ni gurbi acikin zuciyarta, ta ƙara yin farin ciki da jin alfahari a game da dacen mata da Me Babban suna yayi.
and sosai taji daɗin hirar da Fillo take yi ma ta, sai wajen ƙarfe 9 sai ga Turaki ya shigo ɗakin, kallo ɗaya Fillo tayi masa ta ɗauke kanta, ya shigo ya zauna a gefen Maama yana kama hannunta ya riƙe.
"my happiness ya sauƙin jikin?".
Hajiya Madina ta kalle shi cike da so da ƙauna ta ce,"na ji sauƙi me babban suna, ya office?".
"masha'Allah, Allah ya ƙara miki lafiya, Zaytun ta ce min Bp ɗin ya koma normal".
"ai na faɗa maka na ji sauƙi, ɗa zu ma da kayi ta kira bacci na sa mu".
ya sauke numfashi ya ce,"insha'Allahu za ki rabu da ciwon nan Maama, ciwon nan yana takura ni da yawa".
"to Allah yasa, amma ka san girma ya riga ya kama mu, lafiyar sai a hankali, sai dai ai tayi mana adu'a ciwo ya dinƙa zuwa da sauƙi".
sai kuma ta lura da yanda Turaki ya ƙurawa Fillo ido, ita kuma kanta yana ƙasa tana matsa mata ƙafarta ta ɗaure fuska.
sai tayi murmushi tace,"Daugher ina fatan dai baku da wata matsala ko?".
Fillo tace,"ehh Maama babu".
"to Allah yayi maku albarka, ubangiji ya wanzar da zaman lafiya na har abada a tsakaninku, Allah ya kauda mugun ido akanku".
a tare suka amsa da amin.
sai ta kamo hannayensu duk ta haɗe a waje ɗaya tana cewa da Turaki,"me babban suna ina roƙonka da kar Fillo ta rasa farin ciki ko da na sakan ɗaya daga wurinka, amana na baka ita, ka kula min da ita don Allah kaji, tayi min taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba, thats why nake so ka raineta da zallar soyayyarka, ka mayar da ita tamkar jaririya".
ya shafo wuyansa bai iya cewa komai ba. sai ta dubi Fillo ma tace mata,"Daughter ɗago ki kalle ni karki ji kunyata".
Fillo ta kasa har sai da Hajiya Madina tasa hannu a haɓarta ta ɗago fuskarta ta ce,"yaushe za'a haifa min jika?, a yanzu banda burin da ya wuce naga jikana Daughter, so nake na ga ina wasa da jikokina, ina fatan za ki samar min su da wuri".
kunya ta kama Fillo sosai.
"Allah dai ya kawo mana na gari masu albarka". cewar Hajiya Madina.
cike da zolaya kuma ta ƙara cewa,"kyawawa nake so ki haifa min masu kama da ke fa, kar ki yarda su yi kama da Me Babban suna, shi wani lokacin kamar bai da kyau".
duk suka yi dariya ba tare da sun ce komai ba.
ta ƙara cewa,"Allah Daughter duk ranar da Me Babban suna yayi miki laifi ki zo ki faɗa min wallahi sai na rama miki, kinga haka...". Fillo ta ɗaga ido taga yacca ta kama kunnen Turaki.
"to haka zan murɗe shi wallahi har sai yaji a jikinsa". Fillo tayi ƴar dariya shi kuma ya wurga mata harara fuska a cukule.
kafin nan tace da su,"to ku tashi ku tafi ko, dare yana ƙara yi".
Fillo tayi saurin cewa,"Maama don Allah zan kwana anan".
ta faɗa a marairaice.
Maama tace a'a ta tashi tabi mijinta su tafi, har ƙwalla sai da tayi da suka baro wajenta, sai da suka biya ta wajen Mum suka yi ma ta sallama kafin su tafi.
a compound juyin duniya Fillo taƙi yarda Turaki ya kama hannunta, bata yarda ma sun jera ba ganin babu idon kowa, tayi gefe yay gefe, suka shiga mota ma taƙi kallonsa, sai faman ɓata rai take yi tana cin magana.
da tsokana ya ce,"kika ce ba za ki dawo gidan ba".
ta kalle shi sosai kafin ta ce,"da kayi ignoring message ɗin nawa hakan ai bai sa na damu ba".
tun yana tsokanarta har ya rabu da ita saboda ganin ta ɗauka zafi, a lallai fushi take da shi kan ƙin responding messages na ta.
ya koma sai dai ya kalleta yay murmushi ya shafo wuyansa, shi ba abin da ma yake so irin ta kula shi suyi rigima, tayi kuka ko tayi masa tsiwarta.
motar tayi shiru ba abin da kake ji yana tashi sai busawar ac da kuma sautin waƙar i miss you ta Beverley craven.
_here in a silence i wait, there is nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how my aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm couting the hours without you, and i don't know how much i can bear, becox i miss you morethan word can say, all i need you here in my life always, yeah i miss you, till you are back with me._
waƙar ta dinga bin gaɓoɓin jikin Fillo tana ratsata, ta kalle shi ta wutsiyar ido taga ya wani sha murr kaman ba shi ke tsokanarta ɗa zu ba fuskarsa a washe da annuri, wanda ta tabbatar na jin daɗin ganinta ne.
sai ta ɗan murguɗa baki kamar yana kallonta kafin ta kai hannu ta kashe waƙar, tana ɗauke hannu yana ƙara kunnawa, zata ƙara kashewa taji muryarsa a tamke yace,"ranki zai ɓaci".
"to bana son jin waƙar ni".
yay mata wani kallo yace,"motarki ko tawa?".
ta haɗe gira tace,"ba yanzu aka gama baka amanta ba, aka ce kayi min duk abin da nake so".
murmushi ya suɓuce a leɓensa, ya tuna alƙawarin da yaywa Maama na kula da Fillo tun ba'a ranar yau ba, ya tuna girman alƙawari, sai ya kai hannu ya kashe waƙar.
sai ya koma yi da kansa, Fillo taji waƙar tafi daɗi sosai a bakinsa, sai ka rantse shi ya raira, ta lumshe ido tana ta sauraronsa, har su ka zo gida bata sa ni