bakinsa nata ya ɗaga ma ta gira.
tayi ƙasa da idonta sannan ta buɗe bakin, yasa bakinsa cikin nata ya zuba mata taunannan cake ɗin, a lokaci ɗaya tayi differenciating tsakanin daɗin yawunsa da cream na cake din.
ta lumshe ido tana taunawa a hankali, yayin da Turaki ke yawo da hannunsa cikin rigarta, ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana faɗin,"Maama tace tana son ganin jikokinta, tana so tayi wasa da su".
ya murza tafin hannunta ya ƙara cewa,"yaushe za mu samar ma ta su?".
Fillo tayi murmushi tare da ɓoye fuskarta a saman sumarsa.
ya mayar da hannunsa fuskarta ya shafo sajenta,"ki amsa min don in san lokacin da zan ƙara ganin farin cikinta ya ƙaru".
"ni ma ban sa ni ba". ta faɗa in a cool voice.
yay murmushi tare da ɗago fuskarta yana kallonta.
"if you are ready we will get them today".
tayi saurin girgiza masa kai,"not today".
"then when?".
tayi shiru ba tare da amsa masa ba.
sai ya sauke numfashi yace,"ba kya tunanin nayi haƙuri da yawa kuma ina kan yi?".
ta marairaice murya cike da tsoron da ya fara kamata tace,"ai kai mai haƙuri ne, ka ƙara yi".
bai yi magana ba ya ɗauko wani card ya bata, ta karɓa ta buɗe ta shiga karanta abin da ke ciki.
_On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a wife like you is indeed a gift.. Happy Birthday Fulanin Turaki, wishing you a long life and prosperity._
wani sanyayyan murmushi ya suɓuce ma ta, ta kai laɓɓanta saman goshinsa tayi kissing, ta ce,"tanx, really appericiate".
martanin murnushin ya mayar mata, sannan suka saka cake ɗin a gaba suka yi masa cin yunwa.
mutumin da baya shan choculate sai ga shi yay damalmala bakinsa da choculate wajen sha.
bayan sun gama cin cake da shan choculate suka miƙe daga wajen, kwatakwata Turaki bai bari ta fahimci rashin jin daɗin da yake ciki ba.
suka shiga toilet tare don yin brush, Fillo tace masa tana so tayi wanka, ya fita ya barta aciki, ɗakinta yaje ya ɗauko ma ta kayan da zata saka.
after 10minutes Fillo ta fito daga wankan, sai dai lokaci ɗaya ƙirjinta yay wani mugun bugawa ganin Turaki duƙe a ƙasa ya riƙe cikinsa yana wani irin nishi.
siraran ƙafarta suka jata cikin sauri ta ƙarasa gabansa, ta tsuguna tare da ɗora hannunta saman sumar kansa sannan ta kira sunansa.
sai dai a wannan lokacin baya jin zai iya amsa ma ta balle ya iya ɗagowa ya kalleta, duk jikinsa rawa yake yi tamkar me jin sanyi, after all ɗakin lulluɓe yake da ɗumi me daɗi.
cikinsa ne ke yi masa ciwo sosai, irin ciwon cikin da bai taɓa yi ba, wani irin ciwon ciki ne da yake jikin tamkar numfashinsa zai tsaya cak.
yanayin nasa yay bala'in gigita Fillo, tuni idonta ya kawo ruwa ganin yacca yake shuri da ƙafafunsa a ƙasa, gaba ɗaya jikinta sai ya ɗauki rawa kwatankwacin yanda nasa ke yi.
duk sai ta nemi dabara da wani tunani acikin kanta ta rasa, ta kasa magana ma ballanta ta tambaye shi me yake damunsa, and bata san me zata yi masa ba.
cikin karkarwar hannu ta ɗago kansa daga duƙen da yake, hawayenta ya ɗiga a saman fuskarsa, ya buɗe idanuwansa da suka sauya kala ya dubeta.
ta fashe da kuka tana tambayarsa me ya faru da shi?.
da ƙyar ya iya buɗe baki yace ma ta,"cikina Fulani".
a hargitse ta ce,"ciwo yake ma?".
kansa kawai ya iya ɗaga ma ta.
"ko cake ɗin da muka ci ne?".
nan ma bai iya cewa da ita komai ba, ta tashi a rikice taje ta buɗe drower ta kwaso drugs ɗinsa, sannan ta fita da gudu ta sauka ƙasa ta ɗauko ruwa ta dawo.
lokacin da ta dawo ya kwanta a ƙasa yana murƙusus, ta dawo ta ɗago shi da ƙyar, jikinsa duk ya jiƙe da gumi, kuka kawai take yi a lokacin ta kasa cewa komai.
"buɗe bakinka kasha magani". ta faɗa cikin muryar da ta dusashe da kuka.
sai ya buɗe idanuwansa ya dubeta a cikin gigitar ciwo da neman fitar hayyaci, ya manna kansa a cikinta gami da cusa fuskarsa a ƙirjinta.
ƙamshin turaren da tayi wanka da shi ya ƙara motsa ciwon nasa, sai ya damƙo hannunta cikin kyarmar jiki ya ɗora a mararsa ya danna.
lokaci ɗaya taji ya kanainayeta ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da taji tamkar zai ɓalla ƙasusuwanta, ƙanƙamar da ta hanata motsi ko kaɗan.
hankalin Fillo ya ƙara tashi, cikin firgici ta buɗe baki, murya na rawa ta fara ce masa,"ga maganinka na ɗauko, don Allah ka tashi ka sha, i don't want to lose you".
Wani irin rumtse idanu Turaki yayi saboda azaban murɗawar da mararsa ta ƙara yi, ya daɗa ƙanƙameta tare da ƙara danna hannunta a saman mararsa.
Fillo ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin,"in kira Maama?, ban iya driving ba in kira Adda Zaytun?, ko Bello zan kirawo?, in je in faɗawa Baba me gadi?".
tai maganar duk a gigice tana ƙoƙarin zare shi a jikinta taje ta ɗauko wayarsa.
sai ya kai hannunsa zuwa wuyanta, ya sunkuyo da kanta yana ɗago da fuskarsa daga saman boobs ɗinta da ya cusa.
muryarsa a shaƙe tamkar ba tas