NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 278 of 323

ba sai da ya danna horn da ƙarfi sannan ta buɗe ido. "a sauka a miƙo kuɗin mota". ya faɗa a sanda take ƙoƙarin buɗe ƙofa zata fita. ta juyo ta ɗan kalle shi tace,"in doller or in naira?". "in doller". ta gyaɗa kai kafin tace,"to driver you wait for me". Turaki ya buɗe baki galala, zai kamota tayi saurin ficewa tana dariya, shi ma ya fito ya bi bayanta da sauri don ba ya so ta riga sa hawa upstairs becx akwai suprising ɗinta da yake so yayi. a parlo ya sameta su na gaisawa da su Sakina, waɗanda suke kallo a parlo, su na yi mata sannu da zuwa, ita kuma tana ba su haƙurin tafiyar da tayi bata sanar musu ba. bai ko amsa gaisuwar da su Hannatu su ke masa ba ya kama hannun Fillo su ka ɗauki hanyar upstairs, a steps na uku da su ka taka yasa hannu ya rufe ma ta ido. ta san duk neman hanyar su shirya ne don haka sai taƙi kula shi har sanda taji ya buɗe ƙofar ɗaki sun shiga. ƙafafunta suka lume cikin marbles, da sanyin ac'n da ke ratsawa ta ko'ina acikin ɗakin, kafin daddaɗan ƙamshin nan nasa dake motsa zuciyarta ya shiga hancinta, taji san da ya maida ƙofar ya rufe, kafin ya sauke hannunsa a hankali daga idonta ya mayar kan ɗan ƙaramin ƙugunta, tare da ɗora haɓarsa a saman ƙafaɗarta. "suprise". hakan ya faɗa before ta shiga buɗe idanunta a hankali. ba ta san lokacin da ta buɗe idanuwanta duka ba, laɓɓanta suka tale kafin bakinta ya buɗe, fuskarta kuma ta bayyana wani irin farin ciki da jin daɗi. ƙananun bulbs ɗin dake haskawa zuwa different colours of light su suka fara shiga idonta, kafin baloons ɗin da akai design da heart shape ta ɗauki hankalinta, zuciyarta kuma taji ta motsa da zafin ƙauna a lokacin da ta ɗora ido akan flowers ɗin da aka baza akan gado. gaba ɗaya sai ta kasa magana balle motsi saboda yacca abin ya burgeta, sai ta fara bin kowacce kusurwa ta ɗakin da kallo, ta san ɗakin, wan nan ɗakin ne da suke rayuwa ita da Turaki a cikinsa, kuma wan nan lafiyayyan gadon me ɗauke da flowers, gadon su ne me ɗauke da katifar nan me bala'in taushi da suke kwanciya akai manne da juna, but ta ya akayi yau ya sauya?, azababben decoration ɗin da aka yi masa ya mayar da shi tamkar ba wannan ɗakin da suke yini acikinsa ba. _me hakan yake nufi?._ tambayar da zuciyarta tayi kenan, kuma sai taji hannayen Turaki sun kama fuskarta sun karkartar da ita zuwa gaban body mirrow dake gefe ɗaya, ƙwayar idonta ta tsaya cak akan ballon numbers ɗin da aka jera me ɗauke da 1 and 9 making 19, a hankali kuma idonta ya sauka akan ƙaton cake ɗin dake kewaye da candles. muryar Turaki tayi whispering acikin kunnenta da faɗin,"Happy Birthday to you Fulani Nah". she was just astonished, ta juyo ta fuskance shi tana faɗin,"my birthday?". ya jijjaga ma ta kai alamar ehh. with great joy tace,"but how do you know Turaki?, i don't think there is anyone who knows my birthday date". ya ce,"har Ummi?". tayi ɗan shiru tsananin farin cikinta na kasa ɓoyuwa ta ɗaga masa kai. ya daɗa kama ƙugunta yace,"to Ummi ce ta faɗa min, tace ta haifeki a ranar da Yayarta ta rasu shiyasa ba zata manta da date ɗin ba, you are 19years older now, Kaka ce take lissafi ba daidai ba". ta juya ta ƙara kallon yanda aka ƙawata kyan ɗakin. "and all this becouse of my day?". "yes! domin farin cikinki kawai". ya faɗa yana sumbatar kumatunta. hawaye su ka saukowa Fillo ta juyo tayi masa wani irin tight hug. ruwan hawayen ya ɗiga a bayan Turaki, ɗuminsa ya wanzu acikin fatarsa, yasa nasa hannun wurin kewayeta yana shafa gashin kanta, ya ce,"why the Cry Fulani Nah?, i did everything just to make you happy not to make you cry, please stop crying let us celebrate the day". ta ƙara fashewa da kuka tana ƙara rungume shi. "you totally suprised me!, am so blessed and honored to have you, thank so much you for making my birthday so special. You made me feel like a princess and gave me the best gift anyone could ever receive. You are my best friend and I love you more than anything in this world! Thank you for making my day special with your love, care and amazing surprises. i am so lucky to have a wonderful husband like you". ta sake shi tana haɗe goshinsu wuri ɗaya,"Allah yaja da ran mahaifanka, Allah yasa ka rabu da su lafiya, Allah ya ba ni ikon faranta maka nima". ji tayi ya ɗagata sama yana hajijiya da ita yayin da suke rera waƙa tare, waƙar da ita bata iya ba sai in yayi sai ta kama, a haka ya dinƙa zagaye da ita acikin ɗakin har sai da ta fashe duk baloons ɗin da aka ɗaura. kafin ya sauketa ya kama hannunta suka ƙarasa gaban cake, ya zauna a kan ƙaramin carpet ɗin dake shimfiɗe a wajen, sannan ya zaunar da ita akan ƙafafunsa da ya tankwashe. tare suka yi cutting cake ɗin, ta ciro ta kai bakinsa, har ya buɗe bakin sai ta fasa saka masa ta janye tana ƴar dariya, tasa a bakinta tana faɗin ba zai ci ba. ta ƙara yanko wani zata kai bakinta sai ya juyar da hannun ya saka a nasa, sai da ya fara taunawa sannan ya kai
🏠