NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 284 of 323

a danne danne taƙi rabuwa da wayar, abinka da ɗan ƙauye yayi agogo, magana ma in yay sai ta ɗau lokaci kafin ta ba shi amsa. "ba sabanban". tayi murmushi kafin tace,"su Ummi su na gaisheka, Dada tace in ce ka gaida Boɗejo". "yaushe ku ka yi waya?". "ɗazun da kaje masallaci. Ummi na tayani godiya". kallon da yay ma ta yasa tayi saurin rufe ido, ya kama hannun yana faɗin,"Don Allah Hottie, ɗan kaɗan fa". tai saurin barin jikinsa ta ajiye wayarta ta dunƙule a waje ɗaya. "ni a'a, har yanzu ina jin zafi". Daga wannan ranar, sabuwar rayuwa ta *MH*(Muhammad & Halima) ta fara, sabuwar shaƙuwa, sabuwar soyayya, tarairayar juna da kulawa. zuwansu ƙasar Ausburg ba ƙaramin daɗi yayi mu su ba, Fillo an waye an kile, mo re soyayya kawai suke yanda su ke so, kullum su na kan hanyar yawon shaƙatawa, a fita tun safe a yini a bakin beech. wata irin soyayya Turaki yake nuna ma ta me ban sha'awa, yayin da ita ma anata ɓangaren bata ƙyale ba, don tuni Nuratu ta ɗorata a layin manya, ƙoƙari take yi sosai wurin ganin ta faranta ran Turaki, wajen ganin ta mantar shi kowacce mace a rayuwarsa, wajen ganin ta zama ita ɗaya a duniyarsa, gaba ɗaya rayuwar Fillo ta sauya acikin irin kulawar mijinta da tarairayarsa, this week su ne a wannan ƙasar another week su ne a wata ƙasar, acikin wata guda sun manta ma da nigeria gaba ɗaya. su ci abinci tare, su yi wanka tare, su yi bacci tare, shi kansa aikin gida tare su ke yi, su shiga kitchen tare su yi girkin su a tare, don ba sa tsayawa wani bin order, goggling girki take da irin kayan abincin ƙasar su sarrafa abinsu, kuma in suka dafa kamar ma sun fi ƴan ƙasar iyawa. a kullum idan su na tare sai su ke ganin tamkar lokaci a tsaye yake cak, tamkar babu kowa a duniyar nan sai su biyu kacal, rayuwa su ke yi acikin kwanciyar hankali da natsuwa. wajen ƙarfe bakwai na safiya a ƙasar Australia, Fillo na tsaye ne gaban mirror tana tattare jelar gashinta ta tufke acikin ribom, tana sanye ne da ƙaramar riga armless milk colour da tayi matching da skin ɗinta, sai short skirt da ash color da ko gwiwarta bai kai ba. kayan sawarta kenan a kullum tun da su ka baro nigeria, don su ne choice ɗin Turaki, ba ya son wata atamfa da danginsu, shiyasa ko da za su taho ko ɗankwali bai bari ta ɗauko ba banda kayan dake jikinta, sai da su ka sauka a ƙasar tukunna yaje ya rakito ma ta uban ƙanan kaya kamar wanda zai buɗe store. tasa hannu a bayanta ta barƙala yay ƴar ƙara, a gajiye take gaba ɗaya, daren jiya su ka dawo daga saudia, bata taɓa jin rashin jin daɗin zaman jirgin ba sai a jiya. madubin ya haska ma ta fuskar Turaki da ke tsaye a bayanta, wanda yasa hannu ya zare ribon ɗinta gashinta, ya baje a kafaɗarta. "na fi son ganin gashinki a haka". ya faɗa yana rungumeta ta bayan tare da ɗora fuskarsa akan gashin yana goga hancinsa akai. "kullum ƙara kyau kike yi, tell me the secret". ya faɗa yana kama hannunta, ya shiga tracing jan lallen da akayi mata da suka je india. "hannun ya ƙara kyau da ya fara ƙiba yanzu". sai ya ƙara cewa,"na ga twins ɗi na su na ƙara cika". ya faɗa yana zura hannunsa cikin rigarsa ya shiga shafa breast ɗinta. ta lumshe ido kawai kamar me jin bacci, jinta take yi kamar bata da lafiya. ganin yanda tayi wani collapse ya juyo da ita yana cewa,"what happened to my Angel". da narkakkiyar shagwaɓa tace,"yaushe zamu koma gida, na gaji da zaman nan ɗin, yawon ma na gaji da shi, i want to see Mum, Maama, Ummi, Kaka, Dada, Adda Zaytun, Hammah Hamid, and Boɗejo, i am missing them alot". ya rufe ido kafin yace,"not now". ta riƙo hannunsa kamar zata yi kuka ta ce,"haba my soul, mu tafi gobe please, Allah na gaji da cin abincin ƙasarar nan, duk komai na ci babu daɗi, ina so inje in ci tuwon Kaka". "haba Hottie we just spend only 3months fa, ai bamu gama honeymoon ɗin ba, ki bari mu cika 5months ɗin da Bello ya ban takardar hutu da ƙyar". tayi shiru bata ce komai ba. zai ɗauketa ta hana shi tana faman yamutsa fuska, ya waro ido yana cewa,"why?, wani abu na damunki ne yau?, duk naga kin yi wani iri kamar mara lafiya, tell me ina ne yake miki ciwo?". ta wuce ta barshi bayan tace,"idan ka ɗauke ni zan iya yin amai". ya bi bayanta da kallo, har sanda ta kwanta kan gado kamar wata mage, duk sai yaji tausayinta ya kama shi, may be har yanzu stress ɗin jiya bai rabu da ita ba. ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi kaɗan tace,"i want to sleep". ta faɗa tana mayar da idonta ta rufe. ya cire bluetooth ɗin dake maƙale a kunnensa ya ajiye akan mirror, tun da tace she want sleep tana nufin yazo ta kwanta a jikinsa, dan in dai ba dole ba bata taɓa iya bacci in ba ajikinsa. ya hau gadon tare da kwantar da ita a jikinsa, a hankali yake shafa bayanta. _tauraruwa ɗawisu, a Mata ni banga kamarki ba Fulani Nah. ke ce gaba domin kin ba su rata, tauraruwa ke ce me haska Mata, ko ince autar Mata don kina da gata, ba mai taɓaki in bar shi, me sonki dole in so shi...
🏠