yana kanne ma ta ido ɗaya, yau duk sai yanzu tayi masa murmushi, dan tun tashinta take faman cin magani, shi kuma bai takura ma ta ba dan ya san abin da yay ma ta ne jiya.
gida dai sai ya koma kamar gidan biki, don har wata walima suka haɗa wai ta murnar zuwan Mum, wacca tun bayan dawowarta bata sami zuwa ba, Fillo kam sosai taji daɗin zuwanta, kuma nan da nan duk sai ta sake sosai, irin Family ɗin nan ne masu saurin sabo, kuma masu sauƙin kai da mutunta wanda ya shigo cikin su.
da yamma su na zaune a bedroom ɗin Granny wata me suna Nilfat ta shigo, ta kalli Granny tace,"duk kinga balarabiya kin maƙale ma ta".
Granny tayi ma ta daƙuwa tana cewa,"ungo nan".
Nilfat ta ce,"na gode, ai ba zan bari muyi faɗa ba, dan lallaɓaki nake na bi ki europe nima naje na samo irin wannan sulɓin fatar taki da bata tsufa".
ta wuce wajen Fillo tana cewa,"ki je inji mijinki".
Hajjah Yayar Granny ta ce,"kije kice masa ba zata zo ba, ashe shi ma irin Ahmad ne bai da kunya".
"yaran yanzu ne fa, ai sai adu'a kawai, amma kunya ina suka ganta". cewar Granny.
"to Hajjah tafiya fa zai yi, ai sallama za su yi ba wani abu yace zai yi ma ta ba". Nilfat ɗin ta ƙara faɗa.
Hajjah ta ce,"kije kice masa yay tafiyarsa, dole ne sai sunyi sallamar, kaji min mara kunyar yaro, ko wani abu zai bata".
Nilfat tayi ƙofa tana faɗin,"ni dai ban taɓa ganin inda akayi irin haka ba gaskiya, ya zai tafi ba tare da yay sallama da matarsa ba, wallah idan ni ce sai ince ta fasa zama, in ɗau kayata mu tafi, yo in ma ba sallamar zai yi ba ina laifi anan dan miji ya nemi matarsa".
Fillo dai na kusa da Granny kanta a ƙasa, har ga Allah so take taje ta gan shi, tun ɗa zu rabonta da shi wai sun fita shi da wani Baffayo ɗan gidan Anty Hajar.
Mum ta shigo a lokacin, ta zauna tana cewa,"wai Babana zai tafi, jirgin ƙarfe bakwai zai bi, daga masallaci zai wuce".
sai ta kalli Fillo tace,"je kuyi sallama". sai ta kasa sakkowa, duk kunya ta kamata, ga shi ita ba waya ba balle tayi masa text tace ya tafi kawai, sai da Mum ta ƙara yi ma ta magana sannan ta sauko akan gadon ta ɗauki mayafinta ta fita.
a compound ta tsaya tana kalle kallen inda zata gansa, Fareeda na zance daga can wajen flowers ta ƙwala ma ta kira,"Antee".
Fillo ta ɗaga kai da murmushi tana kallonta.
ta ƙarasa wajen na su, Farida tace,"ga wanda zan aura".
"masha'Allah". Fillo ta faɗa kafin su shiga gaisawa da Modi.
Farida ta ce,"mijinki ba?".
Fillo ta ɗaga ma ta kai.
"yana ɗakin Baffayo".
"ina ne ɗakin?".
"ki zagaya ta wurin shukokin nan, ɗaki na tsakiya me bishiyar ayaba a gabansa".
Fillo tabi hanyar da Farida ta nuna ma ta, tun daga ƙofar ɗakin ta san Turaki na ciki saboda ƙamshin turarensa da duk ya cika wajen, ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Baffayo ne ya amsa sallamar, Turaki kuma ya ɗaga kai yana kallonta, Baffayo ya fita a ɗakin, ita kuma ta zagaya ta zauna akan kujerar da Turaki yake, ta shige jikinsa kamar yanda ya buɗe ma ta hannu.
"yau ni kike gudu ko?".
ta ɗago kai tana kallonsa ta ce,"kaima ai mantawa kayi da ni ka tafi wani wajen".
yaja hancinta,"munje gidan wani Kakanmu ne, ƙanin me sunana, da naje su na ta tambayarki nace za ku zo ke da Mum".
"to me ka siyo min?".
"ɗa zu ba gani nayi kin saka fura agaba kina sha ba, ko irin ma ki tuna da mijinki a kusa".
"to a gaban su Mum ɗin zance kazo ka sha?".
"ni ma shiyasa ai da naje Alhaji ya ban abin daɗi ban iya cewa zan ragewa Matata ba".
tai murmushi da kiran sunansa,"Turaki".
ya ce,"na'am Halima".
ta ɗan bugi kafaɗarsa,"sunan fa Ummi ne".
yasa hannu ya rufe bakinsa,"Allah na tuba ka yafe ni".
sai kuma ya kama kumatunta yana cewa,"to ni ma ai sunan Abba ne kike faɗa".
"to ai dai ba ainihin sunansa na faɗa ba, Turaki na ce".
"ehh haka ne afiruwa".
ta turo baki gaba,"mene afiruwa?".
"ɗan siririn mutum da za ki gansa kamar lamba ɗaya, kin san one bata da kauri kwatakwata".
ta shiga kai masa dukan wasa, shi kuma yasa hannu yana karewa yana dariya har sai da ya kama hannayenta ya riƙe.
"ai indai ƙiba ce zan yi".
yace,"ni ma na san da wannan, aikina kawai zanyi".
sai kuma ya kalli agogon hannunsa ya ce,"za ki sa nayi late, jirgi ya tashi babu ni, tun ɗazu na aika ki zo kika ƙi, da nayi tafiyata ai".
"da ni kuma yau banyi bacci ba nayi ta kuka, saboda duk yau nayi kewarka ban ganka sosai ba".
"ehh ba ke bace naga yau duk kina ta shareni, kawai saboda na saka kinji daɗi jiya".
ba shiri tasa hannu ta rufe fuska, ya ɗauke hannun yana faɗin,"idan kika tashi dawowa ki dawo da babban shiri".
"shirin me?".
ya goga hancinsa da nata yana jan haɓarta,"sai kin dawo ɗin dai, ke dai kawai kici tuwon dawar Innah kiyi ƙarfi".
ta cuno baki tana faɗin,"ni dai sai ka faɗa min shirin me?".
"shirin karatu".
"wanne karatu?".
"karatun manya".
"wanne karatun manya kuma?, ni ban sansa ba ai".
ya ɗora hannunsa saman cinyarsa ya tallabi haɓarsa yana kallonta ya ce,"karatun da zai mayar da ke cikakkiyar matar aure".
t