gama bincikensa, a sannan ne kuma idanuwan Turaki su ka koma kan likitan, yana kallonsa ya matsa kusa da Mum da Khaleel, wanda yake tsaye cikin ƙarfin hali. ya san dai likitan bayani yake yiwa su Mum, domin yaga bakinsa na motsawa, laɓɓansa na motsawa da harufan da riga ya san ma'anar su.
kuma cikin sakanni uku sai ga Hajiya Ramla ta dawo kusa da Hajiya Madina, ta kamo hannayenta ta riƙe acikin nata, kafin a hankali laɓɓanta su tale da furta kalmar,"innalillahi ra'inna ilaihi raji'un, gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma".
furucin da ya haddasa motsawar zuciyar Turaki sannan ƙarfin bugunta ya ƙaru a lokaci ɗaya.
idanuwansa su na kallo Mum ta ɗauki zani ta rufe Hajiya Madina da shi, ta rufeta har fuskarta, ta lulluɓeta da wannan zanin da ta ɗauko a jiya tace musu ta siyo shi ne saboda goyon jikanta.
ba zai manta da wannan lulluɓin ba, ba zai manta da shi ba har a bada.
sai kawai ya kifa fuskarsa akan ƙirjin gawar, hannunsa na dama kuma ya shige cikin sanyayyan nata hannun na dama.
"Maama, Maama, don Allah ba yanzu ba Maama".
yay maganar da wata karyayyar murya, a san da yay wannan furucin, a sannan ne hawayen da suka taru acikin idonsa suka sami nasarar gangarowa saman kumatunsa. idanuwansa suka runtse, hoton rayuwar su na tsawon shekaru 27 na haska masa daki-daki, a lokaci ɗaya kuma duk wani sauti na muryarta na amsakuwa acikin kunnensa da cikin kansa, sautin muryar da ya tabbatar ba zai ƙara jinsa ba.
ya riga ya sani, faɗar ubangiji ce kullu nafsin zaa’iƙatul maut, Allah ya faɗi hakan har sau biyu a littafinsa me girma, duk wani bawa mutuwa tana kansa, duk wani me rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yaro ko yarinya, babba ko ƙarami, sabo ko tsoho.
ya sani Mutuwa dole ce, ya san mutuwa akan kowa ta ke, ka aikata sharri ko akasin haka zaka mutu, kana kan aikata daidai ne ko akasin haka, baka san a wani hali za'a ɗauki ranka ba, za mu mutu a yau, ko gobe ko jibi, ko anjima ko yanzu, sai dai dukkanin mu babu wanda yasan a wanne hali zata riske shi, kai dai bawa baka sani ba! baki sani ba!
ya sani yin mutuwa ko ambatonta bai da daɗi, amma dole ne sai mun mutu, dole za mu koma ga wanda ya halicce mu, wajibi ne mu amsa kiran ubangijin mu mai son mu, mai ƙaunar mu, mai jiran tuban mu a ko yaushe, dole ne zamu bar duniyar da aka ara mana, haka dole zamu tafi mu bar duk abin da muke so, haka dole zamu kwanta a ƙabari.
kana tsaka da jin daɗin rayuwa mutuwa na iya zuwar maka, wani tazo mishi fuj’an, wani ta zo mishi idan yay fama da rashin lafiya, wani tari kawai zai yi, wani atishawa kawai zai yi, kuma da zarar ya furta Alhmadulillah sai Kaga a wannan lokacin an ɗauki ransa, wani yana sall