NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 292 of 323

masa rai, yanda ta nuna ko kishinsa ba ta yi, irin ma ba sonsa take ba, kawai da ya faɗa mata ta kalle shi da fara'arta tace Allah ya sanya alkhairi, daga nan taci gaba da harkokin gabanta tamkar ba wadda kishiyarta zata dawo ba, shi kuma wannan nuna rashin kishin nasa ya ba shi haushi har ya ɗauki fushi da ita, kuma ganin bata bi ta kan fushin nasa ba ya ƙara hawa sama. ita kam tun da tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, ba komai take tunawa ba sai ranar da ya sameta a ɗaki tana kuka. ba kamar yacca ya tsammaci kukan nata ba, kuka take yi akan ciwon mara da ya matsa mata kwana biyu, amma buɗar bakinsa a lokacin ce mata yay,"ya fi miki ki koyawa zuciyarki haƙuri da son zama da kishiya akan wannan kukan da kike yi mara amfani, domin kuwa dawo da matata babu fashi, Allah ya halasta min na zauna da irinki har guda huɗu, balle kuma matar da na fara zama da ita kafin ke, ki san da wannan". idonsa kawai ta kalla a lokacin ta san ya faɗa mata hakanne saboda kawai ya ƙuntata mata. ita sai a yanzu ta yarda da batun sauyawar da maza suke yi idan zasu ƙara aure, duk da bata ga yana wani rawar ƙafa ba amma ya sauya fiye da tunaninta, magana wannan bata haɗa su acikin gidan, kuma ba nata laifin bane, nasa ne, don ita ko kaɗan bata ma bari kishinta ya fito ƙarara ba yacca zai gane, tun tana ɗora hakan akan tilasta masa ɗin da akayi har ta daina, ta fahimci zallar bura'uba ce kawai irin ta ɗa namiji, don sosai ya tsiri wa su halaye da bata sansa da su ba, ko zata narke tana masa magana baya tanka mata, ban da jiya da yaci zarafinta. "Jannaty..." ta kira sunansa a hankali, taji ta gaza ƙarashe abin da zata faɗa saboda kukan baƙin ciki da ya taso mata. Turaki yay banza da ita kamar bai ji kiran da tayi masa ba, sai dai still bai bar kallonta ta ƙasan ido ba, yana duban kumbararrun idanuwanta, ga wanda bai sani ba zai ce ciwon ido take yi, but to him da yasan kayarsa ya san uban kuka taci ta ƙoshi har ta godewa Allah. sai ya ɗauke kansa ya sauke ajiyar zuciya, kamar ba zai bi ta kanta ba, sai kuma ya ɗan ji tausayinta a ransa, ya maido da dubansa gareta sannan yace,"ke ba kya gajiya da kuka ne, kin shigo min ɗaki kin min tsaye sai wani faman cin magani kike kina faman ɗaga hanci". Ya ida maganar yana yi mata kallon sama da ƙasa. Cikin sanyin murya ta ce masa,"don Allah kayi haƙuri ka bar ni in yi lallen". ya tamke murya ya ce,"na ce ba za'ai ba". "to ya zan yi da Maama fa?, ita fa ta ban umarni akan in je ayi min". yay ɗan jim kafin ya ce,"fita ne daga gidan nan zuwa gidan mu ba za kiyi shi ba, idan me lallan zata zo nan tayi miki ta zo, idan ba zata zo ba ki haƙura". ta haɗiye ƙullun abu a maƙogoronta na takaici, ta sunkuyar da kanta ta ƙara cewa,"don Allah ka bar ni in koma gidan ku in zauna har a gama biki, don Allah don Annabi". ɗago kansa yay ya bita da kallo, duk tayi sanyi sosai kamar mara lafiya. nazartar yanayinta ya shiga yi, so yake ya gano dalilinta na dagewa akan sai ta koma gidan su har an gama biki sannan ta dawo. yaga ta ƙara kawar da kai gefe tana goge hawaye. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,"matsayina na mijinki wanda aljannar ki ke ƙarƙashin ƙafata, ina me ba ki umarnin ko nan da parlo kar ki bari ayau, har sai an kawo abokiyar zamanki tukunna". yay maganar cikin muryar ba da umarni. ta dube shi a sanyaye,"yan zu ba zan iya cin alfarmar Maama ba?". tayi maganar cikin wani irin rauni. yan da bai tanka mata ba haka itama bata ƙata cewa komai ba ta fita. tana fita ya ɗauki waya ya kira Maama yace mata wai sun fita ita da shi sai zuwa yamma za su dawo, a faɗawa me ƙunshin sai gobe ayi. ƙarfe bakwai na dare aka kawo Ilham, sai da aka fara kaita gidan su Turaki sannan aka yo da ita gidanta. lokacin da Fillo ta jiyo guɗa sai da zuciyarta tayi wani mugun matsewa, yunwa take ji a lokacin ta ɗauko abinci zata ci, amma lokaci ɗaya taji ta ƙoshi, bata buƙatar komai a wannan lokacin sama da tayi kuka. ɓangaren Ilham kuwa tana can tana shan mugwayen shawarwari, an cika mata kai fal da abubuwan da muddin ta ɗauke su ba zata jima ba Turaki zai ƙara saita mata hanya. wajen ƙarfe takwas da rabi na dare, Fillo ce a ɗakinta tana shirin kwanciya bacci, wayarta tayi ƙara, waƙar da ke tashi wajen ringing ɗin ya shaida mata Turaki ne, hakan yasa bata ko matsa daga inda take ba balle taje ta ɗauka. har sau biyu kiran na shigowa ya katse bata ɗauka ba, tana gama shiryawa ta haye kan gado ta kwanta, ta dunƙule a waje ɗaya, idanuwanta na ta hasko mata yacca Turaki zai kwana tare da wata yau ba ita ba. tayi nisa cikin wata duniya ta daban Turaki ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya kunna fitila ya bita da kallo, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror da ya hangi wayarta akai, ya ɗauka ya kunna, sai yaga a silent take, hakan ya tabbatar masa da cewa ba da gangan taƙi ɗaga kiran nasa ba. ajiye wayar yayi ya shiga taɓa ƙafarta, tana jinsa amma tayi masa banza, ta rufe idonta kamar me baccin gaske. zama ya
🏠