NOVEL SHARES -
a biyu ne zuwa uku naki, sanin darajar kai da sanin yadda za ki sarrafa ragamar miji, ki zama kece limamiyar ba wannan limamiyar da ke jan ragamar limancin layu biyu ba. Kissa da kisisina kamar ki lashi takashinsa amma shi ma ina jan kunnenki, mutunciki kar ki sake kiyi wasarairai da shi, domin shi ne limamin rayuwa".
Fillo tasa tissue ta goge hawayenta, kuka ya kubce mata ta ce,"ni kaina na san sai nayi haƙuri yanzu Anty, Turaki ya sauya min fiye da tunani. wallahi Anty da yazo min da batun zai mayar da auren nan sam ban nuna masa ina ƙin dawowarta ba balle kuma na ɗaga masa hankali. amma jiya kafin su tafi ɗaurin aure kar ki ga yan da ya taso min da faɗa, har da zagi fa Anty, kuma wallahi ba wani abu nayi masa ba, cewa kawai nayi zan koma can gidansu sai an gama biki na dawo, wai buɗar bakinsa ce yay tunda ina baƙin ciki da zuwan wata ai dole nace zan bar gida, to babu in da zanje in zauna in kula da ƴan uwanta da suke zaryar shiga da fitar yi mata jere, idan suka buƙaci wani abu wa nake nufin zai ba su, ko shi zai baro wajen aikinsa ne ya kawo musu. to kar inyi kuskuren wulaƙanta masa Mata, don ƴar'uwarsa ce, kuma samun zaman lafiya tsakanina da shi na mutunta ƴan'uwansa, Anty kamar fa zai duke ni, duk yadda na so da kar a fahimci ina cikin damuwa sai da Maama ta fahimta, da na dawo da daddare sai ce min yayi wai naje na kai ƙararsa ina so in shiga tsakaninsa da iyayensa, to wallahi zai yi min abin da ban taɓa zato ba, zamana da shi babu dole..."
kuka ya ƙara kubcewa Fillo sosai,"kuma wallahi tallahi Anty ban kai ƙararsa ba, na san dai nayi iyaka ƙoƙarin da za'a fahimci bana cikin damuwa amma na gaza, shi ne har Maama ta gane ta tsare ni da tambayoyi, kuma ita ma ban ce mata ga dalili ba haka nace mata bana jin daɗi ne, kuma da ta san da ma ban da lafiya bata ƙara tayar da zance ba, amma shi ne har yake ikirarin wai sai ya rabu da ni in har na nuna bana son ƴar'uwarsa ko kuma na ƙara kai ƙararsa wurin Maama. tsakani da Allah Anty ko anan idan tazo ya nuna mata ta fini matsayi ba sai yaja min wulaƙanci daga wurinta ba, yanzu nan ƙunshi nace za'a yi min sai ce yay ba da yawunsa ba".
Nuratu taji tausayinta sosai, ta dinƙa bata haƙuri da lallashinta, tare da yi mata nasihohi da kuma wasu shawarwarin da zata ji daɗinsu muddin tayi amfani da su.
kafin nan suka yi sallama taja motarta.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*58*
dawowar Fillo gida ta tarar ana ta kai komo wajen shiga da kayayyaki ɓangaren Ilham, tun jiya ake wannan zaryar, ƴan'uwan mahaifiyarta ne kusan duk ɗin su, sai Boɗejo da Inna Falmata.
sai dai bata san ba ko yau har da su tunda dai bikin ba ɗaya ba ne, duk da dai taga Boɗejo na nuna kamar bata da hurumi da auren su Zaytuna da Khaleel da Samha, kamar su ma ba jikokinta ba ne.
ɗauke kai tayi daga barin kallon part ɗin Ilham ɗin, tayi wucewarta part ɗinta bayan ta tambayi Baba me gadi ko an kawo masa abinci, da shigarta kuma ta rufe su Sakina da faɗa akan rashin kaiwa Baba abinci da suke yi da wuri.
ta kalli Maijidda da ke zaune a parlon ta haɗe rai, ta ce da ita,"yi haƙuri don Allah, sammako nayi gidan Yaya Yusuf, za su je taraba ne na bayar da saƙo akaiwa Ummi".
Maijidda tace,"ba dai bikin Raudha ba".
"shi ne ya taho wallah, next week in Allah ya kaimu".
"kin ga da an kammala na su Adda Zaytun sai ki bi su ku tafi tare kawai".
Fillo tayi murmushi me ciwo ta ce,"ni ma haka nace. ki hau sama ki jira ni bari na ajiye waɗannan kayan".
ta faɗa tana wucewa kitchen, friedge ta buɗe ta zuba fruites ɗin da ta siyo, kusan kwana uku da ƙarewar na su amma Turaki bai kawo wani ba.
fitowarta daga kitchen ɗin ta tarar da baƙi a parlon, fuskar farko da ta kalla ta shaida ƴan'uwan Ilham ne, don su na kama sosai da Fulani Azima.
ta ƙarasa wajen su ta durƙusa har ƙasa, cikin ladabi ta shiga gaishe su, kuma ba tare da ta miƙe ta koma kan kujerar ba tayi zamanta akan carpet ɗin don bata tunanin zata iya zama kan kujera alhalin su na kai, hakan kamar da rashin ɗa'a.
su uku ne manyan matan, kowacce sai da ta gama yi mata kallo a yatsine sannan suka haɗa baki wajen amsa gaisuwartata.
Antyn Kano ta dubi Fillo da kyau kafin ta mayar da dubanta ga Mama Asabe ta ce,"wannan ce kishiyar Ilham ɗin?".
Mama Asabe tace,"ina jin ita ce ko?".
sai kuma kusan a tare suka jefawa Fillo tambayar,"kece matar nan ɓangaren ko kuma ƴar aiki ce?".
kafin Fillo tayi magana Hajiya Zaliha ta amshe da cewa,"ita ce mana".
"yanzu wannan ita ce wacce aka liƙawa Turakin da ma?, ai ce nake yi waccan da aka ce an ba shi a bushe take ko".
Mama Asabe tayi maganar.
Hajiya Zaliha ta taɓe baki ta ce,"yo ai dama saboda su taimakawa ƴar'su ta zama mutum kuma su ci arziƙi, shiyasa suka bi ta ƙarƙashin ƙasa suka kori Ilham aka liƙa masa ita, amma banda haka Turaki ai yafi ƙarfin tsummar ƴar aiki, ko da yake banga laifin iyayenta ba dan sun yi ƙoƙarin haɗa iri da mai dukiya kamar Turaki ba. hausawa suka ce bangon sukari a ji