ta ta balcony, fuskarta ta gaza ɓoye jin daɗin da take ji, yay murmushi kawai tare da juyawa ya koma ciki domin ya sanarwa da Ilham ita ma ta shirya ta tafi, tun da kusan yaune yinin bikin gidan.
da rana taro yay taro, cikin taron mutanen da ake ta ɗaukar hoto Fillo ta yanke jiki ta faɗi.
cikin tsananin tashin hankali Hajiya Madina da Hajiya Ramla suka sureta aka yi asibiti.
zuwan su babu jimawa sai ga Turaki shi ma ya ƙaraso, cikin matsananciyar damuwar da ta kasa ɓoye kanta ba.
ya zauna kusa da Maama, ta dafa kafaɗarsa tace,"ka kwantar da hankalinka insha'Allahu ba wata matsala ba ce babba".
Mum ta kalle shi rai a ɓace tace,"na jima da fahimtar kana ƙuntatawa yarinyar nan. to wallahi kaji na rantse maka muddin silar ɓacin ranka take kwance anan sai ranka yayi mugun ɓaci".
wucewar mintuna ashirin su na zaune jungum jugum sai ga likita nan ya fito, ya buƙaci cewar wani acikin su ya biyo shi.
Hajiya Madina tace da Turaki ya tashi yaje, ya shiga office ɗin Dr jikinsa a matuƙar sanyaye, duba da yayin da yake gani akan fuskar likitan.
"Bismillah zauna".
ya faɗa yana yi masa nuni da kan kujera.
Dr ya ɗauko file ya buɗe, ya dubi Turaki ta cikin glass ɗinsa sannan ya ce,"Halima Borkinɗo right".
Turaki yay saurin jijjiga masa kai,"yes".
Dr ya sauke numfashi, ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce,"kun san cewa ta kamu da heart failure?".
"mun sa ni Dr".
"to amma ya akayi ku ka yi sakacin da har damuwa tayi mata yawa haka?, tana fa ƙoƙarin barin matakin farko da take ciki ne ta shiga na gaba".
Turaki ya sauke doguwar ajiyar zuciya bai iya cewa komai ba. haushin kansa yayi matuƙar kama shi.
"anyway ga wannan drugs ayi gaggawar siya mata, gudun samun matsala babba. and a kiyaye sosai da duk abin da zai haifar mata da damuwa kar a kai stage ɗin da Babynta zai cutu".
idanuwan Turaki suka ƙanƙance yace,"Baby?".
ya tambaya da mamaki sosai.
Dr ya jinjina masa kai,"ƙwarai Baby, ko ba ku san tana da ciki ba ne?".
bakin Turaki ya buɗe, duka haƙoransa suka yo waje,"i din't get you clearly Dr, wanne irin ciki wai?".
Dr ya faɗaɗa murmushin sa, yana kallon Turaki yace,"zauna da kyau kar ka faɗi".
sai ya ɗebo sauran takardun da ke cikin file ɗinsa ya zubewa Turaki a gabansa ya ce,"ashe kamata yayi in fara yi maka congratulations, so you are expecting a baby in the next five months Insha'Allah, a test ɗin da aka yi mata ya nuna mana cikinta yana cikin wata na huɗu ne, but how comes duk baku yi noticing ba?"
Turaki ya kasa amsa tambayar Dr, sai ɗaga hannu sama da yay yana godewa ubangiji.
ya daɗe a hakan kafin ya mayar da hankalinsa kan doctor ɗin yace,"thank you very much, ga wannan kasa mai a mota".
ya ajiye masa kuɗi saman table ɗinsa, hakan kuma yayi wa Dr daɗi sosai, nan da nan ya shiga bawa Turaki shawarwari akan yacca za su kula da cikin.
Turaki duk ya ƙosa ya miƙe akan kujerar, hannu ya miƙawa Dr ɗin su kai shaking, tukunna ya fita a office ɗin bakinsa sam yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki.
kai tsaye room ɗin da Fillo ke kwance ya wuce, a ciki ya sami Maama da Mum, lokacin ta farka tana zaune, sun sakata da tambayar me take son ci, ita kuma duk ta narke tana faɗawa Mum wai Mangoro take so me warin gawasa.
kallo ɗaya Mum ta yiwa Turaki ta zunguri Maama suka fita suka bar ɗakin, su na fita ya rungume Fillo da farin cikin da ba zai iya misaltuwa ba.
ta ture shi daga jikinta tana turo baki gaba tare da ɓata fuska.
"ni ka matsa daga kusa da ni".
yay murmushi me sauti yana zura hannunsa cikin rigarta, cikinta ya shiga shafawa yana faɗin,"ta ya zan barki alhalin akwai ajiyata anan?. congratulations very soon za ki zama Mother".
ta yi masa wani kallon mamaki, ya ɗaga mata gira duka biyu,"am serious Angel".
sai ta kulle idonta tana jin wani daɗi na tsarga mata, ta kai hannayenta duka biyu ta dafa cikin tare da hannunsa da yake kai.
"Allah ka azurta ni da zuri'a ɗayyiba".
ta faɗa hawayen farin ciki na sakko mata, Turaki yay kissing ɗinta a goshi tare da faɗin,"amin summa amin uwar ƴaƴana, i love you so much".
lokacin da suka fito su Maama har sun wuce, duk kunyar da yake ji, bai iya haƙuri ba sai da ya ɗaga waya ya kira su Maama ya sanar musu.
bayan sun gama wayar ya kira Bello, yana ɗagawa yace da shi,"Bello ai na zan sami Mangoro me warin gawasa?".
Bello ya ce,"yanzu na mayar da farantin tallan gida, ya ƙare tass da yake yau anyi ciniki".
Turaki yay tsaki,"kai dai kana da matsala".
"to MT haka kawai sai ka kama wani kirana kana tambayana in da zaka samu mangoro, hanyar kasuwa ne baka sa ni ba ko me?. ni don Allah kace a bani matata yau wallahi duk na gaji a matse nake".
Turaki yaja dogon tsaki ya kashe wayar, ya kamo hannu Fillo dake dafe da ciki yace,"sorry Angel, duk in da mangoro yake zamu samo shi yanzun nan, ki tayani bawa Baby haƙuri".
sai ya kuma ya fara ce mata,"yanzu idan namiji ne wanna suna zamu saka masa?".
"ai kai kake da wannan alhakin".
"to