NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 28 of 323

wn na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani ai dodo ne". Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan ba a lokaci ɗaya. Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa". "ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata". Me gadin ya faɗa yana yi mata nuni da part din Hajiya Madina. Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai. Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga acikin ranta, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer dake fitowa wanda bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka. Fillo dai kokawa ta kama yi da ƙofar, ta tura ciki taƙi shiga, ta kuma yi ƙoƙarin kama handle ɗin ta janyota nan ma ƙarfinta ya kasa. kamar zata yi kuka ta juya taga saura steps 2 ya ragewa Sameer ya gama sauka. Cikin saurin murya tace da shi. "don Allah kazo ka buɗe min". Ko da ya juyo ya ganta kamar ba zai dawo ba sai kuma ya dawo ɗin, ta wutsiyar ido yake kallonta. Maama me ƴan aiki, ko aina ta samo wannan kuma oho. Yasa hannu ya janyo glass ɗin da aka rubuta open daga jikin handle ɗinsa, yay ɗan murmushi saboda yanda yaga Fillo ta kafe hannunsa da ido da alama tana so ta koyi yacce zata buɗe ne saboda gaba. Ya bata hanyar shiga yana ce mata,"ki ke shiga ta back door, in ba haka ba ƙasusuwanki akan wannan ƙofar zasu ɓalle". Gyaɗa masa kai kawai tayi tukunna ta shige ciki, ai bama sai ya faɗa mata ba, dan ta gama ayyanawa daga yau ba zata ƙara dawowa ba. Yau ɗin ma saboda bata so Kaka taji babu daɗi ne shi yasa banda haka tuni ta juya, ƙofa sai kace dutsen duniya, ai da taci gaba da gwada ƙarfinta wajen buɗewa kaf ɗinta zata kakkarye. Tana tsaye tana ƙarewa haɗuwar parlon kallo tare da saƙe-saƙe cikin ranta Samha ta fito daga wani room dake parlon, ganinta ƙatuwa yasa Fillo saurin durƙusawa tana gaisheta a tunaninta itace Hajiya Madina. Murya can ƙasa Samha ta amsa gaisuwatata ba tare da ta ko kalli inda ta ke ba, ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta sauya channel. Wani abu ya tuƙe a wuyan Fillo, kenan haka Hajiyan ke wulaƙanta mata Kaka?. tausayin Kakar ya kamata, cikin ranta tana adu'ar Allah ya horewa Amir dai suyi aurensu ko sa huta da wannan bautar a ƙasan wasu balle a dinga wulaƙanta su. "gadin ƙofa aka saka ki ne?". Samha ta tambayeta bayan wucewar daƙiƙu biyar. Fillo tace,"a'a Hajiya, ban san aikin da zanyi ba ne". Samha ta ɗago ido tana ƙare mata kallo, garin kwashe-kwashen Maama yau kuma me ƙanjamau ta ɗebo musu, halitta babu kyan gani jiki sam babu tsokar arziƙi, kai da gani kasan ba'aci an ƙoshi ba. baki ta taɓe sannan ta ƙara ce mata,"Maama bata karanta miki aikin da za ki ke yi ba?". Sai a sannan Fillo ta ɗago ido tana kallonta, ashe ɗazu kallon tsoro tayi mata, yarinya ce da girman jiki dalilin daya sa tai zaton matar gidan ce. A hankali tace,"ba'a nuna min ba". ta faɗa tana tura baki gaba. Da hannu Samha tayi mata nuni, ita kuma ta shige sum sum kamar munafuka ta nufi kitchen ɗin, sai faman takure ƙafafuwanta ta ke yi saboda sanyin AC da yay yawa a tiles ɗin, ga shi takalminta ta barsu acan waje. Turaki na tsaye a bakin friedge, ya ɗauko maltina ya buɗe ya tsiyaya a cup, ta tsuguna tana gaishe shi, zaton ta ko me gidan ne, amma bai amsa mata ba kasancewar da earpod a kunnensa duka biyun, har ranta taji babu daɗi, a yau ta ƙara yarda da cewar talaka wulaƙantacce ne indai yana ƙasan me kuɗi. Turaki kam bai ma san da shigowanta ba, ganin ya juyo daga inda yake facing tayi saurin matsawa daga bakin ƙofa ta ba shi hanya, yay ficewarsa still bai lura da ita ba dan hankalinsa ba wajen yake ba. tafi ƙarfin minti biyar a tsaye daga gefe ɗaya, haɗuwa da tsaruwar kitchen ɗin kawai ta ke ƙarewa kallo, ita dai badan-badan ba sai ta rantse gidan ƴan yan kan kai ne nan, ko kuma tace ba'a duniyar take ba gaba ɗaya. Fitowa tai daga kitchen ɗin dan sanin abunyi, bai zai yiwu Kaka na can kwance ba lafiya ba tazo ta tsaya anan babu aikin fari balle na baƙi. tana fitowa sukai kiciɓis da Hajiya Madina, tana kallonta ta shaida itane matar gidan, tai saurin durƙusawa ƙasa ta gaisheta, Hajiya Madina ta amsa fuskarta da fara'a tana ce mata ta miƙe tsaye. Fillo ta miƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya Madina tasa hannu ta ɗago fuskarta tana mata wani kallo, wani kwarjini yarinyar tayi mata, itama Fillon hakan ta ke a wurinta, shi yasa tun kallon farko bata bari sun ƙara haɗa ido ba. Allah ma ya sa ni Hajiya Madina ta girgiza da ganin yarinyar nan wanda ta rasa dalilin hakan, tsintar kanta tayi da jin
🏠