o shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?".
"ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can".
"to shikenan".
Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne.
"sannunku fa". ta faɗa a sanda take zama akan ɗaya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya.
"yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige ɗaka ki barmu zazzaune anan".
murmushi ya ƙwace a fuskar Hajiya Ramla tace,"haƙuri zaku yi, ƴar taku ce ta sakani gaba tana kuka".
ta faɗa a lokacin da take bawa wata tsohuwa umarnin inda zata ajiye kulolin soyayyan naman da ta shigo da su.
sannan ta ƙwalla kiran Ɗausiyya da sabuwar ƴar aikin da suka yi bayan auran Fillo, me su na Maraƙisiyya, cikin sauri sai ga su sun zo sun durƙusa a gabanta.
"ku ɗauko farantai ku fara rabon naman nan, kowanne plate ku zuba yanka goma sha biyar".
sai kuma ta kalli tsohuwar tace,"Yaya kun kai ɓangaren Madina kuwa?".
"ehh Hajiya yanzu Yami ta tafi kaiwa".
"to masha'Allah, sannunku da aiki".
sannan ta ƙara cewa da ita,"Yaya don Allah ce da Madina ta bayar da maƙullin store, sai a samu waɗanda za su ɗebo lemuka aciki, a ɗebo katan arba'in, akai katan sha biyar gidan Babana, sai a bar sauran anan".
cikin sauri tsohuwar ta miƙe ta fita, sai da ta fara zuwa ta duba wajen aikin suyar ta su sannan ta wuce ɓangaren Hajiya Madina.
nan ɓangaren ma cike yake da mutane waɗanda mafi yawansu ƴan'uwa ne, duk sai ka kalla fuskokin su zaka shaida ashe Hajiya Madina ƴar dangi ce, saboda kusan duk kamannin su ɗaya.
"Hajiya tana sama ne?". tsohuwar ta tambaya a sanda ta shiga parlon.
"kamar dai ta shiga kitchen". wata acikin mutanen dake zaune akan kujera ta faɗa.
"ta fito ta koma sama fa, yanzu suka wuce ita da Zaytuna".
Tsohuwar ta miƙe cikin hanzari ta hau upstairs, ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Madina domin jiran iso bayan tayi sallama.
a sanda babu wanda ma ya jita saboda akwai ƴar hayaniya acikin ɗakin.
Hajiya Madina na tsaye a gaban madubi tana ɗaura sarƙa a wuyanta, a lokaci ɗaya kuma tana bayani ga Maga.
"kinga ba wani nama da za'a kai gidan Hakimi, shi ya siyo mana, ko a gidansa ake taron, mu da aurar da ƴaƴa shi da karɓe nama. wani lokacin ma dai Baffa ya fiya neman suna, ya mayar da Hakimi kamar wani ubansa, to kice su yanka a haɗe gaba ɗaya da na gida, in Baffan ya dawo ace masa mantawa aka yi".
Maga ta miƙe tana ƴar dariya ta fita, Yaya ta shigo ita ma, ta durƙusa tana cewa,"Hajiya wai ki bayar da maƙullin store za'a ɗebo lemuka".
"Zaytuna duba drower ɗin nan ki miƙo mata maƙulli".
sai kuma ta dubi Yayan ta ƙara cewa,"don Allah da an ɗebo a rufe saboda jiya sai da akayi mana ta'adi".
Umman Nadiya ta shigo ɗakin a lokacin.
"ke Madina da ma Turaki aure ya ƙara?".
Hajiya Madina ta kalli fuskarta a cikin madubi tare da yin murmushin takaici sannan ta ce,"wa ya guntsa miki wannan maganar?, to ba sabon aure yayi ba tsohuwar matarsa ya mayar, ita ma kuma don fitinanniyar Kakarsa ta ƙara tayar da rigima ne, yauwa biyayya ya ƙara yi a karo na babu adadi, don Allah a bar ɗana ya huta a daina yawan zancensa ana faɗar masa da gaba, haba tun jiya da akace an ɗaura aure da shi ake ta ƙwala kiran sunansa acikin gidan nan kamar wanda yay sata, to idan ma auran ya ƙara zunubi ya aikata ko me?, ina ruwan wani?, ko ba mata huɗu aka halasta masa ba?, haba mutane da shegen gulma da tsugudidi".
Umman Nadiya tace,"to jarababba Allah ya ba ki haƙuri, ni tambaya nayi ba wani abu ba".
Hajiya Madina dai bata ƙara tanka mata ba, ta haɗe rai ta juya kan Zaytuna tana yi mata faɗan kukan da take tayi tun jiya da aka ɗaura aure.
"ni dai ina ga sai na haɗa miki da duka tukunna, haba kuka yaƙi ci yaƙi cinyewa abu tun jiya, to ki shiga hankalinki da ni".
Umman Nadiya tace,"to ai dole tayi kuka, ita kaɗai ce fa acikin su zata yi nesa".
"yo nesa abu da ba ƙasar zata bari ba, Allah na tuba ina nan ina Abuja, shi ma ɗan banzan Bellon da ya biyewa Baffa ya mayar da shi can abujan, ai sai da na faɗa masa ya dage ya barsa su ci gaba da aikinsu anan. ban ma san munafikin dai da ya bayar da shawarar buɗe wani kamfani ba tare da saninmu ba, ko da yake yanzu ai mu ƴan banza ne a wurin Baffa, duk ya mayar mu ƴan wofi, wannan fitinanniyar tsohuwa duk ta bi ta hargitsa mana zama, Allah ya shiryeta kawai, yanzu tun da dai an mayar da auren sai ta bar hankalin kowa ya kwanta".
ta kamo kunnen Nihal da ke shigowa ta murɗe,"ke, ke, ke, ki kiyaye ni fa".
"Maama wallahi Hammah ɗin ne fa ya koro ni, wai daga nace ba za'a bawa masu jeran kayan Ilham abinci ba".
"mtsww Allah ya sauƙa, to Mum ɗin ku tace ki wuce ki karɓo mana kayanmu tun ranki bai ɓaci ba".
"ehh yanzu zan tafi, Maama to sauran kuɗin ai za ki cika min".
"nawa ne?".
ta ɓoye ƴar dariyarta tana leƙo jakar Hajiya Madina dake saman