gado ta ce,"jiya na ƙara kai ɗinki na set uku, su zan saka ranar da za'a kai amare, balance ɗin dai har na ku yace 35k za'a bayar".
"idan kuma babu naki fa?".
"20k".
ta zauna bakin gadon ta ɗauko jakarta, ta ƙirgo kuɗi 20k ta miƙawa Nihal ta ce,"ga namu ɗin, naki kuma bari nayi miki kwatancen ɓangaren Baffa ko kuma na ba ki lambarsa kawai, sa 08065....".
kowa a ɗakin yasa dariya hatta Zaytun da ke kuka tun ɗazu, Nihal ta fara shagwaɓa tana zama kusa da Hajiya Madina ta shiga yi mata kirari da kalallameta.
Umman Nadiya ta ce,"gaskiya ya kamata dai a bawa Auta kuɗi ta karɓo nata ɗinkin ita ma, ba wani sai taje gun Baffa".
Hajiya Madina ta ce,"wannan ƴar fa da kike gani tun da biki ya taho ta fara fashin kuɗi, daga shekaranjiya zuwa jiya kawai tayi min fashin kuɗi sun kai kusan 100k. tsabar rashin sanin darajar kuɗi jiya makeup ɗin 20k akayi mata, ɗaurin aure kawai ba wani event ba. her Excellency kuwa ce tayi sai jiya ta ankare da ATM ɗinta, ta manta shaf ta bawa Nihal tun ranar da aka je jeran kayan ɗakin Samha, ƙarshe dai ta talauta ta babu ko sisi a account ɗin nata, to ni dai na bata shawara nace ta makata a kotun alƙali Dikko kawai, ina dalili yarinya duk ta bi ta yashe mu".
"Allah Maama kina da kuɗi, to ki ban 5k sai Mum ta cika min 10k ɗin".
"yo Nihal ko da Kakar ki Boɗejo uwar masifa kike tafe ai biyar ba zan ba ki ba, don haka ki tashi ki kama gabanki kawai, kije can wajen Uwaki ta ba ki".
Zaytuna ta ce,"ke yarinyar nan wai me kike yi da kuɗi?, Maama ɗa zu ma fa tasa Hammah Bello ya turo ma ta 20k, ina jinta kuma again tana bin Khaleel tana yi masa ƴar murya".
Nihal ta tura baki gaba ta ce,"daga yau ba zan ƙara tambayar mijinki kuɗi ba balle ki zo kina min tonon silili, kina terere da ni mijinki ya ban dubu ashirin. shi ma Hammah Khaleel ɗin da ya ban sai da ya faɗawa duniya ya bani, shiyasa zan mayar masa da kayansa, to wai ma idan baku bani ba waye zai ban? Hammah ne kaɗai a gidan nan zaka tambayrsa kuɗi ya baka kai tsaye babu ƙurewar tambayoyi".
Hajiya Madina tace,"ba kya tambayar na hankali ne shiyasa, tambayar ƴan fashi kike yi, ban san ba kuma ko jari za ki kafa da kuɗaɗen mu".
"Maama to ki ban don Allah, haba Maaman Hamman'mu, Maama me haƙorin maka guda biyu, Maama ƙawar Boɗejo, Maama ta hannun dama na".
Hajiya Madina tayi dariya ta make hannunta dake kan haɓarta,"zan ci gidanku Nihal, naga alama kin mayar da ni Kakarki".
sai kuma ta ɗauko kuɗi a jaka ta bata ta ce,"ga 5k nan daga haka ba zan ƙara ko ficika ba".
Nihal ta rungumeta tana yi mata kiss,"Allah ya bar min ke uwar marayu har ma da masu uba, i love you so much. Allah yaja mana da ranki".
lokacin Samha ta shigo ɗakin, bayanta wasu yara ne su uku ke biye da ita, Hajiya Madina ta bita da kallo, cikin sigar tsokana ta ce,"don Allah Umman Nadiya kin taɓa ganin amarya mara kunya irin wannan?".
ta nuna Samha da ta wuce wadrobe ta buɗe tana ɗebo kaya.
"ina irin ƴar ƙwallar nan da ake yi ta ranar ɗaurin aure, to in faɗa miki yarinyar nan dai bata yi ba, jiya Zaytuna na kuka ita tana wage haƙora talatin da biyu a waje, duk sai ta bani kunya...".
Samha ta katse maganar Hajiya Madina da cewa,"kai Maama, ni yaushe akayi hakan, Allah ma nafi Adda kuka".
"yo camera ai ba zata yi ƙarya ba, za'a kawo bidiyo ko bayan raina Umman Nadiya za kice na faɗa".
Samha tayi murmushi ta ce,"Maama ina tawa atamfar?".
"ki ka bani ajiya?".
"Maama daga wurin Mum ɗin fa nake tace Adda ta taho da kayan nan".
Zaytuna ta ce,"nawa kawai na ɗauko na bar miki naki acan, kiyi sauri kije ki duba in ba haka ba a ɗauke, kin san ɗakin Mum wasarairai take da shi, na nemi sarƙata sama ko ƙasa na rasa".
cikin sauri Samha ta fita bayan ta ce da yaran su biyota da kayan da ta ba su.
Nihal ta matsar da bakinta kusa da kunnen Hajiya Madina tace,"Maama gulma zan miki, kin san me Hammah yaywa Fillo kuwa?".
Hajiya Madina tayi saurin mayar da hankalinta gareta. sai kuma Nihal ɗin ta tashi da sauri tana cewa,"kai ba ruwana, ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba".
ta faɗa tana saurin ficewa ta bar ɗakin.
Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, kafin ta mayar da hankalinta kan maganar da Mama Bilki ke yi mata.
"Zaytuna za'a fara kaiwa kenan?".
"ehh ita za'a kai gobe, jibi akai Samha sai gata mu karɓo amaryar Khaleel, ita anan zata zauna tare da mu, wancan matar ta me Babban sunan kuma yau za su kawota".
Tana faɗa ta miƙe ta fita ta bar ɗakin, don hankalinta bai kwanta ba da maganar da Nihal ta fara yi mata, duk yanda akayi an sami wani misunderstanding tsakanin Turakin da Fillo, dan ta lura tun jiya da aka mayar da aurensa ya zama wani kalar masifaffe, da asuba ma tana jin Khaleel na complain ɗin faɗan da ya kama yi musu na babu gaira babu dalili, to tsoronta kar ya sauke fushinsa akan baiwar Allah, ita da ba ita tasa aka mayar da auren ba, wacca ita ta ma fi shi takaicin mayar da auren, don ta lura da hakan a tare da Fillo, kawai don dai yarinya