NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 323

wanzuwar sabon yanayi, babu shakka yarinyar zata zamar mata jigon wani abu, ta san da wannan. ta kawar da mamakin ganinta a gefe guda, Kafin ta buɗi baki tayi magana Fillo ta rigata. "Kaka Rabi ce ta turo ni na ƙarasa aiki, bata jin daɗin ne yasa ta tafi". Tayi maganar idanuwanta na kan tafin hannun Hajiya Madina dake tallafe da haɓarta. Hajiya Madina ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace,"masha'Allahu sannunki, ya sunanki?". "sunana Halima". "sannu Halima, Allah miki albarka...ke jikar Kaka Rabin ce?". Ta ɗaga kanta,"ehh jikarta ce, a wurinta nake da zama". "to sannunki kinji, amma jikin nata ba tsanani yayi can ba ko?". Ruwa ya kawo idon Fillo sanda tace,"ehh na dai baro ta zata yi bacci, tace kanta ke ciwo". Hajiya Madina tace,"to Allah ya bata lafiya...kin ƙarasa aikin?". ta girgiza kanta alamar a'a. "ai yanzu na shigo kuma ban san aikin da zanyi ba". Hajiya Madina ta sauke hannunta daga haɓarta, bata san me yasa zuciyarta ke wani irin zillo ba. ta kalla kujerar da Turaki ke zaune, bai ci komai ba ta sani, kuma ba zai ci girkin kowa ba idan ba nata ba, ƙannensa ma sai an kai ruwa rana yake iya cin abincinsu balle na wata ƴar aiki, ita kuma tana so ta fita cikin gaggawa, suna da meeting na friends ɗinsu da suka saba duk ƙarshen wata. "mu shiga kitchen ɗin". ta faɗawa Fillo. Tayi gaba ita kuma ta bita a baya. tai mata nuni da wata drower tace,"buɗe ciki ki bani ƙwai guda 10". cikin sauri Fillo ta ɗauko ta kawo mata, ita kuma ta ɓare ledar indomie super pack guda biyu ta jefa acikin ruwan zafi, sannan tasa Fillo ta yanka albasa ta kuma yi greating taruhu. In few minutes Hajiya Madina ta gama soya indomie da ƙwai ta zuba a plate, sannan ta dafa tea daya ji kayan haɗin Sahaz Special Spices, lokaci ɗaya kitchen ɗin ya kaure da ƙamshin spices ɗin, Fillo sai shaƙe ƙamshin ta ke. Ita dai Fillo na tsaye a gefe tana kallon duk abinda ta ke yi, da kuma bin umarnin duk abinda ta sakata, tana kuma yiwa mata bayanin abubuwan da zata yi, ba wani aiki ne me wuya ba, Kula da buƙatun Turaki ne kawai. "miƙo min wancan tray ɗin na tsakiyan". Hajiya Madina ta faɗa tana ma Fillo nuni da inda zata ɗauko tray ɗin. ta jere kayan break fast ɗin akai ta bawa Fillo tace ta wuce da shi kan dining. "Hajiya ina ne dining ɗin?". Allah ya taimaketa bata da ƙauyancin faɗin abu, Hajiya Madina tai murmushi bata ce da ita komai ba. Sai da ta gama wanke hannunta a sink tukunna tace da ita,"muje na nuna miki...in kin kai akwai ɗaki idan kika fita ƙofar kitchen daga baya, sai ki zauna in yana buƙatar wani abu zaki ga kira ya shigo ta wayar ɗakin, landline ce, ɗagawa kawai zaki yi ba sai kin danna wani wuri ba...please karki yi delay wajen amsa kiransa, becouse bai da lafiya isashshe". Fillo ta biyota a baya suka fito, tayi mata nuni da dining area ta wuce taje ta aje akai. "if ya gama sai ki kwashe kayan ki wanke...karki ce za ki ɗora abinci, baya cin abincin kowa sai nawa". tana faɗa mata hakan tace taje tace masa his breakfast is ready. da faɗin hakan ta haura upastairs cikin sauri. Fillo dai bata gane guntun turancin da Hajiya Madina tayi mata ba, tai shiru tana nazari da son gano abinda tace ɗin amma ta kasa. Ta ɗaga kai ta kalli inda Turaki ke zaune kan kujera ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ranta tana mamakin isa da jin kai irin nasa, wato bama iyaka masu aiki yake walaƙantawa ba harda matarsa. komai da take rayawa cikin ranta ya katse lokacin da Zaytuna ta shigo parlon, ƙananun kaya ne ajikinta sunyi mata kyau sose, kamar balarabiya ta watso gashinta ta baya, ta saka head band akan gashin. Wurin Turaki ta wuce tana smiling ɗin dake fiddo da asalin kyan fuskarta, ta zauna kusa da shi kamar zata shige jikinsa, ta kamo hannunsa guda ɗaya sukai shaking. "Hamma nah yau ka tashi da wuri haka". yasa yatsa ya lakuce mata hanci,"aka ce miki irinki ne ni, bacci babu sauƙi". Dariya tayi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa tace,"Hamma nah na fa rage, tunda ka dawo ai baka kalla na kai 10am ban tashi ba ko". Idonsa na manne kan news ɗin da ake a aljazeer ya ɗaga mata kai kawai. Conversation ɗin nasu shi ya warwarewa Fillo komai, kenan wannan shine Hammansu da Hajiya Madina ke ta faɗa mata ɗazu, ba me gidan ba kamar yanda ta zata. Kenan shine mara lafiyan da Kaka ke bata labari?, ta ƙara kallonsa da kyau tana jinjina wani lamari dake cikin kanta. tana jin Zaytuna na tambayarsa,"Maama bata sakko ba?". "yes". Ya amsa mata before ya kalleta yace,"wa akai ma kwalliyan?". Ya tambaya da salon tsokana. Ta maƙale hannunsa tana cewa,"kai Hammah nah ni kam wa zanma kwalliya banda kai". leɓensa na talewa da murmushi yace,"ummm to kinyi kyau sosai...kinyi break fast?". Ta gyaɗa masa kai,"tare zamu yi da kai". Ya hurar da iska daga bakinsa,"to ai Maama bata sakko ba har yanzu, ni kuma bana so ki zauna da yunwa. ko muje kitchen ɗin mu dafa tare kinga mun hutar da ita?". ta ɗaga masa kai alamar ehhh, hannunsa na riƙe da na
🏠