an zauna yay ta tunanin yaushe ne zai mutu?, kuma ai na?, taya zai mutu ɗin?, mene zai iya zama ajalin nasa?, sai dai waɗannan tambayoyi babu wani mahaluƙi da yake da amsar su, mutuwar ce kawai take zuwa da kanta, walau ɗan Adam ya shirya mata walau bai shirya ba, ko ana so ko ba'a so, da zarar ta zo tafiya kawai ake yi, ta datse wannan numfashin da bawa yake fitar da shi, acikin jin daɗi wa ko akasin hakan.
mutuwa ita ce kaɗai abar da ke iya yanke ƙaunar da ke tsakanin uwa da ɗanta, ko miji da matarsa, ko masoyi da masoyiyarsa, ko aboki da abokinsa.
ta kan zo ne bagatatan ba tare da ta sanar ba, sau tari mu kan kasance tare da mutum, kuma a yayin da aka sami giftawar wani lokaci bayan rabuwar mu sai muji ance wane ya rasu, ko kuma wane ya mutu, a lokacin ne zamu yi tunanin me ya sami mutum?, taya za'ai ace ya mutu bayan muna tare a ɗa zu muna hira cikin wasa da dariya?, to ita mutuwa haka take, ta kan ɗauki bawa ne da lafiya ko ba lafiya, kuma a lokacin da wani ke kan hanyarsa ta zuwa duniya, a lokacin mutuwa ke ɗaukar wani ta raba shi da wannan duniyar duk son da yake yi mata kuwa, hakana duk son da ake yi masa.
in ace mutuwa zata bar wani don wani yaji daɗi, da tabbas bata raba ɗa da mahaifiyarsa ba a lokacin da yake zuwa duniya ba, wata uwar kan samun damar ganin yaronta kafin mutuwar ta ɗauketa, yayin da wata yaron na fito ita kuma zata yi sallama da duniyar.
a lokacin da aka ce mutuwa ta raba mu da wani mutum da yake sashi na jikin mu, ruɗewa da tsananin shiga tashin hankali tare da fitar hayyaci kansa mu gaza yarda da cewar an mutu ɗin, anyi tafiyar da babu dawowa, har ta kai ga ba ma gama yarda da cewar tabbas mun rasa wannan da muke jinsa wani ɓangare na jikin mu, har sai lokacin da aka ɗauki gawarsa acikin makara, aka tafi da ita zuwa maƙabarta, aka kama gangar jikin aka zura acikin ramin ƙabari, har a jera tukwane akan gawar, da ƙasar da za'a zuba akan tukwanen, sannan a shafe hasken farin likkafanin dake lulluɓe da gawar.
a sannan ne zamu yarda da tabbas an tafi, an yi tafiyar da ba za'a sake dawowa ba, tafiyar da ba zaka ƙara ganin mutum ba sai a lahira, har ko da yaushe fatan guda ɗaya ne, mu mutu muna masu aikata alkhairi, mu zama masu cikawa da imani, mu zamto mun mutu ana yabon mu.
a lokacin da kumburarrun ƙafafuwanta ke sakkowa daga matattakalar benen a hankali, a lokacin take jin wani baƙon yanayi yana ziyartarta, a lokacin take jin wani abu da bata saba jinsa ba, wani irin yanayi ne take jinta a ciki, wanda ya ke zarcewa har can ƙasan zuciyarta, ya motsa zuciyar tare da abin da ke cikinta.
sai a lokacin da ta isa parking lot, tasa key ta buɗe motar, sannan ne ta fahimci kamar kewa ce take kamata, kamar dai zata yi kewar wani abu me muhimmanci a rayuwarta.
sai dai abu guda ɗaya take so ta sani, menene dalilin da yasa take jin jikinta yayi sanyi sosai?, irin wannan sanyi da bai taɓa ji ba.
wayar da ke riƙe a hannunta tayi ringing, duk irin farin cikin da take shiga a sanda taci karo da kira daga gare shi, yau sai taji wani mix feeling ya kamata, taji kamar tana tausayin shi me kiran ba ita kanta ba da take zama da ƙyar tashi da ƙyar.
ta ɗaga kiran ta kara a kunne cikin jin sanyin jikin da ya ƙaru a gareta.
"uwar ƴaƴana ina kewar ki, kullum idan bana tare da ke sai in ji ina kewarki kamar zan mutu, na kasa yin aiki yau gaba ɗaya, tun da na shigo office na zauna nayi jugum, sai nake jin kamar ban taɓa kewar ki ba sai yanzu ne zan fara, gabana yana faɗuwa, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, yau jina nake tamkar maraya, kuka zan yi Fulani Nah, ina jin kamar zan yi kuka irin wanda ƙanan yara ke yi, Fulani Nah in taho gare ki yanzu?, in zo in kwanta akan ƙijinki in dinga jiyo sautin bugawar zuciyarki a yayinda kike lallashina?, jikinki kawai nake buƙata ayanzu Fulani Nah, ina ji daga yau ba zan ƙara matsawa daga kusa da ke ba, zan daina fita aiki saboda ke, kina lafiya Fulanin Turaki?".
maganganun da suka fito daga bakinsa kenan, kuma maganganun da suka haddasa wata muguwar faɗuwar gaba a ƙirjin Fillo.
bata san lokacin data shiga motar ta zauna ba.
"ki shirya yanzu kije wurin Maama, yanzu zan taho, ba zan iya zaman office ɗin ba, ina so yau mu yini tare, hira nake so muyi sosai, ɗa zu ta kira ni tace min faten tsaki take sha'awar ta sha".
Fillo ta dafe goshinta,"Laaa ƙwara da Allah yasa ka yi wannan zancen, kamar na sani na dafa mata shi tun ɗa zu, kuma kaga har na fito zan tafi na kai mata ashe na barsa ban ɗauko ba".
"ki bata ta ci da yawa Fulani Nah, duk yawansa kisa ta ta cinye shi kin ji, tana sonsa, shi ne favorite ɗinta, ta ce me kifi take son ci, in few minutes zan iso gare ku, ki kula min da kan ku, zan siyo miki mangoro, Maama kuma zan siyo mata gwanda".
"tom Jannaty sai ka dawo, nima yau kewarka da nake yi ta banbanta da ta ko yaushe".
"Fulani Nah saura 20days mu zama Mum and Dad ko?".
"insha'Allahu Jannaty".
"Allah yasa ki haihu da ranki da lafiyarki".
bayan gama wayar ta su Fillo t