NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 299 of 323

kuma sai ta ɗauki wayarta ta kira lambar Hajiya Madina, har kiran ya katse bata ɗauka ba. sai ta miƙe tana cewa da Fillo,"na bar ki anan ko zamu je tare?". "ina Mum?". "wajen Maaman ku. naga tun safe ban ji ɗuriyarta ba, ƙafana na ciwo ban sami damar leƙawa ɓangaren nata ba, ina ta kiran wayarta kuma bata ɗaga ba". Fillo tace,"ai ba mu jima da gama waya da ita ba Mum, ita ma ta kira ni ai". Hajiya Ramla ta sauke numfashi, tayi gaba yayin da Fillo ta bi bayanta. shigar su parlon Hajiya Madina kiran Turaki ya shigo wayar Fillo, tana ɗaga yace da ita. "Fulani Nah kin ƙarasa gidan?". "na je Jannaty, lafiya naji ka kamar a damuwa". "babu komai. yau ɗin ne kawai nake jinta duk babu daɗi, ina Maaman?". "yanzu ai na shigo ɓangaren nata, ban hau saman ba". "kowa a gidan yana lafiya?". "Jannaty wai...". "just answer me". "kowa lafiya lau, Mum ma muna tare da ita". ya sauke numfashin da ta jiyo har cikin dodon kunnenta. "ina kan hanya ne go slow ya tsare ni. amma insha'Allah yanzu babu jimawa zan ƙaraso gida". san da ta shiga ɗakin Hajiya Madina ta tarar da Hajiya Ramla na taɓa jikinta, a yayin da take yin magana da Nihal tana tambayarta,"kuma bata ce miki bata jin daɗi ba?". "a'a Mum, ba ma fa ta jima da kwamciyar ba ai, lafiyarta lau". "to masha'Allah, idan ta tashi ki ce ta kira ni a waya. zan je saboda baƙin Haɗeja da za su zo". "tom Mum". Hajiya Ramla ta fita, Fillo ta ƙaraso ciki ta zauna a gefen gadon da Hajiya Madina ke kwance tana bacci. ita ma tasa hannu ta taɓa ƙafar Maaman sai taji babu zafi kamar yanda kowa ke tunanin ko zazzaɓi ne ya sata yin baccin rana haka. "Allah yasa ba ciwon kai ba ne". Fillo ta faɗa tana cire mayafin jikinta ta ajiye, tare da naɗe ƙafarta ɗaya ta ɗora akan gadon gaba ɗaya. Nihal da ke kan kujera tana aikin project a system tace,"lafiyarta fa lau, ko 10minutes bata yi ba da kwanciya, tace idan kin zo ki tashe ta". "ta fita aiki ne yau?". "a'a haka kawai ta tashi da gyaran part ɗin Baffa yau, nace yau dai soyayya ake ji". Fillo tayi dariya tana faɗin,"amma dai kin tayata?". "ina zuwa ma ce tayi in bar mata ɓangaren miji ita ɗaya take so ta sami ladan". shiru ya gimla na kusan mintuna biyar, Fillo ta miƙe taje ta ɗauko basket ɗin abincin, a ƙasa ta zauna ta buɗe ta zuba iyakar wanda zata ci a plate, Nihal ta taso ta zo ta zauna su ka shiga ci a tare. "gaskiya yayi masifar daɗi, no wonder Maama tace ba zata ci komai ba sai kin kawo mata, bari na tasheta yasin tun zafin flask bai jiƙa shi ba". "no barta tayi baccinta please, abu da an kusa la'asar, lokacin sallah nayi za ki ga ta tashi". bayan wucewar mintuna goma hannayen Turaki su ka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙafafuwansa suka shigo cikin ɗakin yayin da sanyin Ac ke ratsa shi. ƙwayar idonsa bata sauka akan kowa ba sai Maama da ke kwance kan gado tana bacci. A lokaci guda yaji jikinsa yayi wani irin sakayau tamkar an zare masa lakar jikinsa, abun da bai yi tsammani ba sai yaji yawun bakinsa ya bushe, Me ke shirin faruwa ne?. ya saki handle ƙofar da yake riƙe da shi, ya kasa ɗaga ƙafarsa yana jin wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani irin abu mai nauyin gaske, yana jin yanayin bugawar zuciyarsa na sauyawa, yana jin faɗuwar gabansa na ƙaruwa. ya san da cewa don mutum yayi bacci ba wani abu ba ne, dan bacci wani abu ne da ɗan adam ke yinsa a kowanne dare, to amma ba zai iya cewa ga ranar da Maama tayi bacci ba da rana, iyakar tsayin rayuwarsa zai iya faɗin hakan, ko da ace kuwa tana cikin halin jinya ne, baccin rana baya daga cikin al'amarin rayuwarta. to amma yau ɗaya, rana guda, rana ta farko kawai sai ta kwanta irin haka?, ƙarfe ɗaya da rabi na rana, har tayi irin baccin da bata ji buɗewar ƙofar tasa ba, kuma a lokacin da ya san tana zama tayi lazimin sallar azahar?. kawai sai ya ji wani abu ya motsa a ƙasan zuciyarsa, yaji kamar rauni na shirin kama shi, sai dai kamar ko da yaushe a rayuwarsa, yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa da dauriyarsa tare da dakiyarsa, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe. "me ya sami Maama?". ya jefa tambayar ga Fillo da Nihal yana tsaye a gefe guda. "bacci take yi, aiki tayi ta gaji". "aiki!?, ina ma su aikin?". "part ɗin Baffa ne fa Hammah, ka san bata barin ƴan aiki su je can". "gajiya bata sakata baccin rana, tasha magungunanta?". "lafiyarta fa ƙalau Hammah, kawai muna zaune muna hira tace bari ta kwanta kafin ta gaban goshinta ta ƙaraso". ya shiga girgiza kansa, ƙafafunsa na ɗagawa da ƙyar, haka ɗaya Maama ba zata yi baccin rana ba, no matter what bata baccin rana, bai yarda da wannan baccin nata ba. "kar ka damu lafiyarta fa ƙalau, ban da yanayin ciwon kai da sai ka tashe ta". kunnuwan Turaki su ka tsinci muryar Fillo a cikin iskar ɗakin. ta karɓi ledojin da ke hannunsa tana ƙara faɗin,"Allah lafiyarta lau, amma idan kana ganin a tasheta ɗin to". "a ƙyaleta?". ya gyaɗa kansa kawai, sannan a hankali ya tafi zu
🏠