NOVEL SHARES -
a ɗan murguɗa baki bata ce komai ba.
ya lanƙwasa yatsanta ya ce,"ni dai kici tuwon dawa da yawa kiyi ƙarfi, don karatun ba na wasa ba ne, Mum tace 7days za kuyi, ni kuma 7days yay min yawa, dan haka ki dame ta ku taho jibi".
tai lamo da kanta a kafaɗarsa tana cewa,"kamar ma kar na koma ai, family ɗin ku su na da kirki sosai".
"ni ma haka suke ta ce min wai nayi sa'ar mata me hankali da mutunci, anyway yanzu dai faɗa min when zaku dawo?".
ta ce,"to ka zauna anan mana kaima".
"kije ki faɗawa Mum hakan".
suka miƙa yana manneta a jikinsa,"7days yayi yawa Fulani Nah, ki faɗawa Mum hakan".
ta ce,"7days yayi kaɗan Turaki, ina so zanje inga Ummi nah, kaga babu nisa daga nan".
bai ƙara cewa komai ba ya kama hannunta suka fita, lokacin Baffayo har ya tayar da mota, yay ma ta side hug yace,"please don't stress your self wajen yin aikace-aikace da zuwa gaishe gaishe, dan gidan nan da kike ganinsu aiki suke kamar injina. fita indai ba'a mota ba ne kice da Mum ba kya jin daɗi".
ta gyaɗa masa kai kawai tana jin babu daɗi, sam bata so ya tafi.
ganin hawaye a fuskarta yasa shi cewa,"ko in faɗawa Mum ba kya son zama?".
ta girgiza kanta alamar a'a tana riƙe hannunsa.
sai yaji ta ba shi tausayi sosai.
"daina kukan Fulani Nah bana son hawayenki". ya faɗa yana share ma ta hawayen.
sai ya ɗaga waya yana kiran babbar ƴar gidan Inna me su na Hamida, tana zuwa ya ce da ita,"ki kula min da ita kinji, less hayaniya a inda zata zauna please, tana son bacci ki kula da haka, sai an bata abinci tukunna take ci if not zata zauna da yunwa, bata da cikakkiyar lafiya, so duk wanda zai zauna kusa da ita ki tabbatar is not addicted to ɓatawa mutum rai".
tace,"insha'Allahu za'a kula me sunan tsoho".
yay murmushi yana maida kallonsa ga Fillo, wacce ta maƙale hannunsa tana hawaye, ya sunkuya yana ɗora kumatunsa kan leɓenta yace,"ummm 1 peck".
abin da bata taɓa yi masa ba, kuma shi ma bai tsammaci zata yi ɗin ba, tai masa peck a kumatu tare da kissing ɗinsa a goshi tana faɗin,"i will miss you".
"i will miss you too, take care...bye bye".
ta ɗaga masa hannu tana faɗin,"bye". ya sauke ajiyar zuciya,"ba ki min adu'a ba".
tasa hannu akan ido irin yacca yara ke kuka tace,"Allah ya kai ka lafiya, Allah ya tsare hanya, Allah ya kare ka da kariyarsa".
ya amsa da,"amin, thank you so much". kafin ya iya sakin hannunta ya wuce mota, ita kuma taji wani kuka ya taho ma ta but sai ta danne shi saboda Hamida, su na shiga ciki ta wuce ɗakin Hamida ta kwanta akan gado.
wajen ƙarfe goma na dare sun kwanta ita da Hamida sai ga Nilfat ta shigo ɗakin, ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske, Fillo ta buɗe idonta don ba baccin take yi ba.
"au ashe baccin naku ma bai yi nisa ba, mijinki ne ya kira waya".
ta ƙaraso tana bawa Fillo wayar, sai taji wani daɗi ya ratsata, tun ɗa zu take ta tunaninsa, ta kasa ko baccin har Hamida tazo ta kwanta tayi nata, infact jinta take kamar mara lafiya, ta karɓi wayar tana kallon Nilfat da zata fita tace,"ki tsaya ki karɓi wayar".
ta ce,"wala, ba tawa bace ai ta Baffayo ce, yace da safe ya karɓa".
ta fita tana rufe musu ƙofar, daidai da shigowar kiran Turaki wayar.
tana ɗagawa ta saka kukan shagwaɓa,"tun ɗa zu sai yanzu ku ka je?".
"am sorry Fulani Nah, na dawo ne na tarar Maama babu lafiya, yanzu muka dawowa ma daga asibiti".
"subhanallah, me yake damunta?".
"Bp ɗin ta ne, but da sauƙi, ko in kai mata wayar?". ya tambaya jin ta damu sosai.
ta ɗaga kai kamar yana ganinta,"ehh".
yana zuwa ɗakin ya tarar Maama tayi bacci, Fillo tace da safe ya faɗa ma ta tana yi mata sannu sosai.
ya ce,"insha'Allah, tun ɗazu na kira Mum amma sai na kasa cewa ta baki. ba kiyi bacci ba ko tashinki aka yi?".
"ai na kasa yi".
"why?".
tayi shiru ta kasa cewa komai.
ya ƙara cewa,"why?, tell me".
"i am missing your warm body that make me fall asleep".
taji murmushinsa me sauti ya fito.
"sorry Fulani Nah, just close your eyes and go to sleep, I will come to your dreams, then you sleep like you used to".
a shagwaɓe ta ce,"promise?".
ya ce,"insha'Allah".
ba su jima su na wayar ba yace ta kwanta zai je Baffa na kiransa.
ta sauke numfashi tare da ce masa,"don't forget to Perform Ablution and recite Al'qur'an before you sleep".
ya ce,"i will not forget, good nite".
sam bata so wayar tasu ta ƙare, ta danne kukan kewarsa gudun karta ɗaga hankalinsa ta ce,"good nite, sweet dreams, please you take good care of your self".
"insha'Allah".
da ƙyar dai suka iya yin sallama, Fillo ta tashi ta kashe fitilar sannan ta dawo ta kwanta tayi lamo, ba don tana jin zata iya baccin ba, zuciyarta ta cika fal tare da tunaninka kala-kala, har ɓarawon bacci ya ɗauketa.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*55*
kiran sallar farko a kunnen Fillo, tana buɗe ido ta ganta a inda saɓanin Mafarkinta ya nuna ma ta.
ta ɓata fuska tana jin kamar tayi kuka, wayar Baffayo da ke gefen pillow ta ɗauko, adu'arta ɗaya Allah yasa babu pin a jiki, cikin sa'