NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 291 of 323

ngina da kai a lasa, yanzu ba gashi sun mayar da ƴar'su ta zama mutum ba, dama ai ƙwaɗayin dukiyar tasa ake ba wai saboda Allah suka nuna su na sonsa ba, yo ke daga jin labarin ɗauke asiri ai kin san ƙarya ne ma". Mama Asabe ta ce,"to ai ni a wata ruwayar ma ji nayi ance bata da asali, ance uwar na haifarta ta jefar da ita ta gudu, an ce ma bata san uban nata ba sai da zai mutu yazo neman gafarar uwar. to duk dai kin san harkar ta a haɗu a rufawa kai asiri ne shiyasa aka ɓoye gaskiyar zancen, amma dai tabbas an ce shegiya ce". Antyn Kano ta gyara zama tana duban Fillo, ta kama haɓa ta riƙe cikin izgili ta ce,"shegiya kuma?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe abun har haka yayi muni, yanzu tsakani da Allah ina gamin haɗi tsakanin tsarkakke da gurɓatacce, shege ai sai ɗan uwansa shege, gaskiya wallahi an zalunci yaron nan, ko da yake aikin asiri babu abin da ba yayi. to ni su Mai Martaba ma mene na haɗa Ilham kishi da ƴar gaba da fatiha?. kai talaka dai akwai zubarwa da kai mutunci, da zarar an ce an rasa cin na yau da na gobe shikenan sai kiga an faɗa harkar karuwanci kuma. Allah dai ya kyauta yasa kar a haifi iri". tun a zancen farko zuciyar Fillo ta buga da ƙarfin gaske, ranta ya ɓaci sosai. a yanzu da Antyn Kano tayi magana ta ɗago da kanta tana kallon su, lokaci ɗaya idanuwanta suka cika taf da ƙwalla. Mama Asabe ta sake cewa,"um to mu yi dai abin da ya kawo mu". ta kai dubanta ga Fillo ta ce,"ga shi ba sanin sunanki muka yi ba, to ma dai in aka kira ki da shegiya ai ba'ai lefi ba sunan yanka ne irin naku na haihuwar kan titi. allura muka zo ki bamu idan kina da ita za'a cire sartse". a lokacin zazzafar ƙwallar da ke cikin kurmin idanun Fillo su ka gangaro saman kumatunta, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, jin zuciyarta take yi kamar zata yi bindiga. she can't stay any more ana cin mutuncinta da na iyayenta. in ba haka ba za'a iya kaiwa gaɓar da wataƙila zaman aurenta ya ƙare yau a gidan nan. taji yo maganarsu su na ƙara faɗin,"ai Ilham ma tafi ƙarfin kishi da wannan wallahi, ta maishe da shegiya ƴar aiki kawai". cikin raɗaɗin zuciya Fillo ta miƙe zata bar wajen. Hajiya Zaliha ta dakatar da ita da faɗin,"ke figaggiyar kaza dama ba ki da tarbiyya, ina allurar da muka ce ki ba mu?, saboda kin mayar mu ƴan iska za ka kaɗa kai ki wuce ba ki ko tanka mana ba". Fillo ta runtse idanuwanta, ji take yi kamar ta tanka musu, kamar ta faɗa musu maganar da har mutuwa ba za su manta da ita ba, ta ci musu mutunci irin wanda ba za su ƙara sha'awar zuwa gidan nan ba har a tashi duniya, duk kuwa da cewar sun ajiye ƴa acikinsa. but ɗayan ɓarin zuciyarta sai ya haneta hakan, ba halinta ba ne, ba tarbiyar da aka bata ba kenan, tayi banza da su da maganar da suke yi ta haye sama tana goge hawaye. ba ta shiga ɗakinta ba sai da ta daidaita nutsuwarta tukunna, gudun kar Maijidda ta fahimci abin da ya faru. ko da ta shiga ba ta kalli in da Maijidda ke zaune ba tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, tana fitowa sai ga Hannatu ta shigo ɗakin, ta durƙusa tana faɗin,"Anty baƙi a ƙasa sun ce ki ba su allura". ta dafa kafaɗar Hannatu suka fita, su na tsaye ta wuce kitchen ta fito, ta tsaya tare da musu kallon banza kafin ta buɗi ba ki ta ce,"ban da zubar da mutunci ina ku ina aron abu?, anyway matar so bata da kayan faci a ɓangarenta balle tayi ajiyar wata allura". tana faɗar hakan ta haye sama abin ta, fiye da haka ta so ta faɗa musu, to gudun tashin hankali yasa ta rabu da su kawai. ko da ta koma ɗaki bata bari Maijidda ta fahimci komai ba, ta zauna suka cigaba da hira. "kin san Allah da tafiyata zan yi. ni kin san ba son ƴan aikin nan nake ba balle in zauna muyi hira da su. yanzu dai ina zamu je ƙunshin?". "to ai ma Maama tace wadda ta yiwa su Adda Zaytuna ita ce zata yi min, yanzu wurin saloon kawai zan je, mu bari sai da yamma ma je ko?". Maijidda tace,"a'a kin san halin lalle da cin lokaci, mu fara zuwa saloon ɗin tukunna". "to shikenan. bari naje na faɗa masa. kin san nace miki ina son zuwa gidan Yaya Yusuf, shi ne fa yau na buga musu sammako". ta yaye mayafin jikinta ta ajiye sannan ta fito ta nufi ɗakin Turaki, yana zaune kan kujera yana operating laptop, hannunsa riƙe da ƙaramin glass cup yana kurɓan coffee. yaji shigowartata amma bai ko ɗago ya kalli wurin da take ba, sai dai yayi mamakin ganinta ɗin, dan rabonta da ɗakinsa tun ranar da ya faɗa mata cewar zai dawo da Ilham, yau kusan kwana tara kenan. ko abinci idan ta gama a parlo take barinsa, ta ci nata ta bar masa nasa, ruwansa ne yaci ruwansa ne kar ya ci, yacca ya lura ma kamar girkin ma ba yi take ba sai dai ƴan aiki su yi, shiyasa shi ma baya shigowa sai yaci abinci a gidan su ko gidan su Bello. a ciki ya amsa sallamar da yaji tayi, ta ƙasan idonsa yake kallonta, tana tsaye daga jikin madubi ta maƙale, fuska sam babu annuri. yacca take fushi da shi haka shi ma yake fushi da ita, ranar da ya faɗa mata zai mayar da aure ta ƙona
🏠