NOVEL SHARES -
duk sai taji duniyar ta ƙara yi mata zafi, taji kaman ta samu wuƙa taje ta ɓurmawa Fillo, gwara ta kasheta kawai ko ta samu ta sami sauƙin raɗaɗin ciwon son Turaki da kishinsa da ke neman hallaka ta.
tana ganin sun miƙe za su tafi zuciyarta ta yanke shawarar zuwa ta bangaje Fillo, ta hankaɗata daidai saitin in da idanuwanta ke hango ma ta garwashin wutar da aka ajiye wanda akewa Boɗejo gashin ƙafa da shi.
without second tought ta baro bakin ƙofar ta taho gadan gadan kamar wacca ake tunkuɗowa. idon Fillo ya ƙara sauka akanta ta cikin mudubin, kamar tasan abin da Ilham ɗin ke shirin yi, tana ganin ta kusa zuwa in da take, da gangan tai saurin wuntsilawa gefe zata faɗi aikuwa a kiɗime Turaki ya tarota yana faɗin Subhanallah.
"Fulani Nah yi a hankali, am sorry kinji, hankalina na kan wannan tsohuwar ne".
ta ɗage ƙafa tana cije fuska tace,"ka daina bani haƙuri ba kai ba ne".
sai ta dafa shoulders ɗinsa ta ɗago tana duban Ilham dake gefe ɗaya tana faman huci tace,"ina yini, ya mai jiki, Allah ya sawwaƙa ya tashi kafaɗunta. kiyi haƙuri ban san za ki wuce ba da ban tsaya a hanya ba".
Ilham taja dogon tsaki na baƙin ciki da takaici, ta bar wajen tana jin zuciyarta kamar zata ƙone.
Turaki ya bi bayanta da mugun kallo, ya dunƙule hannu yana ɗauke idonsa akanta.
"ita ta bige ki?". Fillo ta kalle shi tayi narai-narai da idanu kamar zata yi kuka ta ce,"don't bother your self, mu tafi kawai kaga ran Boɗejo a ɓace yake".
sai ya tallafota jikinsa ya juya ya fuskaci Boɗejo, muryarsa na shaida zallar ɓacin rai yace,"wurinki muka zo ba wajenta ba, a da nake da hurumi da ita amma a yanzu ban da wata alaƙa da ita, ki ja mata kunne karta ƙara gigin illata min Mata ko da kuwa bisa kuskure ne, dan ba zan ɗauka a hakan ba. ina da sauƙin kai but akan wannan jaririyar da ke jikina ina iya rufe ido na manta duk girman alaƙar dake tsakanina da ko wanene in ci zarafinsa, wannan jaririyar tafi min duk wani mutum a duniyar nan bayan mutum uku, domin ta sadaukar da ranta da lafiyarta akaina tun kafin ta san waye ni, ta cusa kanta a haɗarin da ko wanda yake sona ba zai iya ba, saboda haka nake mutuntata, nake martabata, nake darajtata fiye da ƙima, fiye da lissafi duk wani me tunani. zan ɓata da ko waye matuƙar ya nemi ya cutar min da jaririyata, if not zan manta da alaƙa in nuna the bad side of me, hakan kuma babu wanda zai yiwa daɗi".
a hasale Boɗejo tace,"to ai ka rufe mu da duka ni da ita shi ne kawai, mene wani gargaɗinka, gargaɗin banza da zai bi ta iska, ai rama ma ta kawai zaka yi, wato ga Ramla an taɓa ko Zaytuna dole ka nuna baka da mutumci".
ya rufe ido yana ƙara dunƙule hannunsa, Fillo ta riƙe shi ganin kamar yana ƙoƙarin aikata abin da ba zaiwa kowa daɗi ba.
ya buɗe ido yana kallon Boɗejo yana ta huci yace,"kamar yanda Baffa ba zai iya haɗaki da Mum ba, haka ma ni, amma ki sa ni, gwara a taɓa Zaytun akan a taɓa wannan, saboda haka me kiyayewa ya kiyaye, wanda ba zai iya kiyayewa ba kuma ya shiga sata gonar Muhammad Turaki".
yana gama faɗar hakan ya duƙa ya ɗauki Fillo suka fice, tana ta cewa ya sauketa amma yaƙi, hadimai da dakaran gidan sai kallonsu suke yi har suka shiga mota.
ɓangaren Ilham kuwa su na fita ta kalli Boɗejo tana nuna kanta ta ce,"ni yarinyar nan zata haɗawa sharri, ko fa taɓata fa banyi ba Boɗejo, amma ki ga irin maganganun da Hammah yake faɗa, to wallahi ko ban da niyyar komawa gidansa sai na koma, zata gane tayi da ni".
ta miƙe tana barin falon haɗe da yin ƙwafa me girma wacca ita ɗaya ta san ma'anarta.
a hanya Turaki ya tsaya ya sayi kaza da takeaway na mandi rice. tun da suka taho daga shi har Fillo babu wanda yay magana a motar har suka koma gida.
yana yin parking Fillo ta buɗe ƙofa ta fice tai tafiyarta, shi ma kuma ko da ya shiga part ɗin bai bi ta kanta ba ɗakinsa ya wuce, ya sakar ma kansa shower sannan ya kwanta akan gado ya runtse idonsa, tunaninsa guda ɗaya ne, Anya zai dawo da Ilham cikin gidan nan?.
ya daɗe kwance yana lissafi acikin kansa, kafin ya buɗe ido ya sauko akan gadon ya fita, ɗakin Fillo ya shiga, zaune ya ganta akan gado tayi shiru kanta jingina da gadon, ya tsaya yana kallonta kafin ya ƙarasa bakin gadon, yana zuwa ya ɗaukota ya fito da ita zuwa ɗakinsa.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*54*
akan kujera ya zaunar da ita, idanuwan Fillo suka manne akan hannun Turaki da suke cikin plate ɗin abincin da yayo takeaway, abincin da ta san ya siya ne saboda ita, ba don shi yaci ba.
ya ɗebo ya kai bakinta, har yanzu ɓacin ran da ke saman fuskarsa bai gushe ba, idanuwansu ya sarƙe ana juna, ta kaudar da hannun nasa da ke nufar bakinta.
"ban ji daɗin yanda ka yiwa Boɗejo ba".
ya rufe idonsa bai ce komai ba.
"don Allah kar ka ƙara, ko babu komai ita ce fa ta haifi Baffa, tana da girman da bai kamaci ai faɗa ma ta kowacce irin magana ba saboda ɓacin rai".
still idonsa na rufe ya ce,"ba don hukuncin ubangiji ba, sannan ba don ke da taimak