wa gadon, da tafukan hannunsa guda biyu ya kama kan Maama ya gyara mata kwanciyar.
ya zauna akan bedside drower yana kallon fuskarta, kamar tayi haske?, kamar kuma ta ƙara yin kyau?, sai yasa hannunsa a saman goshinta ya goge guntun gumin da yake ganin kamar idanuwansa na haska masa.
wucewar minti ɗaya!, biyu, uku har zuwa biyar, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da baccinta, saboda haka sai ya kai hannunsa gefen filon, ya shiga dukan filon a hankali yana faɗin,"Maama, Maama, Maama".
ya kira sunan sama da sau goma amma shiru bata buɗa idanunta ba.
a yanda ya sani, duk tsananin baccin da Maamansa ke yi kiran suna ɗaya ne ya farkar da ita, balle ma ita bata da irin nauyin baccin nan, hasalima ko baccin take aka murɗa ƙofa aka shigo sai ta farka, ko kuma idan taji motsi.
dan haka zai iya cewa bai san lokacin da ya miƙe daga kan drower ɗin ba.
kuma maimakon zama a bakin gadon kamar yanda yayi niyya sai ya tsinci gwiwoyinsa da zubewa a ƙasa, kafin yaji wani nauyi ya ziyarci hannunsa, irin nauyin da sai da ƙyar ya iya ɗaga shi ya taɓata.
"Maama".
hannunsa ya sauka akan jikinta da yay sanyi, a yanzu da ya taɓata bai ga ta farka ba, haka bai ji ta motsa ba, sai yaji adadin faɗuwar gabansa ya ninku da kusan kaso tamanin da biyar.
sai kawai ya tsinci kansa da shiga tashinta kamar ƙaramin yaro, babu abinda yake da buƙata a yanzu irin ta tashi, ta buɗe idonta, ta kalli cikin ƙwayar idonsa kamar yanda zai kalli tata, ta faɗa masa wannan maganar da tace zasu yi idan ya dawo, bai taɓa jin ya damu da baccinta ba irin yau, bai taɓa jin baccin wani ya tsorata shi ba irin yau, bai yarda da wannan baccin ba, bai yarda da shi ba sam.
girgiza ƙafafunta kawai yake yi yana kiran,"Maama, Maama, Maama ki tashi na dawo, kin ce Papaya ta ƙare na taho miki da ita ga shi na siyo, ga takardar scaning ɗin jikokin naki ma na karɓo, su biyu ne kamar yanda kika gan su a mafarki.
kuma mun yi magana da Baffan yace za'a buɗe makarantar islamiyar, idan ya so sai a haɗeta da boko, kuɗin da kika ce na kai gidan marayun na kai ga receipt ɗin, amma sun ce na faɗa miki akwai yara guda goma sha biyar da aka kwantar a asibiti, to sai naje asibitin na biya bill ɗin da ake buƙata, waɗan nan yaran ma da aka kai su sudan, sun kira ɗa zu sun ce na faɗa miki result ɗin su yayi kyau, gobe za su sauka a ƙasar nan, sun ce na faɗa miki su na sauka wurin ki za su fara zuwa, su na ta cewa ayi miki godiya su da iyayen su. gwandar a markaɗa ko yanka miki za'a yi?".
gaba ɗaya a wani ruɗe yake maganar, kamar dai wanda ya susuce, ya juyo ya kalli Fillo da Nihal waɗanda ke tsaye a bayansa.
"Nihal ɗauko wuƙa ki yanka mata gwandar".
sai kuma yace da Fillo,"Halima taci faten?". a karo na farko da ya taɓa ambatar ainihin sunan Fillo.
"a'a naga tana bacci shiyasa ban tasheta ba".
"sauri ki zubo mata Halima, yanzu zan tasheta".
kusan a tare Fillo da Nihal suka juya jiki duk a sanyaye, hannayen Fillo na karkarwa ta buɗe flask ɗin ta zuba faten tsakin da yawa, kafin ta yunƙura ta miƙe daga duƙen da take Turaki yazo ya karɓa, karɓar tasa tayi daidai da shigowar Nihal daga ɗauko wuƙar, ta ɓara ƙwallon gwadar ta yi masa wata iriyar rabawa, cikin sauri ta isa ta ajiye plate ɗin akan table ɗin da Turaki ya ɗauko ya ajiye a gaban gadon.
har yanzu baya jin mazaunansa za su iya zama akan wani abu, don haka ko a yanzu ma gwiwoyinsa ƙara zubewa suka a gabanta, kafin yasa hannu ya juyo da kwanciyartata saitinsa, ya kalli fuskarta, ya kalli murfin idonta da yake a rufe, sannan ya kai ɗaya hannunsa ya kamo tsintsiyar hannunta guda ɗaya ya riƙe, tare da kai ɗaya hannun nasa ƙasan hancinta.
jijiya bata motsi!, haka ma numfashin baya fita!, sai ya ƙara maida hannunsa wuyanta, nan ma beat ɗin dake wurin baya harbawa. ya san akwai suma kuma ya san akwai mutuwa, kamar yanda ya san banbancin kowanne, sai dai baya jin zai iya ɗaukar abin da yake ganin gaskiya ya ɗora Maama a wannan matakin, ba zai iya ba, ba kuma ya jin zai iya.
don haka sai ƙafafunsa duka biyun suka tankwashe, yayinda da dukkan hannayensa ke riƙe da nata, a sanda kuma ƙwayar idonsa ta kasa ƙiftawa akan fuskarta.
"ba ki taɓa yin bacci me nauyi ba irin na yau Maama, ba ki taɓa ba. tun ina ƙarami ba kya iya baccin rana kawai saboda mu, balle ma har ki sami damar yin me nauyi, amma yau zan bar ki ki huta, ki yi baccinki yanda ya kamata, na san kin gaji ne, zan zauna tare da ke har sai kin farka".
a lokacin da yay shiru da maganar, a lokacin yaji tarin ruwan hawaye sun cika ƙwayar idonsa, zubowa suke so suyi ya sani, amma ba zai ba su damar hakan ba har sai abun da yake gudu akan farin cikinsa ya tabbata.
shigowar Hajiya Ramla ɗakin yasa shi juyawa ya dubeta, sai ya ganta gaba ɗaya a rikice, cikin irin rikicewar nan da bai taɓa ganinta aciki ba.
"Madam, Maaman yara, kar muyi haka da ke, kar kiyi mana irin wannan baccin, tashi haka don haka don Allah Madam".
zantukan da Hajiya Ramla ke yi kenan a sanda ta