NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 266 of 323

haka zan faɗa". yay murmushi,"wai to duk wannan cin maganin na mene?, ba fa a haka muka fito ba, ko nayi laifi bisa kuskure ne?". tayi narai narai da idanu ta ce,"ni kawai bana son zuwa gidan". "me yasa?". "bana so muje wannan matar ta ganka, na san dole zata kalle ka, na san dole sai taji wani abu akanka". tai maganar kamar zata yi kuka. yay shiru bai ce komai ba, sai da suka yi nisa a tafi sannan ta ƙara cewa,"kuma na san kaima zaka kalleta ko?". nan ma dai bai ce ma ta komai ba, hakan yasa kawai ta kifa kanta a saman gwiwarta tana jin wani bala'in zafi a zuciyarta, idan ta san haka ne da tun farko tace bata da lafiya ba zata iya zuwa ba. *_bari nayi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata da nuna jin daɗi gare ku masoyana, tank you so much lovlies for keeping up with this story, ga shi dai muna ta tafiya amma ko kaɗan baku ƙosa da ni ba, duk da inata ƙoƙarin ganin na yanke labarin an gama shi kwatakwata. Anyway don Allah kuci gaba da bani ƙwarin gwiwa ta hanyar yin warm comments ɗinku da ku ka saba, haɗe da yin voting, mun kusa hattamawa insha'Allah._* *_ina son duk wani makarancin littafin nan tamkar yanda nake son ƴan group ɗina na Halima Hz palace, muaahh to all of you😘😘._* wataƙila a samu sabon update duk dare, amma zai zo babu yawa ne🤕 *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *53* *Azima Tahir Lukman.* ashekarun baya masu yawa da suka shuɗe, Azima Tahir Lukman wata matashiyar budurwa ce, wacce ke matuƙar ji da kanta a ɓangaren kyau, ilimi da kuma dukiya ta mahaifiyarta wadda ta kasance ƴar siyasa. kyau irin na Azima ke tasirantuwa a zuciyoyin maza da dama, daga masu kuɗin har talakawa, a inda ta ware manyan masu kuɗi da masu mulki waɗanda su ne take ganin su kaɗai ne suka isa su mallaketa. kuma a kaf mazan da tayi mu'amala da su babu guda ɗaya aciki da zuciyarta ke jin tana so ko kuma zata iya aurensa, no; zata mu'amalanceka ne kawai domin kuɗin da suke aljihunka, da zarar ta gama da kai shikenan, saboda ta mallaki kuɗi a wurin irin alahazawan da ke zuwa wurinta ta kashe rai ba ɗaya ba, ba biyu ba. zuciyar Azima ta so mutum guda tallin tal ne a rayuwarta, wato Alƙali Habib Dikko, shi kaɗai zuciyarta ta so tsakani da Allah, wanda har take jin she can go to the extend akan taga ta mallake shi, alhalin kuma yana matsayin saurayi ne na aminiyarta da ta san cewa an saka musu rana. Ramla Muhammad Turaki itace babbar aminiyarta da suka yi university tare anan london, duk wanda yasan Azima ya san Ramla, haka duk wanda ya san Ramla yasan Azima, su kwana tare su tashi tare, su ci abinci tare su yi yawo tare, haka zalika ba sa taɓa aiwatar da abu sai da shawarar juna. Azima ta samu Ramla ne tare da Dikko, tare ta gansu, wanda shi ma kuma ya aminta da ita sosai, musamman da yaga Ramla ta ɗauki duk wata yarda da amana ta bawa Azima. sai dai daga lokacin da Dikko ya fara shirin kai lefen Ramla, a lokacin Azima ta fara kunno wutar gobarar da zata lalata lamarin auren, ta fara ɓata Ramla a wurinsa, abubuwa iri iri da zai sa yaji ya tsani Ramla babu wanda ba ta faɗa masa ba, tun baya yarda har ya zo ya fara yarda da ita, saboda sauyin da yake gani a tare da Ramla a lokacin da bata ba shi attension ɗinta, sakamakon final exams da za su fara. hatta vedion tsiraici na lesbian Azima ta ɗauka ta bayar anyi editing ɗinsa da fuskar Ramla ta bawa Dikko, daga wannan lokacin kuma yaji ya tsani Ramla kwatakwata, ita kuwa Ramla a lokacin bata kawo komai a ranta ba dangane da watsi da lamarinta da Dikko yay, ta ta'allaƙa hakan ne da space ya bata saboda ta samu tayi karatun exams sosai. sai dai kuma a lokacin da Azima take tunanin tayi nasara, a lokacin Allah ya toni asirinta a ranar wata laraba, inda wanda yay ma ta editing vedion tsiraicin Ramla yaje ya sami Dikko ya faɗa masa gaskiyar komai, a lokacin soyayya ta riga tayi nisa tsakanin Dikko da Azima, dan saura ƙiris su shigar da iyaye cikin maganar, dan Azima ta gama tsara yacca zata shimfiɗar rayuwar aurenta da shi. kuma duk wannan lamari da ke faruwa Ramla bata da labarin komai, yacca Azima ba ta bari ta fahimci wani abu ta ɓangarenta ba, haka shi ma Dikko bai taɓa tunkarar Ramla da irin abubuwan da Azima tayi akanta ba har kawo iyau da take matarsa, uwar gidansa, kuma uwar ƴaƴansa, wucewar shekaru sama da 20. lissafi ɗaya Azima tayi a bayan da Dikko ya juya ma ta bayansa, shi ne ba zata taɓa yin nisa daga gare shi ba, zata bi wata hanyar da zata kusance shi har ta wanke laifinta, kuma har ya yafe ma ta yace zai aureta kamar dai yanda taci burin hakan. dalilin da yasa ta shiga rayuwar Mai Martaba Hashim Latif kenan, saboda ta lissafa cewa ta wannan hanyar kaɗai zata iya samun damar kusantar Dikko, ta hakan ne ba zasu yi nisa da junansu ba, ta hakanne zata samu damar wanke laifinta gare shi, in ya so a sanda yace ya yafe mata sai tayi duk iyakar ƙoƙarin da zata yi ta raba aurenta da Mai Martaba domin ta mallaki Dikko, amma sai dai me!, lissafin da hasashenta duk sai y
🏠