NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 289 of 323

. Nuratu tayi guntun murmushi me sauti. "me zai sa ta raina ki?, a wanne dalili Fillo?, wurinki fa daban wurinta daban, ko za ku shekara dubu a gidan nan sai kun so za ku haɗu da juna. kinga look, ni fa ko a yanda na ɗauka ma sai ka yi abin da za'a rainaka ɗin tukunna ake samun damar rainaka, as far as kin kiyaye waɗan nan abubuwan wallah ko da me kishiya ke ji bata isa ta raina ki ba. na farko karki kuskuren saka mata Ido a lamarinta, kar ki ke kai ƙaranta, saurin faɗa da ita shi ne babban abin da ke janyo raini, da kuma ɗaukar zuga, in har kishiya ta fuskanci kina ɗaukar zugar mutane to billahi ta gama rainaki, haka zalika kar ki yi gigin dinga shiga kowanne lamarinta ko da ita da kanta ke cusa ki aciki, baya baya dai...". Fillo ta tari numfashinta,"Anty Nuratu to ni ina ma nake da lokacin waɗannan abubuwan akanta. ina miki batu ne na tana ganin ita ƴar sarki ce, ta fini ilimi, ta kuma fini wayewa, kuma tana da aikin yi, sannan zata dinƙa min kallon cewar ni ba kowa bace face ƴar aikin da aka tausayawa aka auro, Anty Nuratu dole ta raina ni". "to ai ƴar aikin ta fita tun da har tausayin ma yasa aka iya auro ki, ita da ba'aji tausayin nata an aurota ɗin ba fa sai cusata da aka yi?, mtsww kin ga don Allah ni kar ki bayar da ni, ko wayewar ma ai bata fiki ba, wayewar shiga jami'a kawai ta fiki, amma ban da ta gidan miji, ko kin manta tsawon watanni da kika shafe a ƙasashe da dama kina durzar amarci ke da mijinki, ita ta sami wannan damar ne?, bata samu ba kuma ba zata samu ba". sai kuma ta miƙa mata ledar da ta gama zuba kaya aciki,"ga waɗan nan ɗin, ai duk nayi miki bayanin yanda za kiyi amfani da su". "to na gode sosai, Anty Nuratu sai garin kunun, don Allah a ƙara yi min, naji daɗinsa sosai wallahi, sometimes idan na kalli kaina sai inga kamar ba ni ba, ji fa kumatun da na tara". ta faɗa tana ƴar dariya me kama da ta ƙarfin hali. "wai ke zatonki kunu ne kaɗai ya saka ki wannan ƙibar, to har da Babyn mu". "hmm ni fa banda wani ciki. haka jiya Ammi ma da naje sai adu'a take wai Allah ya raba lafiya, ni dai nayi murmushi kawai. kafin mu taho test nawa aka yi duk ba ciki ba ne, ni kam ma ba yanzu zan haihu ba sai kamar nan da 2years lokacin na ƙara girma". "yanda za'aji daɗin cewa ke juya ce kenan, ki ma daina wannan kuskuren tunanin, yanda kike da kishiyar nan in har ta rigaki haihuwa sai kin fuskanci ƙalubale, gwarama ki roƙi Allah ya ba ki, in ya so kya huta daga baya". har bakin mota Nuratu ta rakata, ita kuma sai godiya take yi mata. "ki daure dai ta bakin Abban Farha ki ƙara zuwa asibiti su duba, don bani da tantama kin ɗauki ciki". Fillo tayi murmushi me ciwo,"idan cikin ne zai bayyana kansa Anty Nuratu. kin san fa nace masa muje asibitin wallahi ko tanka min bai yi ba, da na ƙara magana ma ce yay bai shirya tara ƴaƴa yanzu ba". tausayinta ya kama Nuratu, ta kawar da zancen dan ta lura kamar akwai damuwar da take ciki, kamar dai yanzu tana zaman haƙuri ne da Turaki kawai. "kin ji bikin Raudha an mayar da shi Adamawa ko?". "haka Ummi ta faɗa min jiya da muka yi waya". "ni ban so hakan ba wallahi, kawai dan ba yanda aka iya da Maudo ne. yaushe za ki tafi to?". Fillo tayi murmushi me ciwo tace,"ai babu ni a batun zuwa kam dan yace ba zanje ba, kuma wallahi ba zan ƙara yi masa maganar ba, na lura tun da zai mayar da auren nan ya ɗauko wata bura'uba ya ɗorawa kansa, kuma sai dai komai ya ƙare akansa shi ɗaya ni ba saurarsa zan yi ba, ban iya haɗa hanya da damuwa". Nuratu tace,"Allah dai ya kyauta, yanzu kam sai kin ta haƙuri, yan da za ki sami mijinki a ke ta ɗaya ba haka za ki same shi ba a ku biyu ba. shawarata kiyi ta adu'a Allah ya kauda fitina tsakanin duk ku ukun, abin da bai da kyau Allah ya mayar maku da shi me kyau. sannan don Allah ba ruwanki da wata fitina, imma daga ɓangarenki ko nata, ki kama mutuncinki ki riƙe, kar ki sake wani hargagi ko cin mutuncin ko fashe fashe da duk danginsu a same su daga gareki, wannan duk kishin marasa ilimi ne. kuma jiya na faɗa miki yau zan ƙara maimaita miki, babu ruwanki da shisshigewa ko tusa kai a wurinta wai ko dan ku zauna lafiya a'a sam, idan har taga kin ja ajinki da mutuncinki za ki ga tana jin shakkarki, idan ma tana tare da tsiya ne to zata sha jinin jikinta. sai kuma shawarar da zan ƙara ba ki, kafin ya amince kici gaba da karatu to ki fara business, kin san ance darajarka jakarka ko aljihunka, to ki kama kasuwanci kamu me kyau, ta yanda hankalinki zai karkata ɗungurungum akansa, ta yanda za ki zama baki da lissafin wata kishiya da takaicin miji sai na kuɗinki, wallah kasuwanci wani babban abu ne na siyawa kai mutunci wasu matan ne kawai basa ganewa, kuma kar ki yarda ki kama kasuwanci da kuɗinsa, ki kira Dada ki faɗa mata kina buƙatar kuɗi ko kuma kice a buɗe miki shago. Sannan ko da wasa kar ki sake mijinku ya fara samun tashin hankali ta ɓangaren ki, in ba haka duk san da wani laifi ya afku ko da ba ke bace zai ce ai kece uwar rigima, abu gud
🏠