dawowa ƙarar text na ƙara shigowa. _just use salt and veniger is oak._
ya jefar da robar baking soda ɗin sannan ya shiga toilet ya kashe ruwan da ya kunna yake ta zuba, ya zuba abin da zai zuba ya sirka ruwan sannan ya fito.
yana kama blanket zai ɗaga ta damƙe tana girgiza masa kai,"please".
ya rufe ido ya buɗe,"babu abin da zan ƙara miki Angel".
sannan ta iya sakin blanket ɗin ya ɗauketa, yana sakata acikin ruwan ta fashe masa ta wani irin kuka tana riƙe shi, sai yaji kamar ya fito da ita, but he has no other choice.
"sorry Angel, i know it is painful but that will only make you feel better".
azabar duniya ta ishi Fillo, ta ƙara damƙo shi zata fito ya daɗa mayar da ita, kuka take sosai tana faɗin zata mutu, a sitz bath ɗin nan dai gaba ɗaya ta ruɗa Turaki ta gama gigita shi.
kuma duk uwar masifar da ta dinƙa masa akan ita ya fita ya ƙyaleta bata son ganinsa amma yaƙi fita, har sai da ya tabbatar ta ga su tukunna ya cirota yay mata wanka da kansa, anayi tana kai masa duka, bayan an gama sannan ya naɗota a towel kamar new born Baby ya fito da ita.
yana ɗorata saman gadon ta zabga masa harara,"ƙafana ba zai kuma iya tafiya ba".
ya zauna tare da kamo hannunta, zata ƙwace ya hana hakan, kissing forhead ɗinta yay kafin yace.
"Allah ya yi miki albarka, Allah yay miki sakayya da Aljannatul firdaus, na gode da kika kula min da kanki, yanda kika saka ni cikin farin ciki, ina roƙon ubangiji ya bani ikon faranta miki har ƙarshen rayuwata, insha'Allahu ba zan taɓa cutar da ke ba, wannan alƙawarina ne".
sai ya saketa yace,"kina jin ciwo a jikinki?".
ta ɗaga masa kai,"ai duk ka ɓalla ni".
"ban ɓallaki ba Hottie, yanzu ma zan ke baki abincin da zai sa kiyi ƙiba ba za ki ɓalle ba".
ta ɗaura kanta saman shoulder ɗinsa tace,"zafi nake ji".
ya ce,"ai na?".
sai tayi shiru, ya sauke numfashi yana shafo gefen fuskarta.
"zai daina, zai daina zafin kafin safiya".
sai kuma ya kira sunanta,"Fulani Nah".
ta amsa,"ummm".
ya ce,"I don’t have all of the words to express how much you mean to me. I can only say that you are the center of my life and everything else revolves around our love for each other. I will keep caring, adoring and loving you forever, during the easy times and the challenges we will face. I love you so much Angel".
ya shiga shafa fuskarta yana faɗin,"you deserve a gift from me in return of what you gave me".
"Bacci nake ji". ta faɗa da tsantsar shagwaɓar da ta motsa zuciyarsa, cikin murya me ban tausayi.
bargon ya ɗaga ya shigar da su ciki, da farko taƙi kwanciya a jikinsa saboda tsoronsa da take yi, kuma da ya shiga kalallameta sai ta lumshe ido ta lafe a ƙirjinsa lokaci ɗaya bacci ya ɗauketa.
shi kuma baccin da bai yi ba kenan har akayi kiran asuba, ya ƙura mata ido sai kallonta yake yi kamar tv.
ya zareta daga jikinsa a hankali ya tafi masallaci, har ya dawo bata ko motsa ba, yana taɓa jikinta yaji zafi rau kamar garwashi, yaji hankalinsa yay mugun tashi saboda zafin jikin nata ya wuce tunani.
tarkacen magungunsa dake watse a ƙasa ya kalla, ya duba kaf ciki babu pracetamol, sai can ya tuna akwai acikin maganinta da ke ɗaki, yana zuwa ya tarar babu, sai ya dawo ya ƙara taɓa jikin nata yaji ba wani sauyi.
ya ɗau waya ya kira Zaytuna bata ɗaga ba, sai ya kira ta Samha, tana ɗagawa yace,"kaiwa Zaytun".
jin muryarsa a rikice ta ce,"Hammah lafiya?".
ya buga mata tsawa,"nace ki kaiwa Zaytun".
da sauri ta diro akan gadon ta fita zuwa ɗakin Zaytuna, lokacin ta idar da sallah kenan.
ta karɓi wayar hannun Samha da ke yi mata alama da ido, ganin sunan Turaki ajikin screen ɗin taji mamakin kiran nasa a wannan lokacin ya kamata, ta haɗiye guntun yawu kafin tace,"hello Hammah...".
ai tun bata ƙarasa ya yarfa mata zagi yana yi mata masifa akan ƙin ɗaga waya.
baiwar Allah cikin sanyin murya tace,"na shiga uku, Hammah yau ni ɗin?, Allah ya baka haƙuri".
yaja tsaki, ba abin tayi magana ba ya ƙara yarfo mata wani zagin, don haka tayi shiru tana jiran cewarsa.
daki-daki taji yana karanto mata sunayen drugs ɗin da ta san nasa ne, daga ƙarshe taji yace,"wanne me zazzaɓi zai sha aciki?".
ta ce,"babu pracetamol ne?".
daga tambaya sai cibi ya zama ƙari, ya taso mata kamar zai rufeta da duka ta cikin wayar,"in akwai zan kiraki ne".
ta ɓata rai tana jin kamar ta kashe wayar.
"ibuprofen ko pracetamol zaka bata".
"duk babu anan, ki kawo min yanzu".
ta waro ido waje tace,"Hammah asuba ne fa".
yay tsaki,"kaiwa Sameer ki faɗa masa ya kawon yanzu, kar ya taho a ƙafa".
yana gama faɗa ya kashe wayar.
ba'ai 5minutes ba sai ga Sameer ya zo, yana fita ko gaisuwarsa bai amsa ba ya warci ledar maganin ya dawo.
ya ɗago Fillo ya zaunar da ita, ta buɗe ido a hankali ta kalle shi, zata sa kuka yay saurin cewa,"sorry Angel, sallah za ki yi".
jin ya ambaci sallah ta buɗe ido gaba ɗaya, taƙi yarda yay helping ɗinta sai da kanta taje toilet, duk taku ɗaya idan tayi sai zuciyarsa ta matse, y