NOVEL SHARES -
a ahaka babu lafiya, suyi aikin da kansu ko kuma su nemi wata".
Kaka ta kwantar da murya tace,"a'a Halima ba haka za'ai ba, kinga aikin nan ma fa ba wata wuya ne da shi ba, daɗewar ma da kika ga ina yi saboda mara lafiyar gidan ne, hatsari yayi me muni yana buƙatar kulawa, zama kawai za kiyi idan yana da buƙatar wani abu kiyi masa, idan dare yayi Hajiyar ta sami zama shikenan sai ki taso kiyi tahowarki...kina gani fa kula da shi kawai aka ƙara yawan albashina ya koma har dubu ɗari".
Fillo ta daɗa ɓata fuska babu alamar zata amince da zuwan tace,"yau ya kula da kansa, gobe naje in Allah ya kaimu".
Ta faɗa tana miƙewa ta fita ta wuce ɗakin Yami, babu kowa a falon su, tana ta sallama ba'a amsa ba. ba tayi mamakin jin shirun Yami ba, wataƙila tana can wurin aiki tana lura da masu yi, tunda ita da Kaka ne manya.
Maijidda kuwa ta san ba zai wuce ta kaɗa yawonta ba, ta ɗaga labulen zata fito sai ga Yami ta dawo. kular abincin dake hannun Yami ta karɓo ta shigo ma ta da ita, gaisawa suka yi ta ke faɗa mata Kaka bata da lafiya.
jin hakan Yami ko zama ba tai ba ta suka fito suka wuce, idanun Kaka na bisa ƙofa suka sameta.
Yami tai mata sannu Fillo kuwa ta shige ɗaki dan ma kar Kaka ta ƙara tada maganar zuwanta cikin gida, tayi shiru a ɗakin tana tunanin dake sakata zubar da hawaye, kiran Yami yasa ta fito.
Yami ce ta lallamata ta yarda da zuwan, kafin ta wuce sai da ta ƙara komawa ɓangaren Yami tace da Maijidda dan Allah ta kula da Kaka bata lafiya, yanzu zata dawo ba jimawa zata yi ba.
A compound ta tsaya ta rasa entrance ɗin da zata nufa, ƙofofi ne suke kallonta na part har guda guɗu, ita bata san ina Kakan ke zuwa ba, ita bama ta taɓa shigowa nan ba, kuma bata ga kowa da zata tambaya ba, kuma ba zata iya zuwa wurin me gadi ta tambaye shi ba.
Ta nan tsaye Khalil yazo ya wuceta, fitarsa kenan ya dawo saboda mantuwar da yayi. yafi minti biyar kafin ya kuma fitowa, ya ƙara wuceta. sai da zai shiga mota sannan hankalinsa ya ba shi kamar fa mutum ya gani tsaye har 2 times.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*9*
Khalil ya kalli me gadi daya buɗe masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo.
Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki".
Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view ɗinta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu.
to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin.
ba tare daya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?".
"a'a ranka ya daɗe, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second ɗaya banyi da shiga ɗaki na ɗakko radio ba na fito, can kuma ina ɗaga kai na hangeta tsaye a wurin".
mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buɗe ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya.
taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba.
To yanzu daya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu.
Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi.
abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba.
"lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta.
Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?".
Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?".
Har yanzu idonta na ƙasa ta bashi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya".
Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?".
ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne".
yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce.
yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buɗe shi kiyi tambaya ba?".
muryarta tayi sanyi yayin faɗin,"ai banga mutane ba ne".
Yay mata wani kallon up and do