sai gobe".
ya amsa ma ta da to sannan suka yi sallama.
ya kalli Fillo wacca ta fara lumshe ido akan cinyarsa yace,"Fulani nah ba kya gajiya da bacci ne?".
ta ce,"naji kana waya ne".
"to tashi muyi hira, bana son wannan yawan baccin idan ina nan, if na fita sai kiyi ta baccinki".
ta miƙe zaune ya sarƙe yatsunsu yana cewa,"after la'asar zamu je duba Boɗejo, wai bata da lafiya".
ta ce,"Allah sarki, me yake damunta?".
"ban sani ba nima, kin san jikin tsufa".
ta ce,"to Allah ya bata lafiya".
kwanto ta yayi jikinsa yana janye wani silin gashi da ya hau saman leɓenta yana ƙoƙarin shiga bakinta. ta buɗe lumsassun idanuwanta da bacci ya fara cika su ta kalle shi, ƙwayar idonsa ya maƙale akan plumpy lips ɗinta, ya ɗora yatsansa a saman lips ɗin ya shafa, numfashin bakinsa da ya fito ya haɗe da tambayar da ya jefa ma ta.
"wanne irin alawa kike sha?".
"da ina shan kowanne".
"yanzu fa?".
"guda ɗaya nake so, ibon".
"ɗan naira goman?".
"yes ɗan goman, flavour ɗinta yana min daɗi sosai".
"kaman flavours ɗin ta yana da yawa ko?".
ta ɗaga kanta,"diffrent flavours, but na fi son pink one ɗin me ƙamshin strawberry".
"tana sa ƙamshin baki ne?".
ta buɗe hannayenta alamun itama bata sa ni ba, sai yay murmushi me faɗi bai ce komai ba, sai ta gyara zaman kanta a cinyarsa ta fuskance shi, ta kalli yanda yatsansa ɗaya ke nannaɗo jelar gashinta wanda ta fahimci yana son taɓa gashinta.
tace,"kayi shiru?, ko alawan bai da daɗi?, ko in daina sha?".
sai tayi shiru tana jin babu daɗi, zuciyarta na faɗa ma ta ko teste ɗin bakinta yaji babu daɗi shiyasa yay ma ta wannan tambayar, lura da sauyawan mood ɗin nata yasa shi tambayarta,"what?".
tasa hannu ta rufe idonta sannan tace,"ya sa bakina babu daɗi ne?".
"me ɗin?". ya tambaya.
"alawan mana, na sha yanzu da safe ai".
yay murmushi, ya lura jikinta har yay sanyi, sai ya ɗago da fuskarta yana sunkuyo da tasa halfway da lips ɗinta, sai yaga ta rufe ido gaba ɗaya, cikin sexy voice ɗinsa yace,"ni ba teste ɗin ibon nake so ba, teste ɗin ki kawai nake so, ina so duk sanda nayi kissing ɗinki to teste only you not ibon".
idanunta a rufe tayi murmushi kawai, nan moment ɗin nasu yaci gaba da yi musu daɗi, musamman a ɓangaren Fillo, hirarsa yake ma ta me cike da tarin tambayoyi kala-kala, da suka haɗa duk detail na rayuwarta, tun daga yarinta har girmanta, abin da yake ɓata ma ta rai da wanda ke sakata a farin ciki, films ɗin da take so da wanda bata so, her favorite food and drinks, wuraren da ta taɓa zuwa a rayuwarta, da kuma places ɗin da take da mafarkin zuwa, ta yanda akai ta fara taimakonsa and so on.
ita kanta ba zata iya tuna rana na ƙarshe da tayi magana mai yawan ta yau ba, ko murmushi tayi sai ya tambayi dalilin yinsa kuma sai ta ba shi amsa in ba haka ba yay ta ma ta cakulkuli.
ƙarshen tambayoyin suka tsaya akansa, tana tambayarsa yaushe ya fara sonta?. sai yasa hannu ya rufe bakinta da cewa,"turn ɗinki ba yanzu ba, sai watarana, har yanzu ban gama nawa tambayan ba".
tayi murmushi tana kama hannunsa ta ɗora saman chest ɗinta, ta ce da shi,"to a bar sauran tambayan sai zuwa gobe, yanzu ka ban labarin ƙiriniyan da ka yi da kana yaro".
yay guntuwar dariya, ya fara bata labarin sokancin da yay sanda yana ƙarami, but daga lokacin da ya haɗu da best friend ɗinsa Bello shikenan ya zama sai adu'a.
yana faɗa ma ta lokacin yana ɗan ƙarami ba shi da ƙarfi, wani class mate ɗinsa ya kama shi zai zane shi after an tashi a school, ya kasa ƙwatar kansa sai Bello ne ya zo ya tare masa, da ma akwai shi da siyan faɗan da ba nasa ba, har kuɗi yake bayarwa ya siya faɗa, akan siyan faɗa har abincinsa break ɗinsa yana bayarwa.
shikenan daga ranar su ka ƙulla abota da Bello, kuma daga ranar shi ma ya zama me ƙarfi ya ko yi faɗa da ƙiriniya, sai da ta kai ta kawo ya koma kamar wanda ke aiki da battery, kuma duk saboda zama da Bello, Maama tayi ta tofa masa lahaula.
duk friday Bello a gidansu yake yini, kuma shi Bello babu abinda ya iya sai shegiyar fitina da dambe, sai suje can field Bello yay ta koya masa yanda zai ƙwaci kansa in wani yafi ƙarfinsa, har ranar ya gwada masa yanda zai shaƙe wuyan mutum, Bello ya shaƙe masa wuya har sai da numfashinsa ya kusa ɗaukewa, kuma kamar wani Malaminsa ko Babansa Bello yace yaje yay ta practical, tun da yana da ƙanne yay ta gwadawa akansu, ai kuwa da daddare ya shaƙi wuyan Khalil zai yi assignment ɗin da Bello ya ba shi, Baffa kuwa ya tarfa shi yay masa ɗan banzan duka ya kulle shi a store, aciki ma ya kwana dan sai da safe Maama ta sato key ta buɗe shi, kuma a washe garin da suka haɗu a islamiyya ya faɗawa Bello, sai yace zai koya masa yanda ake ɓalle ƙofa in an kulle mutum, ko kuma da an kaishi ɗaki za'a kulle ya fice a sukwance tun kafin a rufe, har haura katanga duk tsayinta sai da Bello ya koya masa, da yacca zai ɗauko key ɗin mota ya fice daga gidan, har yana ba shi labarin wai shi a gidansu sai da ya fasa glass ɗin mota har b