i yay saurin dakatar da ita daga shafa masa magani da ta ke yi.
"aure ma zaka yi, ka wartsake kaje ka nemo matar aure ka kawo mana, cikin ƙaramin lokaci ba da daɗewa ba, abun yayi yawa ace kamarka baka da aure, ga mata ds yawa nan a dangi, Allah dai ya baka lafiya".
Shirun Boɗejon ya haɗe da walƙiyar wani haske a idon Hajiya Madina, hoton abubuwa da dama suka bayyana acikin hasken. Ta san dai tayi ƙasa da idonta, amma bata san lokacin da murfin idonta ya rufe ya buɗe ba, wucewar sakan 1,2,3, wani abu da ita kaɗai ta barwa kanta sa ni ya dira a tsakiyar zuciyarta.
Da daddare Baffa yana dawowa Boɗejo ta same shi da kanta a ɓangarensa, tace zuwa tayi ta faɗa masa Muhammadu ya bar zuwa aikin da yake yi acan Habuja, Baffa da yaso yayi ƙoƙarin fahimtar da ita akan hakan ma dake faruwa da shi hanya ce ta matakin nasara a rayuwa, kuma ai mutanen ba zasu taɓa samun nasara ba tunda Allah na tare da mai gaskiya a ko yaushe. tace ita dai indai ta isa Muhammadu ya daina zuwa aikin can tunda ba aljanna ake rabawa a wurin aikin ba.
****
*8:00am.*
Fillo na zaune a uwar ɗaki da ƙur'ani a hannunta tana karatun suratul yasin, taji daɗin jikinta sosai tun aduar da Amir yay ma wancan ranar, daya je gida haka ya jido mata ruwan adu'oi daga wurin mahaifinsa ya kawo mata, ruwan adu'ar da suka zama na shanta yanzu, shi yasa yanzu sumul ƙalau ta ke jinta kamar bata yi wani ciwo ba.
ta rufe qur'anin a sanda ta kai ƙarshen sura, ta tashi ta koma kan katifarsu ta kwanta, idonta na kallon rufin ɗakin.
tasa hannu tana shafa kusa da ita wurin kwanciyar Kaka, ji kawai tayi ruwan hawaye ya cika idanuwanta ba tare da ta san da zuwansu ba.
tun ƙarfe shida da rabi Kakan ta fita aiki cikin gida, ita ba wai fitar sassafen bace ke damunta, tunda a nan ɓangaren ma ƙarfe shida suke fita, to amma ai anan tana ganin gimlawarta da jin muryarta, amma can idan ta tafi sai dare zata ƙara ganinta.
Yunƙurawa tayi ta tashi ta nufi jakar kayanta ta zuge zip ɗin, sai kawai ta zubawa kayan ido, bata san wanne zata saka ba dan yau Kaka ta manta bata ɗauko mata wanda zata saka ba. Kamar zata yi kuka ta shiga ɗebo kayan tana fito da su, kayan duk sun tsufa da yawa, kwana biyu Amir bai yi mata ɗinki ba kasancewar bashi da kuɗi, kullum haƙuri yake bata.
Atamfar ta ɗaya ce me kyan gani ta sallah ƙarama daya ɗinka mata, kuma da so take sai babbar sallah zata kuma sakata.
har tayi choosing wata atamfarta leda sai ta tuna da cewar Amir yace zai zo anjima shi da abokinsa. dan haka sai ta ajiyeta ta ɗauko me sabuntar full cotton ta saka.
Ɗinkin riga da skirt ne, ya zauna ɗas ajikinta, rigar ta kwanta a shafaffen cikinta, breastcuff ɗinma yay dai-dai da breast ɗinta maidaidaita, ƙafar nan tata ƴar sirit acikin skirt ɗin.
kayan ta maida ta ɗauki ɗankwalin ta fita, wurin Maijidda zata je tayi mata ɗauri irin wanda ta taɓa yi mata Amir yay ta santinsa.
don ita ba iya ɗaurin ɗankwali tayi ba, tafi gane ta saka hula akanta.
Tana fitowa saukai kiciɓis da Kaka ta dawo, da mamaki ta ke kallon Kakan, wadda kana gani kasan cikin ƙarfin hali take.
Saurin riƙeta tayi suka shigo ciki, Kaka ta zauna ta riƙe kanta da taji yana sara mata sosai.
"sannu Kaka, ni dama tun jiya nake cewa ba kya jin daɗi kika dage min ke lafiya kike".
Fillo tayi maganar kukan dake bakinta na shirin fitowa.
Kaka tace,"ni ƙalau nake...ciwon kai ne kawai, kuma ina shan magani zai daina".
Cikin sauri Fillo ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko panadol da ruwan adu'a da take sha ta kawowa Kakan. Kaka ta karɓa tasha sannan ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci.
Fillo dai kallonta kawai take yi, tsoro da fargaba fal ranta, idan mutuwa tayi mata haka ya zata yi?, ina zata kama?, wa zai zama gatanta?, shikenan sai ta dawo ainihin maraniya ta gaske.
Hannu tasa ta goge hawayen daya sakko mata, ta kama hannun Kaka ta riƙe gam.
Kusan minti goma Kaka ta farka daga baccin daya fara ɗaukanta, ta kalli Fillo da ta rafka uban tagumi alamu na nuna hankalinta ma gaba ɗaya baya jikinta.
Sau uku ta kira sunanta ba taji ba, sai da ta bubbugi kafaɗarta.
"tunanin ne kike?".
"kin farka?".
Tamyaryoyin suka fito daga baku nan su a tare, Kaka ce ta fara amsa mata da cewar,"ehh na tashi amma yanzu zan koma". Ita kuma tace,"to ki koma dan Allah, ƙila isassan baccin da ba kya samu ne kwana biyu".
Kaka dai kallonta ta ke yi, tunanin da inda zata fara yi mata bayani take, kamar da wuya ta yarda taje tayi aikin nan, ba don komai ba ganin a halin da take ciki, sannan babbar damuwarta ma taya za'a sami jituwa tsakanin Fillo da su Nihal?.
Da ace Zaytuna ce kaɗai to ba zata ji wani fargaban aikata ba.
"yau ba'a gama abinci da wuri ba, ko na tambayo miki Yami?".
Kaka tace,"a'a naci zuwa anjima...yanzu tashi za kiyi kije kici gaba da aikin dana baro".
Fillo ta buɗe baki tana duban Kaka da irin kallon mamaki. murya a kumbure tace,"ba ki da lafiyar ma ba za su yi miki uzuri ba Kaka, ni babu inda zanje na barki ke ɗay