NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 267 of 323

a tarwatse ya bi iskar da ta kaɗa tun a ranar da ta sanya ƙafafunta acikin gidan mai martaba. kuma daga lokacin da ta fahimci cewa ba zata taɓa samun Dikko ba, daga lokacin ta ɗauki alwashin ƙuntata rayuwar duk macen da ke rayuwa tare da Dikko hatta kuwa da ƴaƴan da zai haifa ba tare da ita ba. shigowarta cikin rayuwar Mai Martaba ta gane asalin menene mulki da kuma daɗin da yake cikinsa, wannan yasa ta dasa cin burika da yawa a rayuwarta, lokacin shaiɗan ya fara buga ma ta sabuwar ganga acikin kanta, akan aikata mugwayen abubuwan da ba zasu ɓulle ma ta ba, ya dinƙa rinjayar zuciyarta da cewa tayi duk fafutukar da zata yi wajen ganin ta mallaki kaso 70 cikin tarin dukiyar Mai Martaba kafin ta barshi. shiyasa daga lokacin da ta haifi Ilham, sai tabi duk wata hanya da zai sa Mai Martaba ya koma ganin ƴarta kawai a matsayin ita kaɗai ce ƴar da ya mallaka, wannan dalilin yasa ta kama fufutukar bin bokaye kenan, wanda ya zama mafi muhimmanci a wajenta. kuma tayi nasara akan hakan, domin kuwa cikin ƴaƴa goma da Mai Martaba ya mallaka Ilham kaɗai idanuwansa ke iya gani a matsayin wacca ya haifa da cikinsa, wanda hakan ya janyo rabuwar kawuna a tsakanin sauran ƴaƴan da ita Ilham ɗin, domin ya mayar da ita tamkar ɗa namiji, duk wani abu nasa da ya mallaka yana rubuta shi da nata sunan, har ya kan yawan buɗar baki yace _na so ace Ilham Namiji ce, da ta gaji wannan kujerar tawa tun ina raye._ sai dai babu wanda ya taɓa gane Azima na ɗauke da wani mummunan ƙudiri, kasantuwarta mace mai dabara, macen da ta ke lulluɓe da mayafai guda biyu, ciki baƙi waje fari, sai dai ba ta taɓa barin wani mahaluƙi ya ganta da wannan baƙin lulluɓin sai dai farin da ta yafa daga waye. _"har yanzu mun kasa gano taƙaimemen ciwon da ke tare da ita. duk wasu injina da ya kamata muyi amfani da su sun gaza yin aiki wajen gano cutar da ke tare da ita"._ maganar da ɗaya daga cikin likitocin ke yi kenan acikin ofishinsa, acikin asibitin masarautar kaltungo, Mai Martaba ya miƙe cikin mutuwar jiki suka fito tare da Dr ɗin. a sanda suka fito ya tsaya daga can nesa yana kallon matar tasa ta silin hanyar da ta buɗe ta ƙofar ɗakin da take kwace. kallo ɗaya zaka yi mata tun daga nesa kaji zuciyarka ta motsa saboda tausayin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, ka kuma ƙara jin tsoron ruɗin duniya, a yayin da zuciyarka za ta tuna ubangiji da dukkan irin ikon da yake zartarwa akan rayuwar kowanne bawa. kwance take an ɗaureta ajikin gadon ɗakin asibitin da ke cikin masarautar saboda yawan girgiza da take yi yanzu, idanunta a tsaye suke sun ƙafe akan windon ɗakin da ta nan ne kowa ke iya samun damar ganinta, har kuwa da ƴarta guda ɗaya da ayanzu ita ma bata iya zama tare da ita saboda bala'in ɗoyin da take yi wanda kowa ke cutuwa da shi, hatta kashi idan tayi sai ta jima cikin su kafin azo a kula da ita. gaba ɗaya ta gama lalacewa, ta koma ita da ƙwarangwal babu maraba, a halin da ake ciki yanzu, dukkan wani ɓangare na zuciyarta ya riga ya gama dagargajewa a ƙirjinta, tana jin ƙirjinta ne kamar Allah bai taɓa halittar komai a cikinsa ba, zuwa yanzu duniya gaba ɗaya ta gama yi mata zafi, babu abin da take fata sama da mutuwa, sai yanzu ta gane ka zalunci mutum Allah ya baka damar neman yafiyarsa, ko ka saɓawa Allah ka nemi gafararsa tun kafin ya damƙe ka, wata rahama ce babba daga ubangiji, atleast ka iya samun sassauci na daga bala'in da zaka shiga. halin da take ciki a yanzu ta tabbata babu wani abu na awo a duniyar nan da za'a auna ya fitar da kalmar da zata fassara shi, a yanzu ta afka ne cikin wani rami na nadama, nadamar da ta ke kira da mara amfani. ta kuma sa ni har ta mutu Allah ba zai bata damar yin magana ba, balle ta samu ta fayyace mugun abubuwan da ta aikata, balle har ta nemi yafiyar waɗanda ta cuta. ta sa ni wannan kaɗanne daga cikin hukucin da Allah zai yi mata. _(Ya Allah ka kiyashe mu daga sharrin zuciya, ka rabamu da aikata aikin danasani.)_ Hajiya Ramla ta zo tayi tsaye a bakin windon ɗakin Fulani Azima, kallon junansu suke yi, idon Fulani Azima sai hawaye yake zubarwa kamar an kunna famfo, tana ta girgiza kan gadon da take, da alama so take yi ta sauko, kuma so take yi tai magana da Hajiya Ramla, so take yi a bata aron dama ko da guda ɗaya ce, ko da ta minti ɗaya ce. in har Hajiya Ramla tace bata ji tausayinta ba tayi ƙarya, abu ɗaya ne kawai ta san da shi, shi ne ko akwai sama da abin da yafi tausayi ba zata taɓa yafewa Azima ba ko da ace zata shiga halin da yafi wannan muni. ta sauke numfashi tana ƙara kallon Fulani Azima wacca har yanzu idonta ke maƙale akanta tana jijjiga gadon. sai ta saka facemask ta fesa turare sannan ta fuskanci gaba ɗaya windon, tace da ita,"na san kina ta so ki buɗi baki ki nemi yafiyar abin da kika yi min ni da ɗana, kamar yanda kike so ki buɗe baki ki faɗi mugwayen abubuwan da kika aikata. ban da masaniyar ko Allah zai baki aron wannan damar, but ki sani ko da bayan raina kika sami damar mag
🏠