NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 288 of 323

r na da haƙuri yasa bata nuna ba, sai ka ɗauka ma ko bata san ciwon kanta ba shiyasa take ta hidimarta ko a gefen yatsarta. fatan ta ɗaya Allah yasa ba Boɗejo ba ce taje ta kunna musu wuta a gida. ko kuma halin jiya ya maimaita musu, don ance jiya ma kafin ɗaurin aure kusan rufe Fillo da duka yayi. **** "yauwa bayan kin auna fulawanki sai ki zuba butter, ki kwaɓa yeast ɗin da ruwan ɗumi kuma da shi za ki kwaɓin gaba ɗaya. yauwa to miƙo min gishirin can, if you like you can add sugar". bayanin da Nuratu ke yiwa Fillo kenan a kitchen ɗinta, a yayin da take koya mata yanda ake alkubus, tun san da suka dawo suka zo gidan taci taji daɗinsa tace zata koyi irin nata. Fillo ta ɗauko roban sugar da gishirin kamar yanda Nuratun tace, ta ajiye tana ci gaba da kallon yanda take yin kwaɓin da kuma sauraron bayanin da take yi mata. wucewar wasu mintuna Nuratu ta kalli Fillo jin tayi shiru, ta girgiza kanta kawai tare da jin tausayinta, kafin tace mata,"kin san mene?, wallahi tallahi cutar kanki za kiyi muddin za ki ɗauki damuwa kisa a ranki har haka, ke wa ya faɗa miki yanzu ana nuna damuwa da kishiya?, kina ƴar ƙaramarki haka?, amma...". ranta a ɓace ta ɗauki tukunyar da ta rufe ta bar kitchen ɗin. Fillo ta bi bayanta da kallo kafin ita ma ta bar kitchen ɗin, parlo ta wuce ta zauna, ta ɗauko Farha da ke cikin keken wasanta, tana cikin yi mata wasa Yusuf ya shigo, bayan sun gaisa ya ke ce mata. "jiya sai nake jin zancen an mayar da auren abokiyar zaman ki". wata ƙwallar ciwo ta tararwa Fillo a ido kafin tace,"ehh Yaya". "to Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta haƙuri kin ji ko". "insha'Allahu Yaya, na gode". sai ya ƙara cewa,"amma ba ki da wata matsala ko?". "babu Yaya". "to masha'Allahu, kar fa kice za ki sakawa ranki damuwa kinji ko, kinga ba isassar lafiya gare ki ba. ya zancen karatun ki kuma?". tasa hannu ta goge hawayen da yay nasarar gangaro ma ta kafin tace,"lokacin da muna Ausburg har ya nema min addimission acan, to kuma da muka dawo sai yake cewa wai na haƙura kawai, to ban san me dai yake nufi ba, gaba ɗaya zan haƙura da karatun ko kuma wancan admission ɗin zan haƙura da shi". Yusuf ya sauke numfashi yay ɗan jim kafin yace,"ki ba shi lokaci tukunna, zuwa gaba sai kiji koma menene dai, amma karatun naki yana da muhimmanci sosai". ya miƙe daga kan kujerar da yake zai wuce ɗaki Farha tasa kuka, ya dawo ya karɓeta ya tafi da ita. wayar Fillo dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗauka ta kara a kunne tare da amsa sallamar Maijidda. "ke na zo kuma na tarar ba kya nan". "ehh wallahi naje gidan Yaya Yusuf ne". "lallai ma ke ɗin nan, kuma kika ce na zo na raka ki ƙunshi, kin san za ki fita za kisa na zo, ko don kawai dai kin raina min hankali, wannan ai rashin mutunci ne". "Allah ya ba ki haƙuri maida wuƙar, ba jimawa zan yi ba yanzu ma fa nake shirin tahowa. sanin halin ɓata lokacinki yasa nace bari kawai in je in dawo, don Allah ki zauna yanzu gani nan a hanya". "sai kin dawo, idan da mota kika fita ki yiwa Allah ki samo min mangoro a hanya". "to uwar biyu". Maijidda tayi dariya sosai tare da cewa,"rufa min asiri maza su kaini ba mata ba, uban wa na aura da har zan zama uwar biyu, ke ɗin dai". su kai Sallama Fillo na miƙewa ta nufi ɗakin Nuratu, samunta tayi tana haɗa wasu magunguna a leda da dukkan alama maganin mata ne. Fillo ta zauna bakin gadon tana cewa,"Anty tafiya fa zan yi...". kuma bata ƙarasa ba ƙarar wayarta ya katseta, ganin sunan Maama yasa tayi saurin ɗagawa. daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"Daughter lafiya ba ki shigo ba?". "Maama naje gidan Yaya Yusuf ne". "zuwa yaushe za ki dawo?, ko acan za'a yi miki ƙunshin?". "a'a wallahi Maama, wadda muka yi zata zo ɗin da safe ta kirani an yi musu rasuwa, wai da zata turo sister ɗinta but tana faɗa min bata ƙwarai sosai kamarta ba, shi ne nace ta bar shi kawai". "ok to ki taho yanzu, nasa a kira wacca ta yiwa amare tazo tayi miki, bana so ki ƙara zama haka babu lallai, da ɗaurin aure an ga ba kiyi ba mutane sai su fara zaton ko baƙin cikin damuwar kishiyarki yasa". "to Maama yanzu zan taho". "to shikenan sai kin dawo, yauwa kar ki manta ki taho min da ajiyar nan da na ba ki, ga dai Nihal nan zata ja da duk alamu ɗinkinki na gobe ma babu". Fillo tayi ƴar dariya. Maama ta ƙara cewa,"ga baƙi nan an ƙara yi, su na ta tambayar uwar gidan Turaki, idan kin zo duk zan miki bayaninsu, ƴan uwana ne na Kano, babu wanda ya taɓa zuwar min sai yanzu da bikin ƴaƴansu ya tashi". bayan sun yi sallama Nuratu tace,"to ke ko anan ma ba sai ki godewa Allah ba, iyayen miji na sonki miji na sonki, danginsa su na sonki to kuma dan me na damuwar don ya mayar da matarsa?, auren nan fa biyayya ce kawai zai yi ba wai don baya sonki ba, ko a haka matsayinki da nata ai ba ɗaya ba, matar so kike, ita kuma matar shige". "Anty Nuratu wallahi ni abin da nake tsoro raini da wulaƙanci". ta faɗa cikin rauni da muryan ban tausayi
🏠