in dai namiji ne sunan Abba zamu saka, idan kuma macece zamu sa sunan Maama, in kuma twins ne duka maza zamu sa sunan Abba da Baffa, idan twins ne duka mata sai mu sa Maama da Ummi".
"Mum kuma fa?".
"ita ma zamu saka nata idan kin ƙara haifar wasu twins ɗin".
"wai haka Doctor ɗin yace maka twins ne?".
"hakan nake fata Angel".
sai ta marairaice fuska, idonta ya ciko da ruwan hawaye, ta damƙe hannunsa ta ce,"Jannaty ina tsoron haihuwa, an ce akwai wahala".
tausayinta ya kama shi,"kar ki damu Angel insha'Allah ke kalar taki haihuwar zata banbanta da ta su, cikin sauƙi zata zo miki".
"Allah yasa. amma Jannaty ka dinƙa yi min adu'a kullum na haihu da raina da lafiyata, ina so na raini yarana da kaina domin in ba su ilimi ingatacce tare da ba su kyakykyawar tarbiyya, ba na so na mutu a lokacin dana san ƴaƴana za su buƙace ni".
sai kawai ya gangara motar gefe yay parking, yacca jikinta yay sanyi haka ma nasa, ya juyo ya kalleta yaga tana zubar da hawaye, ya janyota ya rungumeta.
ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"Jannaty bana so su tashi acikin maraicina, ina so su ma suji wannan daɗin na uwa".
lokaci ɗaya Turaki yaji idonsa ya ciko da ruwan hawaye, yana shafa bayanta yace,"mene kuma na zancen mutuwa Angel?, don Allah ki daina, da izinin ubangiji da ranki da lafiyarki za ki haihu, kuma insha'Allahu ubangiji zai ba ki aron tsawon ran da har auran ƴaƴanki za ki gani".
ita dai bata iya cewa komai ba, kuma har suka ƙarasa gida jikinsu duk yay sanyi.
Fillo kuwa tana shiga bedroom ɗin Mum ta rufe fuskar ta, saboda haɗa ido da su da tayi, don samun su tayi zaune su ma duk cikin farin ciki, kuma ganinta kowa ya shiga mata adu'ar Allah ya raba lafiya.
Zaytuna da Samha sai tsokanarta suke yi wai ta zama uwar biyu.
tun daga wannan ranar kuma Fillo sai ta koma rayuwar gidan su Turaki, don ƙememe Maama taƙi barinta ta koma can gidanta tace sai cikin yayi ƙwari, duk ranar kwananta nan Turaki yake zuwa sai su tare a ɗakinsa na gidan.
sosai Fillo ke jin daɗin yanda Mum da Maama ke tarairayarta, musamman a wajen Hajiya Madina, don rainon cikin take yi cikin kulawa ta musamman daga wurin Kakarsa Hajiya Madina.
macen da kullum cikin siyan kayan jarirai take yi, hatta gadon Baby tana zuwa saudiyya ta taho da shi, motsin Fillo kaɗan ta tambayeta me take so.
Rayuwa ta cigaba da tafiya, a yayinda wasu abubuwan rayuwar kan sauya, lokaci yana tafiya a kullum kuma a ko da yaushe. wani lokacin cikin farin ciki wani lokacin baƙin ciki.
A duk lokacin da agogo zai motsa, lokaci ne yake wucewa, lakacin da baza a sake maimaita irinsa ba, lokacin da ba zai taɓa dawowa ba.
Sau da yawa ɗan Adam ya kan ƙagauta akan lokaci ya zo masa, musamman idan ya ƙosa akan cin burin wani abu da ya saka a ransa, sai ya gaza fahimtar irin saurin da lokacin yake yi, har sanda zai ankare da zuwan wannan abin da ya saka a ransa, anan ne zai ga tamkar ansa igiya ne ana janyo wannan lokacin.
hakan take a ɓangaren Fillo, tun daga ranar da likita ya ƙayyade musu watanni biyar a matsayin watannin da zata ɗiba kafin ta haife abinda ke cikinta, daga wannan ranar ta ƙosa da zuwan lokacin, zuwan ranar, sai ta koma ko da yaushe cikin kallon kaɗawar agogo take, cikin lissafa kwanakin kalanda, cikin haddar kwanakin da muke shiga muna maimaita su, cikin lissafi da hasashen irin soyayya, kulawa, ilimi tare tarbiyar da zata bawa abin da ta haifa.
sau tari mu kan yiwa kanmu lissafin tanadin abubuwa, sai dai abubuwa sukan zan zo mana ne a yacca ubangiji ya tsara mana ba yacca muka tsarawa kanmu ba.
wani lokacin ɗan Adam kan iya ƙirga sautin fitar numfashinsa, ba tare da ya san lokacin da numfashin nasa zai daina fita ba, fitar da ba zai ƙara samun damar ƙirga shi ba.
buri wani abu ne da kowanne ɗan Adam ke cin sa, sai dai ba duka burin ɗan Adam ne ke cika ba, kuma sau tari cin buri na katsewa ɗan Adam ne a lokacin da numfashinsa ya daina fita.
Rayuwa babbar nasiha ce ga kowanne ɗan Adam, akan ya gane cewa ba komai ba ne yake da tabbas ba a rayuwa, idan aka cire lokaci, lokaci ne kawai yake da tabbas, sai dai ɗan Adam ba shi da tabbas ɗin zai kai kowanne lokaci na bugawar agogo, ko tabbas ɗin lokacin da yake ta lissafawa rayuwarsa.
ubangiji ya riga ya ƙayyadewa kowanne bawa iyakacin lokacin da zai ɗiba a duniya, numfashin wani zai daina fita ne a bugawar sakan, yayin da numfashin wani zai daina fita ne a bugawar minti, kowanne bawa na tafiya ne kawai akan lokacin rayuwarsa.
a rayuwa ba ko da yaushe ne ɗan Adam yake yin murmushi ko dariya ba, ba kowa ne yake samun damar rayuwa tare da wanda yake ba, ba kowa ne yake samun rayuwa a irin yacca yake so ba, babu wani bawa da ke samun ɗorewar farin ciki a rayuwarsa, fa ce wataran sai yayi kuka.
*MUTUWA*, ita ce tabbatacciya, kuma ita ce abar dake kan kowanne rai, wacca bata da wani banbanci a tsakanin me kuɗi da talaka, babba ko yaro, me mulki ko mara mulki, ita ce wacca bata barin wani don wani yaji daɗi.
sau tari ɗan Adam k