NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 269 of 323

ayi yawa". ta jijjiga kanta ba tare da tace da shi ƙala ba. Fillo ta miƙe ta ɗauki manyan ledojin da suka shigo da su guda biyu, taje gaban Boɗejo ta tsuguna ta ajiye, muryarta ta fito very cool da cewa,"ga wannan ba yawa, Allah ya ƙara miki lafiya". ta numfasa, ta ɗora hannunta akan ƙafar Boɗejo, cikin taushin murya tace,"don Allah kiyi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, da ni da shi duk bamu da laifi, zanen ƙaddarar mu ne ya zo a haka, tun kafin zuwanmu duniya ubangiji ya rubuta cewar zamu kasance a inuwa guda ɗaya, Allah ya rubuta hakan a lauhul mahfuz, dan haka ni ko shi ko wani babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya rubuta zai faru, illa kawai mu roƙe shi ya juyar da abinda zuciyoyin mu basa so su zama alkhairi a gare mu, ya kuma saka mana haƙuri da dangana mu karɓi lamarin a yanda yazo mana". tayi ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin ƙwace ma ta. "don Allah don Annabi kiyi haƙuri ki daina fushi da kowa, duk mun san munyi miki laifi, babu wanda yaƙi bin umarninki, babu wanda zai so abin da ba kya so, kawai dai babu yanda zamu yi da lamarin da Allah ya shirya dole zai faru ne. don Allah Boɗejo ki daina fushi da Maama da Mum, haka ki daina fushi da mijinmu". ta ƙarashe maganar su na haɗa ido, sai Boɗejo taji wani abu da bata san menene shi ba ya tsarga ma ta akan Fillo, abu ɗaya ta sa ni kamar yarinyar tana da wani girma na kwarjini wanda ba zaka san da hakan ba zai ka kalli ƙwayar idanuwanta. duk sai taji ta kasa yi ma ta cin mutuncin da tayi niyyar yi ma ta a duk ranar da tayi tozali da ita, alwashi ne da ta ɗauka, so tayi duk ranar da suka yi ido huɗu sai ta yiwa Fillo abin da zai sa ta bar gidan Turaki da ƙafafunta, tayi tafiyar da ba zata taɓa dawowa gare shi ba. idanuwan Fillo suka manne akan mirrow ɗin da ke fuskantarta, murmushi ya suɓuce a saman leɓenta wanda ita kaɗai ta san tayi shi, hatta Turaki dake kallonta ba zai ce tayi ba. Boɗejo ta haɗe rai tana ɗauke hannun Fillo akan ƙafarta ta ce,"Malama ta shi ki bar kusa da ni, kuma ki ɗau tsiyarki, ki kai can ƙauye inda ake yunwa, amma ba nan inda aka fi ƙarfinsa ba". Fillo ta marairaice murya ta ce,"tuba nake ranki ya daɗe, ina barin kusa da ke ne kawai idan har an dubi girman laifin da na aikata an yafe min ba, hakan kaɗai zai sa in sami sukuni da salama. Kaka bata fushi da jikokinta, ko da tayi hutu ne ta ɗauka saboda ta huta da rashin jinsu, ranki ya daɗe namu hutun ya isa haka a tausaya mana". mamaki ya hana Boɗejo cewa komai, ƙaramar yarinya kamar wannan ta iya zaro zancen tsari irin haka, zancen da tana da tabbacin ba har zuciyarta take yi ba, tsabar kissa ne kawai. "ka taso ka dawo nan". muryar Fillon ta fito ta wuce kai tsaye zuwa cikin kunnuwan Turaki, ya rufe bakinsa da ya buɗe yana kallonta tun ɗazu, ta sakar masa wani kyakykyawan murmushi da ya sa shi tasowa babu shiri, sannan nata murmushin ya ƙaru a sanda ta kuma yin tozali da madubin. ya zauna kusa da ita, ya kama hannunta guda yana murzawa, tare da kai hannu ya ɗauki apple dake cikin plate, ya gatsa sannan ya kai bakin Boɗejo ya ce,"Uwar gidana". ta mangare hannun nasa, ta taso masa cikin masifa har sai da Fillo ta ƙanƙame shi saboda tsorata ba tare da ta san tayi hakan ba. shi kuma yay saurin kewayeta da hannunsa yana cewa da Boɗejo,"yi a hankali tsohuwa Baby bata son hayaniya". sai ya ɗan narkar da murya yace,"kin ga kin tsorata min ita ko, haba don Allah Boɗejo wannan wanne irin fushi ne haka da ba'a hucewa, ce nake tun da har yarinyar nan ta riga ta tare shikenan komai ya wuce". ya faɗa yana shafa bayan Fillo, ita kuwa tun da idonta ya ƙara ƙyallawa ya sauka akan mirror ɗin ɗazu sai ta ƙara shigewa jikinsa tana sakin makirin nishin firgici. Boɗejo kuwa zazzaga masifa da zagege da baƙaƙen maganganu kawai take yi, tana ta zagin kafatanin ahalin Fillo, da Hajiya Madina, ran Turaki ya ɓaci sosai yay ƙasa da kansa, ya kasa ko da motsi ƙwaƙwƙwara. tun shigowar su Turaki parlon Ilham ita ma ta shigo ta ɗayar ƙofar, ganinsu yasa tayi turus a wajen, tayi tsaye ba tare da sun san tana wurin ba, ji take yi kamar ta juya, amma sai taji ta ka sa ɗaga ko da ƙaramin yatsanta, jan ƙafarta ma take so tayi but shi ma ta kasa, ji take yi kamar an daskarar da ita ne a wurin. kuma a lokacin da Fillo ta faɗa jikin Turaki sai ji tayi kaman an kunna gobarar wuta a ƙirjinta. duk sai taji ta rasa me yake yi ma ta daɗi acikin ranta, tun da ta baro gidansa bata ƙara ganinsa ba sai a yau, yau ɗin da take ganin kamar an sauya shi, ya ƙara kyau ya ƙara kumari, annurin fuskarsa ya fita daban da asalin yanda ta san shi. sai taji masifar son shi da kishinsa ya ƙara bin sassan jikinta, yau shi ne gabanta da wata mace da ba ita ba, macen da ta san ta fita asali, kyau, nasaba, ilimi kai komai na rayuwa ta san ta fi Fillo. a gaban idonta yake ririta ƙwailar da ta san bata da uban komai bacin kyau irin na ƴaƴan aljanu, har yake rungumeta a jikinsa alhalin ya san a cikin gidan su yake.
🏠