NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 262 of 323

should wait till tomorrow". Sun ɗau kusan minti goma suna tattaunawa kafin Turaki ya kashe wayar. "Turaki menene?". Fillo ta tambaya bayan ya ajiye wayar, ganin yayi looking so worried. yaja hancinta har sai da tayi ƙara yace,"Turaki ba, shi ne sunana a bakinki ko?". "to ai haka ne sunan naka". ta ƙara cewa,"har yanzu ba'ai settling matsalan ba?". ya shafo fuskarta,"an kusa insha'Allah". "to kaje office ɗin ma na". "kin fi office buƙatata". tace,"to kar Bello ya faɗawa Baffa fa". "rabu da shi ba zai iya faɗa ba, ko ya faɗa zan cewa Baffa ke kika hanani fita". ta ɗago da idonta ta kalle shi, tsinin hancinsa ya sauka a gefen nata sannan numfashinsu suka haɗe waje ɗaya. ya sa hancinsa yayi grazing akan na ta, sai taji da ma su tsaya a haka, a hankali yace da ita,"yunwa nake ji". "to ai Adda Zaytuna ba ta kawo ba". "na kirata ba ta da lafiya, and idan na cewa Maama akawo abinci za tayi ta min tambaya ne har taga ko kamar muna faɗa ne". "Allah sarki, shikenan yau baka da cin abinci". sai ya marairaice ya kamo hannayenta ya ce,"ba zan iya zama da yunwa ba". "to ai ƴan aiki yanzu sun cinye abincin". yay ma ta wani kallo,"ni zan ci abincin ƴan aiki?, oya miƙe kije ki sama min abin da zanci". tana ƙunshe dariya ta ce,"sai ka roƙe ni, ka ce don Allah Fulani nah". ya lanƙwasar da kansa, ya karkata kansa dab da kunnenta, ya sauke muryasa can ƙasa sosai yace. "Dan Allah Fulani Nah". sai kuma ya ɗauka cup ɗin da ta gama shan kunu ya miƙa ma ta yana faɗin,"wa yidi, sadaƙa, iya ko gaya ne ba miya, iya ko ɗan ƙanzo ne, iya ko ɗan ya ya ne, iya nayi barar ban samu ba, don Allah iya ki taimaka". Fillo ta ƙyalƙyale da dariya, tana jin daɗi da nishaɗi na ratsata, tana jin daɗin na mamaye kowanne lungu da saƙo na cikin kanta, ta zame daga jikinsa tana faɗin,"close your eyes, kar ka buɗe har sai na dawo". yay knodding ma ta kansa kawai a yayin da ya rufe, yana rufewa ta miƙe taje ta ɗauko breakfast ɗin da ta haɗa ta ajiye, ta zuba iyakar wanda ta san zai ci sannan tace ya buɗe idon, da ma tuni ƙamshi ya doki hancinsa tun kamin ya buɗe, ya sauke idonsa akan plate ɗin da ke ɗauke da cake ɗin, ya kalleta with suprise on his face yace,"wow who make this delicious?". "am the one, kana ta bacci naje kitchen". ta faɗa tana saka fork ta gutsura ta kai bakinsa, aroma ɗin na sauka akan harshensa ya lumshe ido, kafin ya buɗe tasa masa mug ɗin dake ɗauke da herbal tea a bakinsa, ya kurɓa ya kuma lumshe ido saboda tsabar daɗi. bai san da gaske yake jin yunwar ba sai a yanzu da yaji wannan abin me ɗan banzan daɗi, ko da yake ta ce ma ta yana jin yunwa, yana so ne ta fara shiga kitchen yau dan ya hutar da Zaytuna, ashe already ma ta haɗa masa lafiyayyan breakfast ɗin da bai yi tsammani ba. sai ganinsa tayi ya sauko ƙasa ya tankwashe ƙafafu yana faɗin,"zan iya faɗowa daga kan kujeran". "saboda?". "ni dai dawo nan". ta sauko akan kujerar ta zauna kamar yanda ya zauna, ta dinƙa ba shi yana karɓa kamar ƙanƙanen yaro, yana ta zuba ma ta santi ita kuma sai dariya take yi, har da ɗauko pillow tayi masa kariya wai kar ya faɗa gefe, sai faɗa ma ta yake yi wai tunda yake bai taɓa cin wani abu me daɗin wannan ba, ko wanda Zaytuna ke girkawa ma babu daɗi, ita ba ta saka sugar yaji kuma taste ɗinsa ma kaman abincin ƴan koyo, zai bata shawara idan sun tashi aure ta zo ta koya. Fillo ta dinƙa dariya tana cewa sai ta faɗawa Zaytun ɗin. duk da ita ta ƙoshi sai da ya ƙara bata ita ma taci, wai wancan ba abinci taci ba ai, ya kama complain ɗin an kawo ma ta jagwalgwalo ita kuma saboda kwaɗayi ta kama ci. da rana suna zaune su na kallon pixx na ranar dinner kiran Mum ya shigo wayarsa, yana ɗagawa bayan sun gaisa tace masa,"gobe idan Allah ya kaimu zamu je taraba, Yaya Naja tayi accident zamu je dubata, so sai ku shirya har da ku zamu tafi, but ita Halima zata zauna tare da mu ne, zamu yi 7days acan". kaman wanda yaji mugun abu ya zabura wajen tambayarta,"Mum har ita za'a yi 7days ɗin?" Mum ta ce,"bayanin da nayi ne baka gane ba ko me?, nace maka har kai zamu tafi but zaka dawo ita zaka barmu tare da ita, nima ina so na shiga wurin families so duk zamu je da ita taga ƴan'uwa". yanayin Fuskar Turaki ya sauya, sam bai ji daɗin hakan ba, yay shiru kamar ba zai amsa ba sai kuma yace,"to Mum, by what time zaku tafi ɗin?". ta ce,"da sassafe mana, za'a fita da ita india ne aikin ƙashi za'ai ma ta, so ina so na samesu kafin tafiyan na su". "to Mum, mu zamu bi flight ne". ta ce,"duk yanda kayi. and ku shirya anjima kuje ku duba Boɗejo, bata ji daɗi ba ashe har kwana biyu". ya ce,"gobe kafin mu tafi ba sai muje". "anjima nace Babana, ko so kake ka jawo mana magana, da ma kowa yaje tana faɗa masa mun san bata da lafiya amma bamu je dubata ba, alhalin ba'a sanar mana ba, ka san Baffanku ba ya nan. to bana son fitina ka shirya kuje anjima mu ma yanzu can zamu wuce, ina nan ina fama da Madam, itama wai sai dai a bari
🏠