au rana ta farko da yaji kamar yay ihu saboda rashin samun damar maido da ciwon wani jikinka.
yana kallo ta fito tana dafe bango, ba zai iya jurar ganin yanda take takawa da ƙyar ba, kawai ya miƙe yaje ya ɗaukota, ya kunce towel ɗin ya saka mata jallabiyarsa, ya buɗe wadrobe ya ɗauko hiram ya yafa mata sannan ta tayar da sallah.
after ta idar ta kalle shi kaɗan tace,"ina so in kwanta".
ya taso ya ɗaukota ya dawo da ita kan gadon, sai da ƙyar ta buɗe baki ya zuba mata maganin ta sha, tun da ta sha kuma sai ta fara kukan ita Ummi ya kai ta wurin Kaka, tana jin zafi sosai ya kai ta su yi mata magani, acikin kukan kuma bacci ya ɗauketa.
ƙarfe goma sha ɗaya Fillo ta buɗe idonta a hankali, daki-daki ta dinƙa tuna abin da ya shiga tsakaninsu a daren da ya wuce, har yanzu a cikin kanta tana jin haskawar furucinsa na please help da ya ambata yafi sau a ƙirga, bin ɗakin ta dinga yi da kallo kafin ta iya miƙewa zaune.
karaf idonta ya fara sauka akan wani card da ya ɗauki hankalinta, ta ɗauko tana karanta rubutun da ke ciki, ɗauke da handwriting ɗin mutum ɗayan nan a duniyarta.
_i am proud of you wifey, very proud of you Angel, you are a precious girft to me from God, i love you so much Angel...Allah ya bamu ƴaƴa ma su albarka. Barka da tashi._
bata san lokacin da wani murmushi ya suɓuce ma ta ba, ta kai hannu zata taɓa cikinta idonta ya sauka akan kwalin waya dake kan blanket ɗin, Samsung W21, kamar ta so ta san wayar, sai ta tuna shekaranjiya ne su Nilfat ke browing suka ganta, ana lissafin kuɗin wayar 1.4something ML, ta ɗauka kwalin tana shafawa.
a lokacin ta ankare da farar takarda dake saman pillow daga gefen kanta, ta kai hannu ta ɗauko haɗe da maƙullan mota guda biyu da suke ajiki.
tana riƙe su a hannunta zuciyarta ta karanta ma ta,_another suprise, a huge suprise._
a sannan idonta ya kai kan wani gajeran rubutu ajikin ƙaramar papper,_Gratification of what you gave me last night._
cike da zumuɗi ta buɗe takardar, doguwa ce ɗauke da dogon rubutu acikinta, takardar shaidar mallakar gida ce da ke ƙasar Ausburg ɗauke da sunanta a jiki, *Halima Muhammad Barkindo.*, ta ɗauki keys ɗin guda biyu tana juya su a hannunta.
bata san lokacin da ta ƙwala ƙarar murna ba, daidai da shigowar Turaki ɗakin, ta kalle shi ta yunƙura zata miƙe sai taji ba zata iya ba, lokaci ɗaya hawayen tsananin farin ciki suka zubo mata.
ta buɗe hannayenta tana kallonsa tattare da so da ƙauna, sunan da bata taɓa ji ya shiga cikin kanta ba, sunan da bata taɓa alkintawa ba a mind ɗinta, sai a lokacin taji wanzuwarsa acikin zuciyarta da ma ruhinta.
"come to me Jannaty...".
tray ɗin hannunsa ya ajiye kan table ya taho gareta, a gabanta ya duƙa ya shiga jikinta kamar yanda ta buƙata, ta kewaye shi tana masa wata special runguma, ta ce,"thank you so much for the gifts, thank you Jannaty, love you more, i'm very proud of you, you made my world so beautiful, Ya Rahman ya saka maka da gidan Aljannah".
ta faɗa tana ɗora bakinta a wuyansa tayi kissing ɗinsa.
"Jannaty...". ta kira sunan nasa bakinta yaƙi rufuwa.
yaja hancinta ya ce,"yau ba Turakin?".
sai tace,"Turaki ina so zan ga motan".
"bakinki kawai ne ya iya faɗin sunan Turaki".
ya kamo hannunta ta tsaya akan ƙafafunta da ƙyar, kafin ya ɗauketa suka fita, a downstairs su ka wuce su Sakina dake zaune a parlon su na kallo.
a sanda Fillo taga motoci biyun, a lokacin ta nemi ciwon da ke jikinta ta rasa, ta doka uban tsalle ta maƙale wuyansa cike da tsananin murna.
godiya kawai take zabga masa tare da jero tarin adu'oi, ta nemi wannan kunyar tasa da take ji tun a daren jiya ta rasa.
"Maama tayi min kyautar su, ni kuma naga babu wanda ya dace da su sama da ke. ina sonki da yawa Angel".
sai da ta shiga duk mota biyun kafin ya ɗauketa su ka koma ciki, yana faɗa mata idan taji sauƙi zai fara koya ma ta driving.
ya sauketa a kan kujera, ta shaƙi iskar bakinsa da ta fita a lokacin, ta marairaice murya tare da faɗin.
"you have your breakfast without me?".
ya kalli yanda tayi narai-narai da fuska kaman zata yi kuka.
"ban yi breakfast ba Angel".
"but naji bakinka na ƙamshin mint leave and coffee".
ya ɗaga mata gira tare da miƙewa yaje ya ɗauko tray ɗin da ya shigo da shi ɗa zu.
"kurɓa ɗaya nayi, and am sorry for that".
"wa ya haɗa wannan?".
"ni ne".
"ummm".
"da gaske fa, i make this coffee for you, Zaytun na kira ta faɗa min yanda zan yi. tana ta min dariya da tambayar ƙwaƙwaf".
da kansa yay feeding ɗinta har ta ƙoshi, sai bayan nanne ya kira sunanta da Mrs Turaki.
abin da ya faru daren jiya ya dawo ma ta sabo, kunya ta lulluɓeta, ta yi saurin saka hannu ta rufe fuskarta.
"wallah you are so sweet Angel, you finished me yesterday night, shiyasa zan koma kiranki da Hottie, ƴar ƙarama da ke kin zautar da ni".
ba shiri ta ƙara ɓoye fuskarta a jikinsa.
da daddare su na zaune, kan Fillo na saman cinyarsa, yayin da wayarta ke riƙe a hannunta, tun ɗa zu take t