y a gefen gadon kafin yasa hannu ya yaye blanket ɗin da ta rufa da shi, ya rumtsa idonsa a lokacin da idanuwansa suka sauka akan cikakkun breast ɗin ta da ya kwan biyu bai haɗu da su ba.
Fillo ta buɗe ido a lokacin ta zabga masa harara tare da faɗin,"lafiya?". ta faɗa murya a sama kamar ba ita ba.
ba tare da ya kalleta ba ya miƙe tsaye, ya zuba hannayensa cikin aljihu sannan yace da ita,"ki sauko ƙasa ki same ni, ina so zan yi magana da ku".
taja blanket ɗin ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me yace ba. ya juyo yana kallonta,"ba magana nayi miki ba kika koma ki kwanta?, me kike ji da shi ne yanzu?".
ta ƙara jan blanket ɗin ta rufe har kanta, yana tsaye yana ta kallonta yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ransa, ya fi ƙarfin minti uku a tsaye Fillo bata ko motsa ba balle yasa ran ma zata tashi ne, ya jijjiga kansa ya fita ransa a mugun ɓace.
yana sauka ya tarar Ilham ta shigo a lokacin, tana tafiyar yauƙi ta wuce ta zauna kan kujera, sai kallon parlon take yi tana taɓe baki kamar wacca taga kashi, mamaki take yi sosai har cikin ranta, bata taɓa zaton kaya masu shegen kyau da tsada ba ne aka zubawa Fillo.
kusan zata ce kuɗi daidai ne da nata, kuma in har ba son zuciya ba colour ɗin funitures ɗin Fillo sun fi nata kyau sosai ma.
sai da aka kwashi kusan mintuna goma kafin Fillo ta sauko, sanye take da hijab har ƙasa, fuskarta wasai kamar bata da damuwar komai, sai ma bacci da ya fara nuna alamarsa a fuskartata.
tun da ta taho Ilham ke kallonta idanuwanta kamar za su faɗo ƙasa, zuciyarta tayi mugun bugawa da wani masifar kishi, ta haɗiye yawu da ƙyar a maƙoshinta, dama har haka Fillo ke da azababben kyau bata sani ba?, a yau dai ba zata so zuciyarta ba kam Fillo ta ci uwar ubanta a kyau, kyan nata har tsoro ya bata, yarinyar ta koma kamar ba ita ba, ta ƙara fresh da kyau me matuƙar ɗaukan hankali, sai ƙyalli take yi, ga shi kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana ɗauke da ciki, bata san lokacin da wani uban gumi ya wanke mata wuya ba, ta damƙe hannunta a jikin kujerar tana ji kamar ta tashi ta bar parlon.
Fillo ta wuce ta kashe tv, sarai ta san Turaki kallon news ɗin yake yi, ya bita da kallo, tun ɗazu yake a hasale da ita, ya lura ta ɗauki salon rashin mutunci, dole zai taka mata burki tun kafin akai ga nisa, don ba zai ɗauki wannan banzan halin ba, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai ɗauke idonsa akanta ba, so yake ya karanci ma'anar murmushin da yaga tana yi tun da ta sakko.
"i'm sorry Jannaty, haɗewa nayi da shaf'i da wutri shiyasa na ɗan ɓata lokaci, i hope hakan bai ɓata maka rai ba".
tayi maganar tana kallon Ilham ta ƙasan ido, wacca ta cika tayi fam tana kallon yacca Fillo ta wani maƙale a kusa da Turaki.
Turaki ya sauke numfashi ya dube su gaba ɗayan su, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga yi musu nasiha akan zamantakewar su, ya faɗa musu yacca yake so zaman su ya kasance, ya faɗa musu abubuwan da yake so su kiyaye gudun ɓacin ransa da na su.
daga ƙarshe kuma ya tsara yadda kwanakin kowacen su zai kasance, sannan ya ba su damar jin ta bakinsu, Fillo na wasa da yatsun hannunta ta ce,"duk yanda ka yanke Jannaty ni kam yayi min".
ya kalli Ilham, wacca ke kallonsa fuskarta na bayyana rashin amincewarta akan hakan, sai da ya ɗaga mata gira ya ce,"ehen, ko kina ciwon baki ne?".
ta kawar da kai gefe guda tana cin nagani ta ce,"da dai ka ƙara, kwana biyu sai kace a zamanin da, ko gidan ƙawata kwana huɗu ake yi musu su da suka fi mu jimawa ma kenan".
Turaki yay mata mugun kallo kafin ya ce,"to kwana biyun na yanke ba zan ƙara ba, nan gidana ne ba gidan ƙawarki ba ne".
ya danne ɓacin ran da ke ingizo shi, ya ci gaba da yi musu nasiha sosai, irin nasihar da kowaccen su sai da taji a zuciyarta, bayan nan yay musu adu'ar zaman lafiya, kafin nan ya rufe taron na su da adu'a.
cikin ƙarfin hali Fillo ta danne bala'in abin da ke taso mata ta ce,"Allah ya amsa dukkan adu'oin da kayi mana ranka ya daɗe, insha'Allahu ta ɓangarena ba zaka taɓa samun wata matsala ba, zan kiyaye dukkan abin da baka so, haka zan yi ƙoƙarin aikata duk wani abu da kake so domin farin cikinka, na yi maka alƙawarin hakan muddin numfashina".
sai kuma ta kalli Ilham tace,"abokiyar zamana ina yi miki barka da dawowa, ina fatan zamu haɗe kanmu mu zauna lafiya kamar yanda mijinmu ke so, ni dai ta ɓangarena ba ki da damuwa na ɗauke ki tamkar ƴaruwa ta jini. bismillah gaisuwar musulunci".
ta faɗi hakan tana miƙawa Ilham hannu don su gaisa, but sai Ilham ɗin taƙi miƙa mata nata, ta yi mata kallon sama da ƙasa tare da jefa mata wani irin wulaƙantaccen kallo.
ɗan runtse idanun Fillo tayi tare da yin murmushin takaicin da babu wanda zai fahimta, bata san cewa ita ma ba har zuciyarta ba, yanda bata so ta haɗa hannu da ita haka ita ma, don ko ace ma ta amince su gaisa ɗin cikin dabararta zata aiwatar da abin da zai hana hakan, ai ba don Turaki a wajen ba kallo bata isheta ba.
Ilham ta miƙe a zafafe zata fita ta bar parlon Turaki ya dakatar da