NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 265 of 323

arta ta nutsu sannan ya a hankali laɓɓansa su ka sauka akan cheeks ɗinta. sannan ya shiga tambayarta me yasa bata shirya ba, Mum na ta yi masa waya tun ɗa zu, idan ba su je yau ba za'a sami matsala. ta ce,"ni ban san kayan da zan saka ba ai". a lokacin taji sautin murmushinsa kafin ya saketa, closet yaje ya zuge ya buɗe ɓangaren da abayas suke jere a jikin hanger, ya ɗauko wata orange colour da tasha uban adon stones a jiki. "na ɗi son abaya akan atamfa ko less". ya faɗa yana ajiyewa akan gadon sannan ya kamo hannunta ya kaita gaban dressing mirro ya zaunar da ita kan stool, da kansa ya ɗauka body lotion ya shafa ma ta, ita dai kallonsa kawai take ta cikin madubin, kamar ba asalin Turakin da ta sani ba, ya ɗauka powder ya rambaɗa ma ta, taita dariya, ganin zai mayar da ita dodanniya tai saurin karɓar form ɗin ta gyara powdern. ba ta yarda ya saka mata brezier ba kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi, ta karɓa ta shiga toiler ta saka da kanta, tana fitowa ta tarar baya nan, sai ta ɗauki rigar ta saka, abayar ta ƙara haska fatar jikinta da tayi fresh, tayi rolling mayafinta, sai ta zama kamar balarabiya, kamar ba wannan Fillon da ke yawo cikin tsumman kaya ba shekarun baya da suka wuce, wannan wata Fillo ce ta daban, wacce ake rainonta cikin so da kulawa, wacca ake nuna ma ta babu wata tamkarta, wacca ta shigo cikin sahun masu ji da ado da ƙwalisa. ta ɗauko ƙaramar jaka kalar kayan, duk sai taji ta ƙosa Turaki ya dawo ya ganta, tana tsaye tana ta kallon kanta a madubi, tana tunanin duk ranar da akace ta ƙara kumari kuma ya zata dawo kenan saboda tsabar kyau?, sai ta tuna irin wankan da Raudha ke yi a saudiya idan zasu fita, tafiya tayi ta ɗauko wani box ta buɗe ta ɗauko glass ta saka. tana shirin fita yay daidai ta buɗewar Turaki ya sanyo kai, turus yay ya tsaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa, laɓɓanta suka tsuke fuskarta na bayyanta murmushin jin daɗi. tana jiran kalman yabawa su fito daga bakinsa sai taji yace,"ina za ki a hakan?". ya faɗa annurin fuskarsa na ɗaukewa, bai bari tayi magana ba ya wuceta ya shiga ciki, binsa tayi da kallo taga ya ɗauko hijabi, babu shiri ta juya zata fita yay saurin damƙo hannunta. "babu abin da za ki fita a haka, da igiyoyin nawa uku reras akanki za ki fita a haka saboda an faɗa miki bana kishinki?". "to mene a wannan shigar?". "abubuwa da yawa kuwa da zasu ja hankalin wani ɗan banzan a kanki, ko ba kiga yanda kika yi kyau ba ne?". ta juya idanu tare da yin fari tana cewa,"ai baka ce nayi kyan ba". ya ce,"idan nace zan tsaya faɗa miki yacca kika yi kyau ba zamu samu damar fitar nan ba, dan duk lokacin za su tafi ne ba tare da na gama fayyace miki irin kyan da kika yi ba. oya ta ina zan zan cire wannan pin ɗin?". ta marairaice da cewa,"please ka bar ni a haka, wa ye ma zai ganni to bayan a mota zamu je?". sai kuma ta ɓata rai tana cewa,"wai ma ba gidan su me wancan part ɗin za mu ba?". ya kalleta yaga yanda ta wani ci kunu tamkar ba ita ba, yace,"can zamu sai aka yi ƙaƙa?, sai aka ce a gidan su babu maza ko babu masu idanu?". ta ɗan murguɗa baki,"sai ba zan dankama hijab naje gidansu ba tayi tunanin ni ƴar ƙauye ce wadda bata waye ba, ka sa aita gulmana idan mun baro gidan". "su waye za su yi gulman naki?". "ko ba tayi ita da muƙarrabanta ba za tayi ita da zuciyarta, don Allah ka barni in je a haka kar ta raina ni". dariya ta ba shi, but sai ya gimtse yana ɓata nasa ran shi ma, ta durƙusa tayi pleading hannayenta tana yi masa magiyar ita ya barta ta tafi a haka, a ƙarshe dole ya haƙura ya barta, sai dai bai yarda tasa glass ɗin ba ya zare shi yay jifa da shi, ya kama hannunta su ka koma ɗakinsa ya ɗauko facemask ya saka ma ta. "kuma saura idan munje in ga kin wage baki kina dariya ko murmushi...". tun bai ƙarasa faɗar abin da zai ce ba tace,"yanda zata ji daɗin cewa zaman ƙunci nake yi da kai ba, ni dai kawai babu ruwanka da ni ka bini da ido kawai". ya buɗe. baki da mamaki fal yana cewa,"when?, where?, how?, duk a yaushe kika yi baki har kike magana haka?". ta turo baki gaba, ta ƙwace hannunta ta ɗauko baƙin glass ɗinsa ta saka masa,"yana yi maka kyau sosai idan ka saka, amma ni ɗaya zaka ke sakawa, promise". ya karyar da wuya,"i promise you". hannunsa ta riƙe suka fita, tunda suka hau saman titi kuma duk sai ta koma masa kamar ba wannan ƴar Babyn ba sarkin daru da rigima, wacce ta ke hawar masa bori ya zauna zaman lallashi, wannan wa ta Fulani ta daban ya ɗauko, me faɗa kamar yaƙi, da kuma ba da instructions. ta dage tana faɗa masa in sunje gidan bata yarda ya kalli kowa ba, bata yarda yay magana sama da sau biyar ba, bata yarda ya amsa gaisuwar kowa ba, bata yarda ya cire glass aga hasken idonsa ba. shi ma ya tamke murya yace,"duk da wa kike?". "da Muhammad Turaki". ya saki hannunta ya ɗalli bakinta, ta ɗauke idonta da ga barin kallon titi ta juyo ta kalle shi. "to ba sunanka ba ne?". "a bakin mutane ba, amma ban da naki". "to ni
🏠