NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 298 of 323

o koma ciki, tana shiga kitchen ɗin ta kira lambar Hajiya Madina. daga ɓangaren Hajiya Madina ta ce,"Daughter yanzu nake shirin kiranki, ina ta jin kewarki na damu na, idan babu abin da kike yi ki taho yanzu, in Me Babban suna ya dawo sai ku tafi tare". Fillo ta ce,"Maama faten tsakin me nama nayi, kina so ko nayi miki me kifin?". fuskar Hajiya Madina ta washe da murmushin jin daɗi, duk duniya tana bala'in son souls ɗin nan guda biyu, Turaki da Fillo. "kar ki wahalar da kanki, ba sai kin ƙara ɗora wani ba, zanci wanda jikana ya ci". "to Maama idan na zo ba zan dawo ba, yau ba'a ɓangarena yake ba". "to shikenan. ki hanzarta ki zo Daughter, ina so zan yi wasa da jikana, ina so yau nayi ta kallon fuskar ki". Fillo na murmushi ta kalli cikin da ke jikinta, haka Hajiya Madina take yi, aikinta yanzu bai wuce tasa Fillo a gaba ba tayi ta magana da cikin tamkar a gaske, in anyi dariya sai tace ai ita tana jinsa su ne basa ji, kuma idan ya fito zai ba su labari ne. haka ɗaya yau zuciyar Fillo taji tana so ta yafewa wannan mutumin da ta manta a rayuwarta, kamar ta yafewa Amir, sai ta rumtse idonta ta hura iska a bakinta ta fita daga kitchen ɗin. tana tayar da mota kiran Ummi ya shigo wayarta. "Auta kina lafiya?". "lafiya lau Ummi". "masha'Allah, ina zaune naji ina kewar ki". "wallahi nima Ummi jira nake naje gidan su sai muyi vedio call da ke, yau kawai ina ta kewarki sosai fiye da da. Ummi na yi mafarkin Abba ma, yace in gaida ke, sai naji kamar na bi shi Ummi". *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *59* idan mu ka duba fuskar rayuwa, zamu ga gaba ɗaya tana tafiya ne based on yanda Allah (SWT) ya tsara mana. rayuwar mu na tafiya ne daidai da yanda ubangiji ya rubuta mana tun kafin zuwan mu duniya. duk hasashenmu, duk lissafin mu, duk yanda muke so, duk yanda muka tsara, duk yacca muke tunani, duk yanda ba ma so, duk yanda muke gudu, duk yanda muka yanke, to haƙiƙa yanda ubangiji ya rubuta mana hakan ne zai kasance, kuma na ubangiji shi ne daidai. sau tari idan muka duba fuskar rayuwa, zamu ga duniya tana yiwa wanda ya jima yana aikata laifi talala, zai ta aikatawa yay ta aikatawa, kafin ya ankare sai ya farga lokacin tuba ya ƙure masa, wani Allah zai iya nufar sa da tuba kafin mutuwa, wani kuma ba zai sami wannan damar ba, haka zai wuce lahira da tarin ɗumbin zunubi. haka sau tari zamu ga rayuwa ta rufta da wanda zai aikata laifi sau ɗaya tal a rayuwarsa, nan da nan sai ya fuskanci hukunci abin da muke tunanin me aikata babban kuskuren shi ya kamata ya karɓa. haka zalika idan mu ka ƙara duba fuskar rayuwa, abin da duk mu ka sani shi ne asiri gaskiya ne, tun da har yaci shugaban mu fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW), kuma tasirin adu'a ya warka da shi, har aka gano wanda yay wannan sihirin. sai dai abun da yake da akwai a tamu rayuwar, ba ko da yaushe Allah ya ke tona asirin waɗanda suka zalunci wasu bayin Allahn ba, sai dai ubangiji yay wa bawansa sakayya kawai. idan mu ka ɗauki ɓangaren masu aikin asiri ga wani wanda bai ji ba bai gani ba saboda son zuciya da tsantsar zalunci. zamu ga a yayin da suka yi asiri sun yi nasara, sai dai ƙarfin adu'a kan karya wannan asirin na su komin tsayin shekarun da za'a ɗauka, yayin da wasu za su sami waraka suci gaba da rayuwar su ta yau da kullum, yayin da wasu kuma warakar zata zama ajalin su. sai dai fa abin da yake da akwai ko da asirin ya karye to bai zama tilas dole ba a san wanda yay wannan asirin har kuwa duniya ta naɗe, duk da cewa a yanzu ubangiji ya daina barin wannan ladan gabar, sanda za'a barka kayi ta yawo da hakkin mutane har ka mutu sai anje ƙiyama tukunna. a'a! a wannan rayuwar da muke ciki ta yanzu, tun a duniya Allah yake wulaƙanta mutum, rayuwa tayi kacakaca da shi, tayi masa ɗaurin goro, wataƙila ma ya faɗa tsananin wuyar da ta fi ta wanda ya jefa a ciki, har sai ma ubangiji ya so ka da rahmarsa sannan zai baka damar roƙon yafiyar wanda ka zalunta, idan kuwa aka yi rashin dace ubangiji bai baka damar fallasa kanka ba, balle har ka nemi yafiya, to lallai wata shari'ar sai dai a yi ta kuma a lahira. a lokacin da motar tata tayi parking a compound ɗin gidan, ta fito daga ciki riƙe da babban flask na abinci a cikin basket, ta jingina da jikin motar domin numfasawa, saboda yanayin nauyin cikin jikinta. Auwal ɗan me gadin gidan ya ƙaraso wajenta cikin sauri, bayan sun gaisa ya karɓi flask ɗin domin taimaka mata, bata hana shi ba saboda ita ma tana buƙatar ataimaka mata ɗin, duk da flask ɗin ba wai nauyi ne da shi ba, kawai dai ko ƙaƙa abu yake yana yi mata nauyi a yanzu. part ɗin Mum tana fara nufa, a parlo ta sameta tana kallon news da ake yi, ta zauna suka shiga gaisawa Mum na tambayarta yanayin jikin nata. a lokacin da Fillo ke kallon Hajiya Ramla tace,"Mum lafiya dai ko?". tayi tambayar duba da yanayin Mum ɗin da ta gani, fuskarta da damuwa sannan ga jikinta kamar a sanyaye. "babu komai Daughter, kawai yanayin garin ne na yau". tana faɗin hakan
🏠