NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 294 of 323

ita. "ta wurinki zan fara samun matsala kenan ko?". Fillo ta miƙe ta ce,"zan wuce ɗaki, Allah ya bamu alkhairi ya tashe mu lafiya, sai da asuba ranka ya daɗe". tana faɗa ta wuce upstairs cikin natsuwa, Ilham ma ta bar parlon kamar wacca iska ke tunkuɗawa. tun da Fillo ta koma ɗaki taji bacci ya ƙara ƙauracewa idanuwanta, ta gaza danne abin da take ji a zuciyarta don ta samu ta saita kanta, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe take, bata taɓa zaton zafin kishinta ya kai har haka ba sai yanzu, tayi saurin faɗawa toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah. salloli tayi ta jerowa, gani take kamar idan tayi kuskuren sallamewa zata iya yiwa kanta rauni. bayan ta idar tayi zamanta akan dardumar tana tasbihi, lokaci zuwa lokaci sai ta sharce ƙwallar da ke sakko mata.. zuciyarta zafi take yi mata sosai, hatta kanta jinsa take yi tamkar zai rabe gida biyu, gaba ɗaya jin duniyar take babu daɗi sam, wataƙila in ace yau ba zata yi kwanan gidan nan ba da zata iya samun sassaucin raɗaɗin da take ji a zuciyarta. a can ɓangaren Turaki kuwa tun komawarsa ya tarar Ilham ta rufe ƙofa, bai ko bi ta kanta ba ya wuce ɗakinsa, sai dai tun da ya koma zuciyarsa ta gaza yi masa daɗi, tazara!, irin tazarar nan da bai taɓa zaton zata kasance tsakaninsa da Fillo ba, ko da sukai shariyar juna ya kan shiga duk dare yaga sleeping beauty face ɗinta. ya zata ji yau zata kwana a ɓangarenta ita ɗaya ba tare da motsinsa a sashin nata ba?, sai yay shiru kawai tare da rufe idonsa, haka kawai ya ji ya damu sosai akan halin da yasan babu makawa tana cikinsa yanzu. ya san yay mata rashin kyautawa, bai kamata ya shareta ba har ya canja mata ya zamar mata wani kalar mutum na daban da bai raineta akan hakan ba. tabbas tana buƙatar rarrashinsa ko ya ne, tana buƙatar kulawarsa da rarrashinsa a wannan daren ko zata samu bacci, don kamar yanda ya san kayarsa ne daren yau ba lallai ne ta iya bacci ba. wajen sha biyu saura aka turo ƙofar ɗakin a hankali, tun bata ɗago kai ba ƙamshin turarensa ya daki hancinta. ta ɗago domin ganin shigowar ko ta lafiya ce, kallo ɗaya tayi masa ta watsar. kallo ɗayan da tayi masa ya fuskanci tayi kuka ne har ta godewa Allah, don idanuwanta sun yi mugun kumbura, sai kawai ya tsinci kansa da matsanancin tausayinta a ransa. ƙarasa shiga yay, ya zauna a gefen dardumar, ya dinƙa kallonta yana ganin yacca taƙi ɗago ido ma ta kallesa, kenan bata ko ƙaunar ganinsa a yanzu?. kafin ya buɗe baki yay magana yaga ta miƙe, taja dardumar ta jefar da rabin ƙafarsa da ke kai, ta ninke sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta haye saman gado. ji tayi ya biyota kan gadon, tayi saurin miƙewa zaune tana cewa da shi,"ka tashi ka fitar min a ɗaki". ta faɗa murya a karye, yayin da hawaye ke sakkowa saman kuncinta, hawayen da yake jin su har cikin ransa tamkar ana hura huta a zuciyarsa. ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa, sai taji ta kasa ƙwacewa, kawai ta kifa kai akan gwiyarta, tayi kewarsa har bata san iyaka adadinta ba. Cikin kwantar da murya ya soma magana yana faɗin,"na san ban kyauta miki ba akan canjawar da nayi miki, tsawon kwanaki tara kenan ina ƙuntata miki, ba zan hana ki jin haushina ba, amma ki yi haƙuri don Allah, ni ma nawa ranne babbu daɗi, tilasta min da aka yi akan mayar da auren nan duk shi ya dagula min lissafi ". tsabar tuƙuƙi da ɗacin dake tasowa a ƙarƙashin zuciyarta, tun da ya fara magana har ya kai ƙarshe bata ko kulasa ba, haka bata ɗago kai ta kalle shi ba, sai ma zame hannunta da tayi a nasa. Turaki ya gyara zamansa, ya matsa kusa da ita ta yadda numfashinsu yake gauraya da na juna, ya riƙo hannayenta duka acikin nasa yana murza lallausan tafin hannun nata, ya kifa goshinsa saman kanta yana sauke numfashi. baya jin a duniya akwai wata mace da zata kama zuciyarsa kamar ƙaramar yarinyar nan, kullum cikin adu'a yake yi Allah kar yasa sai ya rigata mutuwa. cikin hikima da iya tsara zance na miji ya shiga bata baki, yayi amfani da duk wasu kalamai da za su kwantar mata da hankali da shigar da nutsuwa cikin zuciyarta, har sai da yaga alamar hucewa a saman fuskarta. but hakan duk bai sa Fillo ta samu sauƙin zafin kishin da take ji ba, abu ɗaya kawai ta sani mijinta yana mata tsananin so, kuma yana sonta fiye da ɗayar matarsa. da kansa ya sauƙa ƙasa ya dafo mata indomie, ya zo ya sakata a gaba taci da ƙyar saboda lallamar da yake yi mata. tamkar ɗacin magani haka ta dinƙa cin indomie ɗin, but babu yanda ta iya sosai take buƙatar abinci, dan zata iya cewa rabonta da wani abu a ciki tun kunun gyaɗar da ta sha a gidan Yusuf. sai da ta kwanta sannan Turaki ya bar ɗakin, tana jin fitarsa ta ƙara fashewa da kuka, ba wai don tana so ba sai dan bata ma san lokacin da yake zuwar mata ba ɗin. washe gari da sassafe kuwa sai ga text ɗinsa akan ta shirya ta tafi gidan na su. tsabar farin ciki da jin daɗi bata san lokacin data tura masa da reply ɗin thank you ba. lokacin da ta fito zata tafi yana hango
🏠