NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 268 of 323

ana, karki tsammaci za ki ambaci sunana da roƙon na yafe miki, karki saka sunana acikin waɗanda zasu yafe miki, Azima ba zan taɓa yafe miki abin da kika min ni da Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji ni da ke, sai Allah yayi mana hisabi. but just keep in mind da bakina dai ba zan taɓa faɗar abin da kika aikata ba, idan Allah ya nufeki da yin magana kafin mutuwarki kya bada labarin zaluncin da kika aikata, duk da bana fatan Allah ya baki aron wannan damar, gwara ki tafi da tarin alhakin mutane ta yanda za ki ɗanɗani abinda kika shuka tun a ƙabari kafin ranar tsayuwa a gaban ubangiji, Azima insha'Allahu har mutuwarki babu me yafe miki abin da kika masa domin ke ɗin azzaluma ce". tana gama faɗar haka ta bar bakin windon tana kuka. hango tahowarta yasa Zaytuna fitowa daga mota tazo ta kama hannunta. Hajiya Madina ta kalleta ta girgiza kai tace,"your excellency". Mum ta ɗaga kai ta kalleta, sai Maama tasa tissue tana goge ma ta hawaye. "don Allah ki daina zubar da hawayenki ga wacca bata kamaci a zubar ma ta da hawaye ba, duk da irin tsananin halin da take ciki, masu imani ake yiwa kuka ba azzalumai irin Azima ba". sai kuma ta numfasa ta ƙara cewa,"in dai ina raye Allah har Azima ta mutu ba za ki ƙara zuwa inda take ba, balle ki dinga zubar da hawaye haka a banza, ba gwara ki tara mana hawayen ba idan abin farin ciki ya same mu ki yi". "na daina ma daga yau, ba zan ƙara ɓarnatar da hawayena ba akanta". "better!, ki godewa Allah da ya saka miki tun daga nan duniya". da sauri Hajiya Ramla ta ɗago tana dubanta da mamaki. Hajiya Madina tayi murmushin da ya tsaya a iyakar leɓenta sannan tace,"ban da masaniyar wanda yay miki asiri kika bar gida, but haka ɗaya nake jin zuciyata ta kasa aminta da Azima, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya amma ni dai ita nake zargi, shiyasa ko kaɗan bana tausaya ma ta, wallah in har itace silar asirinki da na me babban suna da yardar ubangiji sai tayi mutuwar wulaƙanci". tayi shiru tana rufe idonta na sakanni sannan ta buɗe, sai kuma ta juya topic ɗin da cewa,"yanzu me babban suna suka shigo, ba ki gansu ba gwanin sha'awa sunyi kyau sosai, sai naji kamar ni ɗaya nai sa'ar haihuwar ɗa me kyau da kuma dacen balarabiyar sirika". Hajiya Ramla tayi murmushi. "ai ce nake ba za su zo ba, dan ɗan naki yayo halin kafiyarki". "yanzun ma na faɗa musu sannu ce kawai ta kawo su, da zarar sunyi ma ta sannu ko ta amsa ko bata amsa ba suyi tasowarsu su tafi". Hajiya Ramla ta girgiza kanta,"da ba ki ce musu haka ba ai". "hakanne ma yasa na hanasu zuwa wurinki nace su wuce wurin Boɗejon kai tsaye, kana tausayin me tausayinka ne, haka kana mutunta me ganin mutuncinka". ƙafafun Turaki suka shiga cikin parlon kafin na Babyn roba su bi bayansa, ya kama hannun Fillo da ke rakuɓe a bayansa suka shiga ciki. su ka zauna da ga ɗan nesa inda Boɗejo tasa wata hadimarta tayi musu nuni, tun da akace ma ta su ne ta sunkuyar da kanta, har suka zauna kuma ko ɗago kai bata yi ta kalle su ba don bata tunanin iyayensa ma sun isheta kallo balle shi kansa da wata sillan karan matarsa. Fillo ta kalleta taga tamkar bata san da shigowarsu ba, sai taji wani abu me kama da tsoro ya kamata, ta kalli Turaki suka haɗa ido, cikin bin umarnin da yay ma ta da ido ta buɗi baki ta ce,"Boɗejo ina yini, ya sauƙin jiki?, Allah ya ƙara miki lafiya yasa kaffara". ta haɗe duka maganarta a lokaci ɗaya, dan ta san abu ne me kamar wuya Boɗejo ta amsa ma ta, ile kuwa kamar yanda tayi tsammanin uffan ba ta ce ma ta ba. Turaki ya kama hannunta ya riƙe wanda yake jin yana rawa a jikinsa. ransa ya ɓaci sosai, daraja ɗaya Boɗejo zata ci haifar Baffa da tayi, ya rumtse idonsa ya buɗe, ya danne abin da yake ji yana taso masa a zuciya ya ce,"tsohuwa ashe ba kiji daɗi ba, na san ba komai bane sai kewata ko?, to ai gani na zo kuma naga sai wani ciccin magani kike yi, ko ba'a maraba da ganin nawa?". ya faɗa cike da tsokana dake tsakaninsa da Kakar tasa. ta ɗago tayi masa wani kallo me cike da ban haushi ta ce,"munafiki, mara mutunci, wanda ya kunyata ni akan kucakar ƴar aiki, wanda ya fifita mace akan bin umarnin mahaifinsa, kai har kana tunanin muryarka ma ina ƙaunar ji ne, ai tuni na sallamaka acikin jikokina, saboda haka ka bar bin wata hanyar shishshige min, ranar da Amaryarka ta koma ɗakinta wataƙila ma iya shiryawa in akwai rabon hakan". yay murmushi me faɗi har da sauti yace,"ashe zamu shirya ɗin dai, yanzu dai ya jikin naki kin ji sauƙi ko ya?". ta galla masa harara,"ina ruwanka da lafiyata, ka ga tun kamin raina yay mugun ɓaci tashi ka fita ka bar min waje, idan ba haka ba na ƙwala ihu yanzu na ƙalawa wannan ƴar banzar yarinyar sharrin da babu wanda zai iya ƙwatarta duk duniyar nan". fuskar Turaki ta washe da murmushi ya ce,"yo ba tana da Allah ba, shi ai zai ƙwaceta, yanzu dai ban gaji da ganinki ba kya bari in gama kallonki tukunna sai ki kora ni, ke kawai daga yi miki kishiya duk sai bi ki zama fitinanniya, wannan kishin naki y
🏠