ta suka miƙe tare, kai tsaye kitchen suka wuce, suna shiga ƙamshin egg ya shiga hancinsu, idonsu kuma ya kai kan wanke-wanken dake cikin sink, Zaytuna ta dube shi, shima ita ɗin yake kallo idonsa na haskawa da irin abinda nata ke haskawa.
"but yaushe Maama ta sauko har tayi girki ban sa ni ba?".
"may be bata san ka shigo ba, ko ka shiga ɗakinta?".
"nop, time ɗin dana shigo bata tashi ba ai".
Fitowa suka yi daga kitchen ɗin, Zaytuna ce ta kula da Fillo bayan da Turaki ya haye upstairs, ta kalleta da murmushi a fuskarta tace,"sannunki".
Da yake Fillo ta shaidata ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, Zaytuna ta amsa tana tambayarta lafiya tayi tsaye anan.
"Kaka ce bata da lafiya shine na amsheta".
"ohh kece jikartata dama?".
ta gyaɗa kai,"eh ni ce".
Zaytuna ta sakko daga step na farko data hau, ta dafa kafaɗar Fillo tana kallon fuskarta, haka kawai taji yarinyar ta burgeta.
"sannunki, kina da kyau sosai...amma jikin Kakar da sauƙi ko?".
"ehh na dai barta tana bacci".
"Allah ya bata lafiya". Zaytuna ta faɗa tare da kai kallonta kan dining ɗin, tana buɗe plate tace,"ke kika girka?".
"a'a Hajiya ce, babu jimawa ta hau sama. tana ta yi min bayanin wanda zaici abincin to ban gane ba ne".
Zaytuna na murmushi ta ƙara dafa shoulders ɗinta tace,"na Hammah ne, ba ki lura da shi ba ne a zaune?".
Fillo tace,"nayi zaton Alhajin gidan ne".
Zaytuna da Nihal wadda ta shigo yanzu taji abinda Fillo tace suka saki dariya tare.
"Lallai kuwa Alhajin gidan, yau an maida Hammah tsoho...ke sai kace mara gani sosai ki kasa banbance dattijo da matashi".
Nihal ke faɗa.
zata hau upstairs ta ke cewa da Zaytuna.
"Adda kije Baffa na kiranki".
"oak, to kice da Hammah ya sakko ga breakfast ɗin nasa".
Nihal ta haye upstairs ita kuma Zaytuna ta fita, suka bar Fillo tsaye a wurin. da jikin bango ta jingina har sanda Hajiya Madina suka sakko ita da Nihal da Turaki, da shirin fitarta ta sakko hakan yasa tayi mata adawo lafiya, babu jimawa Turaki ya dawo daga rakiyan da suka tafi yi mata.
yana waya da Bello Ƙaraye ya shigo, ya zauna kan dining ɗin ba tare daya taɓa abu guda na abincin ba. har sanda ya gama wayar Fillo dai na nan tsaye kamar soja, wasa kawai take da yatsun hannunta, hanakalin na can wurin Kaka, tana ta zullumin wannan bawan da har yanzu bata sami kallon fuskarsa ba ya samu ya sallameta tayi tafiyarta.
Turaki na danna waya ya ɗago ido ya kalleta suka haɗa ido, tayi saurin ɗauke nata, shi kuma ya kalli kayan abincin sannan ya ƙara kallonta ta gefen ido. maganar Maama na dawo masa cikin kansa, wai ita tayi helping nata da greating taruhu da yankan albasa, to taya ma zai soma cin abicin da wannan yarinyar ta saka hannu?.
wani ɓacin rai ya ziyarce shi, ai ko abincin restaurant ba kowanne yake ci ba, balle kuma na wannan abar. yau bai san me ya sami Maama ba, ita da ta ke haƙura da ko menene akan buƙatarsa kawai, amma yau akan wani meeting har tana haɗa dafuwar abincinsa da ƴar aiki.
murya a tamke yace da Fillo,"ja kujera ki zauna".
Ba dan tasan su biyu ne kawai ba da sai tayi zaton ko da wani yake, tunda babu wata alama da ta nuna da itan yake. kuma duk da hakan dai sai ta tsaya, domin tasan kujerar da yake magana tafi ƙarfin zamanta.
Ita duk rayuwarta ma bata taɓa ganin irin kujerun ba ma.
kusan 2minutes da maganar tasa ya ƙara ɗago ido yana mata wani duban yatsine, yay saurin kauda kansa a tsawace yace,"do you want me to repeat my self before you sit?".
Saurin rufe ido tayi tare da ƙanƙame jikinta, sai rawar jiki ta ke yi kamar me jin sanyi. A rayuwarta ta tsani tsawa, bata sonta ko kaɗan, tsawa na firgitata, tsawa na sakawa ta kusa fita a hayyacinta, tsawa na sakawa ta tuna wani moment da bata son tuno shi a rayuwarta, tsawa na sawa har suma tayi, dalilin da yasa a ko yaushe ta ke guje duk abinda zai sa ayi mata tsawa.
tafi minti uku kafin ta dawo normal, da ƙyar ta iya haɗiye yawun bakinta, a hankali ta buɗe ido ta sauke su akansa, irin kallon da yake yi mata gani ta ke kamar zai duke ta...idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta shiga ƙiftasu gudun kar su zubo, ta kama jan yatsun hannunta tana danasanin zuwanta, da wannan abun da yayi mata ai gwara tayiwa Kaka gardamar ba zata zo ba.
ta kalle shi suka haɗa ido, ta yi saurin ɗaukewa tana jin faɗuwar gaba.
Muryarsa har cikin kanta ya ƙara cewa,"Do I look like someone who would talk to you and ignore?".
Da ƙyar ta iya buɗe ido tana kallon yatsunta, shi wai bai san bata jin wannan yaren ba ne da yake ta ɗaga mata murya da shi. ita bata san ba ma ko abincin ma baya ci da kansa sai an bashi, ƙilan shi yasa yake tayi mata wannan ihun, to ai ba laifinta bane laifin babarsa ne da bata yi mata wannan bayanin ba, kuma ma ya za'ai ace wannan ƙaton ba zai iya cin abinci da kansa ba, banda dai lalacewa.
in cool voice dake rawa tace masa,"kayi haƙuri ka daina ɗaga muryar, ni ban san me kake cewa ba shi yasa, bana jin wannan yaren".
Yay ma ta wani uban kallo kafin yace,"na farkon m