onki ba, da yanzu bana raye, ko kuma da ban kawo yanzu da lafiyar da zan yi tafiya ba, da yanzu wataƙila ina kwance marabata da matacce numfashi kawai, kuma wataƙila da har yanzu ban ga mahaifiyata ba. saboda haka girmanki da nake gani yafi gaban tunani, kina da girman da ba zan iya ganin an ci mutunciki na ƙyale ba".
ta buɗe baki zata yi magana ya ɗora yatsansa a leɓenta,"shhhh bana son magana, ki ci abinci".
ta kalli abincin ta ce,"bana ci".
"saboda me?".
"saboda kaima ba zaka ci ba, me yasa zaka tsaya siyan abinci bayan na iya dafawa, and beside da ka siyo bafa ci zaka yi ba, so kake ka kwana da yunwa?, ban iya rashin adalci ba kuma ba zan fara ba daga yau, Ummi ta jaddada min sau babu adadi cewar kar na taɓa barinka da yunwa".
kafin yay magana ta miƙe, ta kamo nasa hannun shi ma ya miƙe.
"muje kitchen na dafa mana abin da zamu ci".
ya dakatar da ita,"kin gaji ba za ki iya girki ba, kuma kinga akwai ciwo a ƙafarki".
"ni ban gaji ba". ta faɗa tana saƙalo hannunta guda a wuyansa sannan ta ƙara cewa,"idan ƙafan na ciwo ai sai ka ɗauke ni".
murmushi yay tare da ɗaukarta su ka fita a ɗakin, su na saukowa downstairs kitchen ya nufa, sai da suka shiga ya ajiyeta, ya kama ƙugu yana cewa,"zan ga yanda ake aiki da gurguwar ƙafa".
tayi murmushi me sauti tare da jan gemunsa ta ce,"to ai da ka ɗauko ni na warke".
ya buɗe ido yana kallonta,"ƙatoto da ni kika yiwa wayo?".
ita ma ta kama nata ƙugun ta ɗaga kai sama ta juya idanu, sannan ta ce,"me zamu ci?".
"duk abin da aka girka da waɗannan siraran hannun zan ci".
ta dafa kafaɗarsa ta ce,"ummm Maama ta taɓa cewa kana son soyayyan indomie, so yau zan ci abin da kake so ni kuma bana sonsa, but na san daga yau zan fara so, in dafa ko?".
ya ɗaga ma ta gira yana jin wani daɗi a zuciyarsa, ta wuce ta ɗora tukunya a gas, ya bi ta yana faɗin zai tayata, ta dakatar da shi,"no ba yanzu ba, zaka fara girki but not today not now, but one day. for now just sit and watch".
kujeran dining ɗin dake kitchen ya ɗauko ya zauna gefe daga in da cooker gas yake, kafin ta gama yankan albasa idonsa duk ya cika da ruwan hawaye saboda yajin albasar, tuni kuma suka zubo, sai ƙyafta idanu yake, Fillo duk na kallonsa tana ƴar dariya, tace,"me aka maka kake kuka?".
ta tambaya tana dariya ƙasa-ƙasa.
"ni kike yiwa dariya?".
ya miƙe zai bar kitchen ɗin ta maido shi ya zauna tana faɗin,"sorry, idan ka fita ina jin tsoro".
ya ƙanƙace idanu yana kallonta cikin tarin ruwan da ya cika idonsa,"Fulani Nah idona yaji".
"ni dai ka zauna haka, ina gama yankawa zai daina ai". ta faɗa tana narkar da murya, haka ya zauna babu yacca ya so, har sai da ta gama yankan albasa tukunna ta wanke masa fuska a sink.
wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga Sameer ne, yay picking Sameer na faɗa masa ga shi ya kawo masa ticket ɗin.
ya kalli Fillo ya ce,"Fulani Nah zan amso saƙo wajen Sameer".
tayi shiru kamar bata ji shi ba har sai da ya ƙara kiran sunanta.
ta ɗan ɓata rai ta ce masa,"to ya shigo parlo ya jiraka mana, idan mun kammala sai mu same shi, ni ba zan iya jira idan ka fita ba, kafin ka dawo dodon kitchen ɗin ya cinye ni".
yay murmushi yana girgiza kansa,"my drama queen". sannan yace da Sameer ya shigo ya jira shi a parlo ga shi nan fitowa.
wucewar minti goma ta kammala suyar indomie ɗin, sannan ta haɗa pineapple juice, tana sane take ta delay dan ita bata cika son Sameer ba, musamman ma idan tana tuna ƙullin da suka dinƙa yi akan su kashe Turaki.
"na gaji ka zo ka wanke min hannu".
ta faɗa a sanda ta nufa sink ta tsaya. ya taso ya tsaya ta bayanta, ya kama hannayen da suka shige cikin nasa, ya zuba morning fresh ya wanke ma ta.
ta ɗauka abincin da tasa a plate shi kuma ta ba shi jug da cup ya riƙe suka fita, Sameer yana zaune yana jan tsaki kaɗan kaɗan saboda ya fara gajiya, ta ajiye plate ɗin akan table tana gaida shi, ya bawa Turaki ticket ɗin yana faɗa masa ba'a samu flight ɗin 8 ba kamar yanda ya ce, sai na 9 aka samu.
kaɗan Sameer yaci indomie ɗin, shi ma saboda Fillo ta takura ne, bayan tafiyarsa suka koma kitchen suka ɗauki na su sannan su ka wuce upstairs.
kamar yanda ya zamar musu jiki yanzu, kuma kowannen su ya saba da hakan, ba wanda ke iya cin abinci shi ɗaya, sai dai su yi feeding junansu, yanzu ma tare suka ci abinci.
su na ci Turaki na zuba santi, ita kuma sai taji tamkar bata taɓa ƙin cin indomie da ƙwai ba saboda yacca take enjoying feeding ɗin nasa.
bayan sun gama ci Fillo ta fita a ɗakin ta wuce nata, shi ma toilet ya shiga bayan fitarta, yay wanka sannan yay alawala ya fito ya wuce masallaci, bai dawo gidan ba sai da akayi sallar isha'i.
ɗakinsa ya wuce direct, shigarsa ya tarar bata nan hakan yasa ya fita ya koma nata ɗakin, nan ɗin ma bata nan, ya murɗa handle ɗin toilet nan ma bata ciki, sai yaji faɗuwar gaba ta kama shi, cikin sauri ya fito sai gata tana hayowa upstairs ɗin.
doguwar ajiyar ya sauke, ya harɗe hannayensa a ƙirji, idonsa akanta yana d