NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 264 of 323

iyu, Abbansa yazo dukansa ya ɗafe wuyansa yaƙi sakinsa. watarana sun tashi a school yasa driver ya wuce da shi gidan su Bello, ya koya masa duk kalar yanda zai tseratar da kansa, wata rana kuwa yaywa Granny laifi zata kullesa a ɗakinta yay sufa yabi ta ƙarƙashinta, garin kamo shi ta zame ta faɗi, Anty Sa'adah ta kama shi ta murɗe masa kunne har sai da ya saki fitsari a wando. yay shiru yace,"kin san Bello har cewa yay inyi kashi a fo sai in dangwala in rubuta sunana ajikin bangon ɗakin Baffa, in dai yake ni to baya so na...ai ko in faɗa miki ina yin haka washegari Baffa ya kaini Europe wurin Granny". Fillo ta dinƙa dariya har da riƙe ciki, shi ma ya shiga tayata dariyar kamar yanda take yi. ta kama hannunsa ta ɗora a saman ƙirjinta tana rufe ido, yayinda dariyarta ke juyewa zuwa sanyayyan murmushi, a yanzu ta ƙara yarda cewa Turaki yana sonta har cikin zuciyarsa, kuma ba ta tunanin akwai abinda zai canja hakan, tana ganin zallar soyayyarta fal a cikin idanunsa a duk sanda ya kalleta, duk da har yanzu da bakinsa zuwa kunnenta dai bai furta ma ta kalmar i love you ba tun bacin wadda ta gani a takarda. acikin kwanaki ukun nan kacal tana cikin wata duniya ne ta daban me cike tarin kulawarsa da tarairayarsa, ta daina jin tsoronsa dan ya bi ya kulle duk wata hanyar tsoronsa a gareta, ta saba da shi yanzu fiye da tunanin kanta ma, ta saba da hirarsa da yake cikin yi ma ta ko da yana cikin aiki ne, kamar yanda ta saba da jikinsa, dan duk wani motsi nasa cikin taɓata yake yi, ko akan laptop yake to hannunsa ɗaya na cikin nata, ko kuma ya ɗorata ajikinsa yay aikin a haka, haka in bacci ne tana manne a jikinsa. kuma yanzu duk ta san abubuwan da yake so da wanda baya so, dan a kwanaki ukun nan duk ya lissafa ma ta halinsa, ya faɗa ko mai da yake so ta dinƙa yi masa, kuma sai a yanzu ta fahimci ashe shi mutum ne me sauƙin kai in har ka fahimce shi. bayan sallar la'asar Fillo na zaune ita ɗaya a ɗaƙin Turaki, wayarsa ce riƙe a hannunta tana game, ta ajiye wayar tana ɓata fuska, Tunda Turaki ya fita masallaci bai dawo ba, wai Baffa yayi baƙi daga ƙauye sun zo ba su sameshi ba, shi ne yace yaje ya kula da su, gaba ɗaya bai fi minti goma sha biyar da fitar ba, amma duk sai take jin babu daɗi, ta san dai akwai ƴan aiki amma gidan duk sai taji yay ma ta girma, ba ta san ta saba da shi ba har haka ba, ji tai tana kewarsa sosai kamar tun safe ya fita ya barta, abu ɗaya kawai ta sani ba zata ji daidai ba har sai ya dawo. tun ɗazu tayi wanka but ta kasa shiryawa, so take sai yazo yayi mata choosing kayan da zata saka, cikin kwana ukun nan duk shi ke zaɓa ma ta kayan da take sawa, and ta lura ya fi son ƙanan kaya, amma yanzu fita za su yi, ba ta san waɗanda zai so ta saka ba a yayin da fitarsu za ta zama karo na farko. ta ɗau wayar tana jin kamar ta kira shi, sai dai bata so ta dame shi, duk da bai faɗa mata ba tasan shi ma hankalinsa na kanta. miƙewa tayi ta koma ɗakinta, ta buɗe wadrobe ta watso da duka kayan ciki, ta kama ƙugu ta tsaya tana ƙare musu kallo. ta ɗauki wata blue ɗin atamfa, tsaye tayi a gaban full body mirrow tana kara atamfar a jikinta tana kallon kanta, ta ƙara haske sosai alamun jin daɗi na ratsata, kuma idan tasa atamfar ma zata yi ma ta kyau sosai, sai tasa hannunta a kumatunta tana taɓawa, sai taga kamar ƙashin wajen ya fara komawa nama yana son cika wajen. a lokacin taji ƙarar buɗe ƙofa, tana juyawa idanuwanta suka sauka akan Turaki da ke gyara zaman hula a saman lallausan gashin kansa, fuskarsa ɗauke da wannan murmushin da yake tafiyar da tunaninta, baƙin boyel ne acikinsa ɗinki boda, yayi kyau sosai, sai taji kamar ta ɗauke shi ta kaishi can ƙuryar zuciyarta ta adana, ta yanda babu wani da zai dinƙa ganinsa, sai ita ɗaya tallin tal. Turaki ya gama gyara zaman hular tasa, ya ɗago ya kalleta, ya furta ya Ilahi a sanda ya lura da ƙwayar idonta. ya ƙaraso ciki da sauri, ya tsaya a dab da ita yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa biyu. "Fulani nah me ya faru?, me ya same ki?, me ya taɓa ki?". yayi tambayar duk a lokaci ɗaya, me shirin kaɗan kawai sai ta sa masa kukan shagwaɓa, cikin sheshsheƙar kuka tace,"ba kai ba ne ka tafi ka barni ni ɗaya, gidan duk babu daɗi yay min girma". "shhh...". yasa hannu yana goge ma ta hawayen a hankali, ita kuma tana ƙara narkewa da shagwaɓe masa. duk sai yaji zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya san tunda ya sabar ma ta da zama tare da shi yanzu dole ba zata ji daɗin zama ba idan ba ya nan. "i'm sorry Fulani Nah, ban san zan jima har haka ba da ban fita ba sai in aika Sameer kawai, sai da naje naga ashe wai wata gona za'a ba su, kuma ba su faɗa min ba har sai da na dawo gida na duba takardar gonar a cikin takardun Baffa, ina ta sauri but kin san lamari irin haka dole yana ɗaukan lokaci". ya faɗa yana sa hannunsa a bayanta yana zagaye ɗan ƙaramin ƙugunta da shi, sannan a hankali ya ƙara raɗa ma ta,"am sorry, kin haƙura?". har sai da ya tabbatar zuciy
🏠